Washe gari ta kama ranar d’aurin auren Khaleed da Salmah. K’arfe goma na safe za'a d’aura auren, amma ango na kan sallaya yana kwasar bacci, dak’yar ma ya iya tashi yayi sallar asubah.
Ameerah kuwa da ta tashi tayi wankanta ta koma ta kwanta, sai k’arfe goma ta farka, ta tashi ta je kitchen dan ta had’a breakfast, sai sallamar Aunty Fareedah ta ji. Ta je da gudunta ta rungomota kuwa.
Aunty Fareedah tace, “yau dai mun zo tausar k’irji ne, dan haka ina nan har dare, dan kar y’an kawo amarya su zo su miki rashin mutunci, gwanda mu kasa mu tsare kayanmu."
Ameerah ta yi dariya, cikin murnarta tace “nagode auntyna.” D’an basket Fareedah ta mik’a mata tace, “ga kayan breakfast na zo miki da shi.”
Ameerah tace, “ohh my aunty, you are the best, kaman kin san yunwa nake ji, yanzu ma haka da kitchen zan je.” Ta ja ta suka wuce d’akinta.
Suna shiga d’aki Ameerah ta zuba breakfast d’in ta fara ci, suna d’an tab’a fira da Aunty Fareedah. Suna haka sai ga Kausar ta shigo a d’an hargitse.
Ameerah tace “ya aka yi kika fad’o haka kamar wacce aka koro?”
Kausar ta zo ta wani turb’une fuska tace, “ina yaya Khaleed?”
Da Mamaki Ameerah ta kalleta, sannan tace, “ kamar ya? ba yau ake d’aurin aurensa ba? May be yana can mana.”
Kausar tace “kinga, ina baccina mai dad’i fa Dad ya tasoni, wai antaru wurin d’aura aure amma ba ango ba alamarsa, Dad da friends d’insa sai kiran wayarshi suke yak’i ya d’auka, shine aka ce na zo na duba ko lafiya.”
a razane Ameerah ta mik’e tace, “bari na je na duba d’akinsa ko k’alau yake.”
Aunty Fareedah ta janyota tace, “ki k’yaleshi kawai, kar a d’aura auren ma, ke miye naki a ciki?”
murmushi Ameerah tayi tace, “anti Fareedah kishi ba hauka ba ne fa, ba zan iya yi mishi haka ba, bayan kuma ya tara jama'a, after all ban ma sani ba ko ba ya da lafiya ne.”
Kausar ta tab’e baki tace, “ai sai ki je ki taimaka mishi ya auro miki kishiya.”
Ameerah dai ta fita barsu tana d’an murmushi.
D’akin Khaleed ta tura ta yi sa'a k’ofar a bud’e. Can ta hango shi akan sallaya kwance. Da sauri ta je wurinshi ta fara tab’a jikinsa, ta ji ba zafi, amma sai baccinsa yake kwasa.
Ameerah ta rasa ya zatayi ta tada shi. Ta je tana bubbugashi kad’an kad’an. Janyota yayi ya rungume, ya cigaba da baccinsa hankali kwance. wayarsa ce ta dinga ruri, dak’yar Ameerah ta janye hannunshi daga jikinta ta je ta janyo wayar. sunan Dad ta gani kan screen ta d’aga wayar.
Tana d’agawa Dad ya fara zabga masifa, “idan kasan da can baka son auren ubanwa yasa ka fara tara jama'a? Wannan ai wulak’anci ne, toh bari ka ji, minti goma na baka ka iso wurin d’aurin aurenan, idan ba haka ba zanyi mummunan sab’a maka, dan ba zaka mayar da ni mutumen banza ba, bayan ma kasan yanda aurennan yake, nikad’ai ne ma har na tsaya maka.” ya kashe wayarsa, ba tare da ma yasan wa ya d’auki wayar ba.
Ameerah na sauke wayar ta rasa yanda zata yi. Ta koma gun Khaleed ta shiga bubbuga shi. Khaleed sai ya bud’e ido ya rufe kamar d’an maye, sai janyota da ya k’arayi a jikinshi ya rungume.
Ameerah ta tak’ark’are ta gantsara masa cizo a hannu. A razane Khaleed ya mik’e zaune yana fad’in, “ke mahaukaciyar ina ce ne wai? Are you a vampire? Are you thirsty for my blood?” Ya ma k’i bari tayi magana, ya koma cewa, “meh ya kawoki d’akina yanzu?”
YOU ARE READING
KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com
RomanceComplete novel is on okadabooks.com Highest ranking #1st in romance lots of times. This is a journey of a Hausa Girl Love Story. A girl fall in love with a man Who never notice her, who she doesn't even know his name, talkless of anything about him...