001

4.5K 283 15
                                    


*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*

*ALHAMDULILLAH, INA MI'KA GODIYATA GA ALLAH DA YA BANI IKON FARA RUBUTA SABON LABARI, HASKEN RANA LITTAFI NE MAI CIKE DA ABIN AL'AJABI, ABIN TAUSAYI, ABIN MAMAKI, ITS NOT ABOUT ROMANCE ITS ABOUT REAL LIFE, TAIMAKO, JIN 'KAI, DAUKAR FANSA, SADAUKARWA..........*

*001*

Sanyi ke dukan jikinta yayin da abubuwa ke tsikarar jikinta,  'ko'karin motsawa takeyi saidai ta gaza aikata hakan, ko idanuwanta ta gaza bud'ewa balle ta motsa ga'bo'bin jikinta,  cikin 'kan'kanin lokaci taji duk jikinta ya d'auki ciwo, 'Kara struggling da takeyi yake sanya ciwon yana 'karuwa.

Nutsuwa ta fara sanyawa ranta tana jan numfashi tana saukewa a hankali ta samu ta  bud'e idanunta, 'kifta idanunta tayi na lokuta sannan ta bud'e ta fara kallon wurin da take.

Yanayi ne na asuba musamman da tayi duba da sanyin dake tsikarar jikinta, hannunta ta motsa a hankali wanda taji alamun ciyayi a 'kasan hannunta, a wane irin wuri take haka?

Ta jima tana sarrafa jikinta kafin ta samu ta zauna, jingina tayi a jikin dutsen da take kwance gabansa sannan ta fara bin wajen da kallo.

Waje ne tamkar jeji domin iya kallonta bata hango gida ba sai busassun ciyayi da bishiyu, dutsen da take jiki shi kad'ai ne dutse a wurin, d'aga idanunta tayi ta kalli dutsen yayin da ciwo ya tsarga mata cikin kanta.

Ri'ke kan nata tayi tana 'kara kad'an yayin da bayanta da cikinta suka fara mata ciwo, komawa tayi ta sake kwanciya cikon ciwo tana mur'kususu saidai ta lura cikinta ya tokare ta, duk yanda taso ta 'kudundune ta kasa.

Ciwon yana lafawa ta tashi ta zauna ta kalli cikinta tare da sanya hannu ta dafa cikin, tsorata tayi jin motsi ya bayyana daga cikin cikinta, me hakan yake nufi?

A firgice ta tashi tsaye ta fara juyi tuni ta manta da ciwukan da take ji, waiwaye take saidai iya waiwayenta ta kasa gane a ina take, me takeyi a wajennan? Me ya kawota wannan wajen?

Rigar jikinta ta kalla rigar atamfa ce taga ta yage tun daga 'kugunta har zuwa 'karshen rigar, wandon dake jikinta ne ya rufa mata asiri, kanta babu d'ankwali haka kuma babu mayafi.

Shin a haka take rayuwarta ko wani abun ne ya faru da ita? Wacece ita? Me takeyi anan? Ina ne gidansu? Su waye iyayenta? Wa ya kawota wajennan? Menene ya kawota?

Bata samu amsar ko da d'aya daga cikin tambayoyinta ba sai ma azabar ciwo da kanta ya fara, jikinta gaba d'aya ya mutu haka ta koma ta zauna.

Dukda sanyin dake wurin gumi ta fara had'awa numfashinta yana sar'kewa, wata azababbiyar 'kishirwa taji ta taso mata ga cikinta da ya takura mata da motsi haka ma bayanta ciwo yake.

Daurewa tayi ta sake tashi tsaye tana dafa jikin dutse tana tafiya, tangad'i takeyi haka idanunta baya gani sosai, hannunta d'aya na dafe da dutsen d'aya na ri'ke da cikinta.

Tafiyar da tayi bata wuce taku talatin ba taji gaba d'aya 'karfinta ya 'kare, yawun bakinta ya 'kafe haka idanunwata sun gaza bud'ewa, wani irin yanayi take ciki? Ko wannan ne yanayin da ake kira mutuwa? Tana bu'katar ruwa tana bu'katar abinci tana kuma bu'katar sanin wacece ita? Menene matsayinta a rayuwar duniya? Mutum ce ita ko aljana? Me ya kawota jeji?

Da wannan tunanin taga duhu ya fara d'aukarta, bata da 'karfin fighting ma kanta haka ta kwanta yayin da duk duniyarta ta zama duhu.

Bata san adadin da ta kai a hakan ba ta sake farkawa, fatan ta shine wannan karon ta farka da cikakken tunaninta, wacece ita?

HASKEN RANA✔️Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon