*RUWAN JIRA.....*
*Freedom writer's association📚🖊️*
*_Rubuta labari_*
*Fauzah* *(Ummuh Affan)*
*Dedicated to*
_Mijina Abdul Sidi Isah Haruna, son so fisabillillah_❤️
*1-2*
Kallonta yakeyi da shanyayyun idanunsa ya kalleta yace “Zuhura zaki dawo fah" murmushi tayi masa tace “Ya Nura baka rabo da abin dariya waye ya fada maka ni rayuwata da waiwaye a cikinta, bana waiwaye Yaya nura don Allah ka daina wannan mgnr sabo kakeyi" lumshe idonsa yayi yace “shikenan kije Allah ya bada saa amma nasani tabbas zaki dawo malamina ya fadamin hakan" bata bawa batunsa muhimmanci ba ta tsayar da dan sahu ta hau tayi masa bayanin inda zai kaita ya zaro kudin ya biya tayi masa godiya ta nufi gdanta.
A qofar gdan ya sauketa ta sanya mukulli ta bude ta shiga komai yananan inda ta tafi ta barshi ta sauke numfashi ta zauna tare da kunna TV domin hutawa idanunta nakan TV amma zuciyarta bata gurin tana gurin Yayanta Nuraddeen, jitayi an dafata ta dago da sauri tare da qaqalo fara'ar dole ta sauke masa tare da cewa “lahh hubby dama kana gida ai nayi tunanin baka dawo ba" zama yayi kusa da ita yace “ko yaushe idan kikaje gida kina dawowa da wani mood mara dadi Wanda nake kasa fahimtar inda ya dosa Zuhura meye yake sanyaki damuwa a yan watannin nan ne game da visiting din family house dinku da kikeyi?"Qoqarin saita nutsuwarta tayi ta hadiye wani yawu me daci tace “ba haka bane Ahmad kawai halin da baba yake ciki shine yake damuna sosai Amma nasan insha Allahu zai samu sauqi" janyota yayi jikinsa yace “kiyi masa addu'a yafi wannan damuwar da kikeyi Ina kika baromin yarinya ta?" Sake narkewa tayi a jikinsa tace “tana gurin ummah harma Shafeeq din shima wai ya girma yaqi biyoni"
Narkar da ita yayi yace “shikenan sai muji dadinmu mu biyu ko?" Lumshe idonta tayi ta zura hannunta cikin gajeran wandonsa tace “abarnan taka bata qara girma kullum haka take Ahmad ka rinqa neman magani" zuba Mata ido yayi yana nazarin kalamanta tayi saurin cewa “aa bafa wani Abu nake nufi ba Ina nufin maganin rage jaraba My Ahmad ka fara damuna kayita qwaqulata ko gajiya bakayi" ajiyar zuciya yayi yace “yau na zakiyi bayani ne"
Daga haka suka miqe tace kaje masallaci ka dawo bari nayi wanka nima nayi sallah" fita yayi itakuma ta nufi dakinta tayi wanka tayi sallar magrib ta zauna tana addu'o'inta zuwa wani dan lkc ta miqe tayi isha ta fara shirin kwanciya bacci, tana gamawa ta haye gado ta kwanta gabadaya zuciyarta tana gurin Nuraddeen kalamansa sunayi mata yawo “Zuhura da rana daya cikin shekarun da mukayi bamu tare bantabajin kinyi rawa a zuciyata ba, bantaba hada sonki da na wata mace ba a duniya, Zuhura bansan ke rayuwata bace saida na rasaki, na rasa kowanne farin ciki don Allah ki yarjemin zan rabaki da Ahmad cikin sauqi banso Kuma bana fatan rabon dake yawo a tsakaninmu yayi kisa"Gabanta ne yabada wani rass a bayyane tace “waye zai mutu kenan ni ko Abban Husnah?" Saurin girgiza kai tayi tare da kawar da tunanin a ranta daidai lkcn da Ahmad ya shigo ya kashe fitilar ya kwanta yana addu'a ya janyota jikinsa ya fara lalubarta tanason salon mijin nata amma yau ta kasa basa hadin kai data rintse idonta kalaman Nuraddeen ke dawo mata a haka suka raya daren bacci ya daukesu da mamakinta kamar yanda ta saba ko yaushe yau ma hakance tafaru mafarkinta sama da 10 years indai zatayi da namiji to Nura ne, ta miqe tayi alwala tayi nafila tare da roqon Allah ya yaye Mata abinda yake damunta,
Tanayin sallar asuba ta shiga kitchen kasancewar mijinta da wuri yake fita ta dora abin karyawa tana aikin wayarta tayi ring ta dauko ta duba taga baquwar number ta daga tare da sallama a daya bangaren aka amsa da cewa “qanwata kin tashi lfy?" Gabanta ne ya fadi ta dubi qofar da sauri tace “yaya Nura meye haka da safennan?" Ji tayi yaja numfashi yace “nakasa jurewa ne Zuhura inayin iyakar qoqarina amma abin yana neman fin qarfina zuciyata tana qoqarin rinjayata waini meye ma yasa nayi Miki saki uku ne har wani ya samu damar samunki...."Katse wayarta tayi tana share hawaye taci gaba da aikinta tace “nikam na shiga ukuna Yaya Nura neman sanyamin wasu wasi yake a aurena" da haka ta gama girkinta ta jera a parlour ta nufi dakin baccinsu yana tsaye yanasa kaya ta matsa ta rungumeshi tace “morning Sweet" murmushi yayi yace “morning darling" dariya sukayi tare tajasa suka fita ta rinqa basa abincin a baki yanaci suna yar Hira kadan kadan bayan ya gama suka fice tare ya sauketa gurin aikinta shima ya wucce nasa,
Tunani ya hanata aiwatar da komai a haka Suwaiba tazo ta sameta tace “Zuhura ana nemanki a waje" dagowa tayi tace “waye" sunkuyar dakai tayi tace “Yayanki da yake zuwa gurinki kwanaki" zaro ido tayi tace “ki rufamin asiri kice masa kinje kin tarar na fita ta qofar baya" kallonta Suwaiba tayi tace “why?" Daganta hannu tayi tace “kawai ki fada masa haka" juyawa tayi ta fita bata jimaba ta dawo ta zauna suna facing din juna idonta na zubar da hawaye Suwaiba tace “subhanallahi waini meye tsakaninki da mutumin nan ne duk sanda zaizo sai kinyi kuka shima sai naga yana sharar hawaye don Allah ki kwancemin wannan qullin Zuhura"Girgiza kai tayi tace “kada ki damu da abinda Bai shafeki ba Suwaiba komai da kikaga ya faru ya farune da amincewar Ubangiji Kuma yana cikin qaddarorin bawa Abu daya da zan iya fada miki shine Yaya Nuraddeen yayanane abokin wasana kuma tsohon mijina da mukayi auren saurayi da budurwa dashi yasoni ya nunamin qauna Kuma ya sadaukar da abubuwa da yawa domin ni a baya Amma ya kasa samun zuciyata qarshe a lkcn da na fara aminta dashi na farajin zanyi rayuwar dashi Kuma sai qaddara ta ratsa muka rabu rabuwar da cikinmu babu Wanda yasan dalilinta illah mun barwa Allah komai"
Jinjina Kai Suwaiba tayi tace “don Allah ki bani lbrn dalilin rabuwarku naji inason jin wannan labarin Zuhura inasonki da zuciya daya Kuma na fahimci kema kinason yayanki"~@Ummuh Affan~