.*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
™/8/ 2018🔞
*🌺SAKAMAKO🌺*
_The pitch blunder__Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_
@ _IG:Surriem-sule_*#Lovestory2018*
*#romance#fiction..*
*any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.**Page▶43-44*
Washe gari da safe suhan ta tashi Da shike jikin ta ya dan bata captain ba adai dai yake ba kamar yana fushi. cos daga yanayin yadda ya mata magana tun jiya sai ta sha jinin jikin ta gashi dama tasan bata da gaskiya.
So da safiyar Allah ta tashi tayi normal duties dinta a tsanake ..duk ma bai tashi ba amma sai ta dan kimtsa masa dakin sa lokacin yana kwance ne kamar yana bacci
Har ta gama ta fita Bai motsa ba kuma bai fita ba tana ta na kan jira ga lokaci ya tafi ta kira su anty jamila kuma shiru baya tafiya bare tasan ya ake ciki da jikin ummahn ta.
Wajen 10 dai dai taga bazata iya hakura ya tashi ba kawai tayi serving dinsa abincin sa takai masa...
Alokacin kam bacci ne na gaskiya ta dan dauke sa don bai ma san da shigowar tan ba ta ajiye a kan table
.tana fita ta sabi hijabin ta ta kama hanya...Asibiti ta soma shiga cikin sauri amma dai dai bakin ward suka hadu da su ummah..
Tace anty ya dai..ya jikin ummah?ena zakuje kuma... ya naga kun fito? A sanyaye anty jamila tace da sauki suhan" ummah ta dan dago da kyar tace "gida zamuje kawai sunce kudin mu ya kare ga kuma magani nan da suka rubuta enaga kwara muje gida sai muyi na magananin if not da wanne zamu ji ?
Suhan tayi ajiyan zuciya in dismay" tace to bakomai ummah..amma dai da dan sauki ko? Ummah tace eh ba laifi muje jamila ke kuma sai kije aiki tace toh umnah sai nazo....
tare da antyn suka dan taya ummah takawa har suka tafi bakin hanya ita kuma ta kama hanyar wajen aikiKwata kwata hankalin ta baya jikin ta" amma sai ta yi kokarin kwantar ma kanta hankali cewa ummah zata samu sauki...
Da safiyar Allah zarah ta tafi singapore basu ko hadu da captain ba..shikam yana kan bacci tafiyar suhan da kusan minti 15 ya tashi .
A gurguje ya kimtsa ya fito... dakin ta ya fara dubawa bai ganta ba ko tsaya tambaya bai yi ba ya fito ya dauko mota ya fice daga haraban gidan ..
Yana tuki yana dube dube har Sai da ya dan samu nitsuwa aransa sannnan ya kunna tracker daga wayar sa nan ya soma tracing location dinta..
Anguwar da ya nuna masa yakama hanyar zuwa..Lokacin suhan isowar ta kenan itama keke napep ya ajiye ta suna kan neman canji a bakin titi
Suna Cikin haka wata shaqiqiyar prado baka kirin wanda taji tintect ta dan dosu su ..gashi ba aganin kowa aciki so bata ma kula ba
mutumin da ke aciki da boys dinsa guda biyu" yayi mugayen dariya tare da cewa ince dai kun kalle wannan yarinyar da kyau?..duka suka maida hankali kan suhan as there were coming closer. Nan suka kare mata kallo da kyau sannan suka ce mun gane ta ogah..yace good to muje gaba chan ku ajiye ni sai na shirya muku yadda zaku min da ita..
Ba musu suka isa gaba ..sauka mutumin yayi bayan sun gama zancen su wani mota na daban ne ya zo ya dauke sa ya bar wajen
Wannan pradon ne ta dawo kofar restaurant
Daya daga cikin boys din ne ya shiga ya ce ena mai wannan shago .
YOU ARE READING
SAKAMAKO
RomanceYa zatayi da Yarinyar da bata kai ta goge mata takalmi ba amma ta kwace mata miji?...... #Suhan #captain majeed # Zarah