Wata kyakkyawar budurwa ce mai kama da Khaleed ta doso wurinmu da gudunta. Tana zuwa tayi hugging d'ina tace, "welcome our pretty sister inlaw."
murmushi na sakarmata, ta ja hannuna sai wani katafaren parlour. Yawu na had'iye nace a raina, 'wannan gida shi ake cewa aljannar duniya, no wonder Khaleed yake jijji da kanshi haka, amma dai yau ya taimaka min, dan da na zo da jallabiyata ko y'ar aikin gidan sai ta fini kalluwa.'
Wata mata ce ta fito daga sama ta zo wurinmu, tana zuwa tayi hugging d'ina tace, "welcome my daughter."
Mamaki nayi, dan kwatata ba zaka ce itace ta haifi su Khaleed ba, saboda jin dad'i ya b'oye tsufanta, sai dai ka d'auka ko yayar su ce.
Duk'awa naje nayi na gaida ita, ta d'agoni tace,"no my daughter, ki d'aukeni tamkar mahaifiyarki, kuma k'awarki." ta ja hannuna muka je kan kujera muka zauna.
Muna zama tace, "Gayamin wani abu a game da ke, kuma ki saki jikinki kar ki b'oyewa mummynki komai."
Khaleed ne yace, "mummy sauri muke, dama daga skul muka fito zamu mayar da ita gida kar a fara nemanta."
Mom tace," no way son, yanzu da zuwanta ko hutawa bata yi ba zaka wani ce zaku tafi? Yau ina tare da y'ata har dare, ko har ka fara kishi ne son?"
Khaleed yayi dariya yace, "kishi kuma Mom? no way."
A raina nace 'wannan ashe yana dariya he' s looking so cute.' A fili kuwa nace, "don't worry Khaleed, nasan Mama zata fahimta idan nayi mata bayani."
Khaleed yace, "well if you say so."
Mom cikin jin dad'i tace, "that's my girl, son yau na kasaka fa, ta zab'eni ta barka." muka sa dariya mu duka.
Khaleed ne ya ja Sa'id yace masa, "mu tafi please, bana son kallon wannan Dramar."
Dariya Sa'id yayi yace, "are you jealous man?"
Khaleed yace, "no way man, amma ba zan yi maka k'arya ba, naso ace Salmah ce anan tare da Mom suka fara sabawa da juna ba Ameerah ba. Saboda na san halin mum, ranar da duk game d'inmu tayi over, zan sha wahalar kafin na fahimtar da ita. Shiyasa banaso ta shak'u da Ameerah sosai."
Sa'id yace, "kanada gaskiya, sai dai ya zakayi tinda baka isa ka hana Mom ta so wanda take so ba, baka isa ka hanata son Ameerah ba, kuma ga dukkan Alamu ma ka makara, dan na lura Mom da Kausar kamar su goyata suke ji." da haka suka fice.
GEFEN SU AMEERAH
Momce tace, "my dear ki kira Mamanki ki gayamata kina wurin Mom inlawnki kar ta shiga damuwa."Nace "Mom ai ni banida waya, haka ma Mama ma batada, ba ma wanda yake da waya a gida."
Momt ace, "oh ya akayi haka? Ya akayi son bai siya miki waya ba?"
Nayi sauri nace, "A'ah Mom, ya kawo min nice dai nak'i karb'a."
Mom tace," ok kar ki damu, yanzu dai gayamin wani abu a game da ke, da famlynki."
Na fara bata labara kamar haka, "Mu biyar ne a wurin Mama, nice babba, sai Aliyu, Suhailah, Fatima da kuma autanmu Umar, amma muna kiransa Abul-Khairi, ko kuma Khairi kawai."
Mom tace," mahaifinku fa?"
Nace, "mahaifina is late, ya rasu."
Mom tace,"sorry dear," tayi hugging d'ina.
Sannan tace "how about school Ameerah?"Nace "ina Udus ne, yanzu zan je 200 level, and i'm studying biology."
Mom tace, "very good swearie, ke da Kausar abu d'aya kuke karatu, amma ita 300lvl zata je yanzu, may be shi yasa baku san juna ba."
YOU ARE READING
KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com
RomanceComplete novel is on okadabooks.com Highest ranking #1st in romance lots of times. This is a journey of a Hausa Girl Love Story. A girl fall in love with a man Who never notice her, who she doesn't even know his name, talkless of anything about him...