RUWAN DAFA KAI 2

44 0 0
                                        

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA
2

"Wallahi kaci amanata daka yaudareni ka munafurceni,baabinda zance saidai Allah ya isa tsakanina dakai,h...."zaa ga wanda yaci amanar wani tsakanina dake munafuka algunguma ke har kyayi zancen munafurci,idan akwai wanda yakamata yayi magana ma nine,tunda ai ni kika so ki zalumta,"ya hayayyako mata kuka take babu ko hawaye,tama rasa mezatace mishi taji dadi wato dan Adam dai babu na yarda kenan?ita datake tunanin tasami lusari hotihon dazata dinga juyawa son ranta ashe ta tapka babban kuskure,kodayake dai tukunna ai itace farida wannan dinnan mai samun duk abinda takeso a duniya a sanda take so kuma,karyarshi yace zai kuntata mata ya wulakantata yaci bulus,yayi karya wane shi?.

"Ka budemin kofar nan in tafi,don idan ma baka sakeni anan ba ta ruwan sanyi,dole zaka sakeni ta karfin tsiya"tafara maganar bayan ta share hawayen dake zubo mata,banza yayi da ita kamar ma baiji ba,"nace kazo ka budemin kofa na fita"ta daka mishi tsawa,"inji ajikina tukun,eh nace inji na jaki sai in nutsu uwata mtsw shashasha"maganganunshi ne kawai suke bata mamaki tabbas wannan abu ko a mafarkinta bata taba zata ba,"wallahi wannan ne karo na karshe dazan sake maka magana kazo ka budemin kofar nan in fita,"tace a fusace don tasha alwashin idan yadage bazai bude ba to kuwa zata iyayin komai don ganin ta kubutar dakanta,wani irin kallo yabita dashi cikeda raini,na irin me kika isa kiyi dinnan,sannan yaja tsaki yaki bata ansa,hakanne yasata kara fusata,tareda nufar kitchen a sukwane don dauko wata zabgegiyar wuka,irin babbar nan ta yanka nama tacikin set,saidai kuma me,dubawar duniyar nan duka wukaken kitchen babu su, don ya kwashesu,harda kananan,har irin table knives dinnan,dasu fork da duk wani abu dazai iya zama makami,tabbas kuma tafara gasgata zancenshi dayace batasanshi ba yafita tantiranci tunda ga alamu nata bayayyana.

Shikuwa yariga yasan dama haka zata iya kasancewa,tace zata dauko wuka ta mishi barazana ko ta kasheshi shiyasa data kwanta bacci dazu ya kwashe komai da komai ya zauna cikin shiri.

"Ina nan fa ina jiran fitowarki malama,yadai nace ko kin chanja shawara ne?"ya ce da karfi ganin ta dade bata fito ba daga kitchen din don yasan tabbas sanyin jiki tasamu saboda batasamu abinda take nema ba.
Kwanciya kawai tayi akasan kitchen din tadinga rusa kuka,kamar wata yar jaririya,dalilan kukan dayawa bazasu lissafubba tukun,"ki sauke wannan girman kan da taurin kan naki watalika idan kika lallabashi kika bishi ahankali ku rabu lafiya,irin wayannan basason taurin kai karki biye mishi"wata zuciyar tace da ita,hakan ne yasata ajiye duk wata isa tata,da wani cin buri ta fito ta nufo inda yake,yana ganinta yafara wannan murmushin,durkusawa tayi akan gwiwowinta,don tariga tagama karaya,ta ajiye makaman yakin nata tunda yanuna mata yafi karfinta dagaske gwara ta lallabashi, don a yadda abubuwa suke gudana tsab zai iya kashetan dagaske kamar yadda yake cewa, hawaye na zuba wani nabin wani tafara rokonshi"Don Allah don Allah don Girma da darajar iyayenka kabarni natafi gidanmu,na rokeka don Allah"ta hada hannaye tareda fashewa dawani matsanancin kuka,"Ayya,Allah sarki,"yace cikeda rainin wayo tareda girgiza kanshi wai yana tausaya mata,"ke dukfa wannan salon yaudarar ni bazaiyi tasiri akaina ba dakika ganninan,walahi banida mutumci mugun taurin kai ne dani,duk bama wannan ba matsalar itace idan naci alwashin yin abu tofa sainayi don haka dama kinyi shiru kin rungumi kaddararki don muna nan dake,zaki tashi daga wannan durkushen iskancin ko saina subirbideki?"Ya daka mata tsawa a take jikinta ya fara rawa,tafara karkarwa,don idan ya murtuke fuskar nan kamar bashi ba,abin tsoro yake zama ita kam yau ganinshi take tamkar wani dodo,"ai idan kikaga kin fita daga gidan nan to fa saidai idan gawarki ce aka fitar,amman kedai da ranki da lafiyarki ahaka babu inda zaki"yacigaba,gefe takoma ta rakube kamar wata yar bora tacigaba da sheshekar kuka,don batasan mezatayi ba kuma.

Gani tayi ya tashi yana hangame baki wai hamma"zan shiga ciki saura ki gwada yin wani shashanci,idan kina kaunar kanki dakuma lafiyar jikinki karki kuskura kiyi wata giggiwa nadai gaya miki"yace tareda sakar mata danniskan murmushin nan,shiru tamishi tacigaba da kukan zucidon kukan filin ma tagaji dayi sai dai ajiyar zuciya kawai.

Ganin ya shafe kusan mintina talatin bai fito bane yasata fara dube dube a palon ko Allah zaisa taga mukullin kofar amma inaa duban duniyar nan babu alamu,hakan ne yasata komawa kitchen tafara kokarin bude window abin mamaki shima gam,babu lamun buduwa baya ko motsi,bayan ko jiya ta budeshi,dube duben abinda zata fasa glass din tadingayi amma babu ya kwashe komai,dakyar tagano wata muciya a wani dan lungu,batareda wani bata lokaci ba kuwa tashiga bugun glass din take kuwa ya tawarwatse,karar fashewar abuce tasashi fitowa aguje don ganin metake shirin yi,"ke!""ya daka mata tsawa  tareda karasowa,yafara janyo kafar data zura zata fitan kota halin kaka don ta riga tagama tsorata dashi,kankame karfen windown tayi tana kuka tana cewa ya kyaleta amma ina kara jawota yake tana cijewa,hakan ne yasata tura bakinta waje tafara ihu iya karfinta wai ko makota ko maigadi Allah zaisa wani cikinsu yaji yazo ya ceceta amma shiru,dukan hannun nata yake amma taki sakin windown hakan ne yasashi dauko muciyar data ajiye yafara kwala mata iyakar karfinshi tun tana iya jurewa harta hakura tasaki take hannu ya kumbura yayi ja ga mugun zafi Allah yasa ma dai babu karaya ko gocewar kashi.

"Wa kika fi basira wai?ko angayamiki ni shashasha ne saida namiki kashedi fa amma bakiji ba atoh gwara ma kidaina wahalar dakanki idan kinaso ki rayu don muddin kikace zaki cigaba da taurin kai kina yunkurin barin gidan nan to kuwa jikinki ne zaiyi ta gaya miki baji ba gani zata yi magana ya buge bakin,ya fama ciwon dazu ai kuwa sai jini kamar jira yake yafara kwaranya har ta hanci,amma ko ajikinshi saima sungumarta dayayi kamar wata gawa don ko kwakwaran motsi yanzu bazata iya ba,sai hawaye kawai,bai zame ko ina ba da ita ba sai daki,inda ya jefata kan gado,yashiga biyawa kanshi bukata batareda wai halinda take ciki ya dameshi ba,saida ya kammala sannan ya sake dauketa yakaita wani daki mai mugun duhu da babu komai aciki,don ko window babu bare ma har tayi tunanin fita ko taga haske,wurgar da ita yayi akasa sannan yajawo kofar ya garkameta da key yayi wanka ya fita abinshi yana fito.

RUWAN DAFA KAI 2Where stories live. Discover now