*_RUWAN JIRA.... BOOK 2_*
*_Ummuh Hairan ce_*
_*Wattpad-realfauzahtasiu*_
🅿️5️⃣▶️6️⃣
_Part 2 na kudine 200 regular VIP 500 ki biya ta wannan account din 0255526235 GTB ko Kati MTN ta wannan number 09031307566_
Ban biye Mata ba na tashi daqyar marana na ciwo nayi wanka lkcn cikina nada wata bakwai da sati biyu muka zauna a parlour mukaci gaba da hirarmu lkc zuwa lkc Ina kora lemon Apple wayata tayi ring na dauka Ina me qarewa number kallo qirjina na bugawa da qarfi ganin inda na kafawa sensor din wayar ido yasa Sister leqowa ganin My Noor yasata warce wayar ta danna ta kara a kunnenta tare da sanya handfree yanajin an daga ya saki ajiyar zuciya yace.
“Qanwata ya gda?" Numfashi Mardiyyah ta sauke tace “ba ita bace yar'uwarta ce Mal don Allah idan zai yuwu to a shawarce Ina baka shawarar ka hqr ka daina Kiran matar wani hakan baso bane jefata kakeyi a tasku da fushin Ubangiji idan Kuma bazai yuwu ni da kaiba to zamu iya shiga kotu dakai akan kana Kiran matar mijina babu wani dalili na shari'a wannan shine warning na qarshe Kuma na farko da zamuyi maka idan wani abu bayan wannan ya bullo to muma zamu dauki matakin shari'a akanka, yes mijina adali ne bai hanaka gaisawar zumunci da ita ba a matsayin ta na jininka bayan haka Kuma to ka shiga gonarsa idan shi bazai dauki mataki ba ni zan dauka wai a hakama don Ina ganin mutuncinka ne"Tana gamawa ta kashe wayar tare da jan tsaki tace “bansan meye yake damunki da wannan mutumin ba da kike neman ki dorawa kanki wani ciwon akansa nidai nasan baifi mijinmu komai ba balle kice wani abu kike hange sister ki tsayar da hankalinki kiyi bautar Allah mu rungumi yayanmu muyi musu tarbiyya ta shari'a wlh ba komai ke tunzura zuciyarki wa wannan mutumin ba sai shedan Kuma Ina tabbatar Miki idan kikayi saken da kika rasa Lukman a matsayin miji shidin ma ba auranki zaiyi ba Kinga yayi miki biyu babu ba wan ba qanin karatun dan Kama to ki dawo cikin hankalinki"
Tana gama fadin haka ta miqe ta haye sama tana mita kamar itace Lukman din nidai binta kawai nayi da kallo tana qulewa hawaye ya zubomin na miqe nima na shige dakina daqyan nake hawa nawa bangaren saboda nauyin cikin jikina Ina shiga na lalubo number na kirashi bugu biyu ya daga ya cikin muryar kuka nace “Yaya" jin muryata yasashi miqewa yace “bakimin adalci ba Zuhurah baki riqemin alqawari ba kin barni sai lalube nakeyi na kasa samo madadinki nasan bazan samu ba Zuhurah don Allah ki hqr da daular nan ki dawo gareni kinsani duk wani Abu da yake baki zan iya baki shi saboda kece rayuwata Zuhurah ki ceceni wlh saura kadan na zama mazinaci duk matan duniya jinsu nakeyi lami basa gamsar dani....."Katse wayar nayi da sauri na turata qarqashin gado na kifa kaina a gadon na Kama kuka Ina riqe cikina Alh Lukman ya nufoni da sauri yana fadin “ya Salam Paradise meye yake damunki?" A zahiri qalau nake Amma saboda banaso ya gane inda kukana ya dosa sai na nuna masa cikina take cikin kidima ya fara Kiran likitansa babu bata lkc yazo ya dubani na shimfida masa qarya yabani magani ya tafi shikam wawan ya zauna sai sannu yakemin Mardiyyah tasan babu abinda yake damuna Amma dake macece me amana data fahimci baisan komai ba itama bata fada masa ba saima daukar wayata da tayi ta goge call long dina gabadaya yanda ko tsautsayi zaikaishi dubawa bazaiga komai ba, Saida nayi bacci sannan hankalinsa ya kwanta ya tashi shima yayi wanka yazo ya kwanta tare da janyoni jikinsa.
Tundaga wannan rana Yaya ya samu dama kullum zai kirani musha Hira yanata yimin pampo tare da fadamin irin halin da yake ciki nikam saidai nayi murmushi kawai saboda nasan banida wata matsala da zan fadi game da Alh Lukman saidai idam qarya zanyi masa, soyayya ta rinqa qaruwa tsakanina da Yaya Noor a boye batare da mijina ya sani ba na manta da cewa idan mijina Bai sani ba Allah ne wakilinsa yanaji yana gani,
A bangare dashi kuwa zamanmu ya fara samun tasgaro duk wani Abu da nakeyi da tausayinsa da nakeji ya goge a mind dina na koma kallonsa a matsayin barazana ga cikar burina saidai duk wannan abinda nakeyi ban yarda Koda wasa Mardiyyah ta fahimci halin da muke ciki ba saidai da dangantaka tayi tsami ne Alh Lukman yake fada Mata abinda ke faruwa ta sameni a hikimance tayimin nasiha nakuwa yi kamar naji yana dawowa na rufeshi da bala'i wai yana tonamin asiri a gurin kishiya kalmar ta bashi mamaki Amma baiyi mgn ba saboda neman sulhu yakeyi ranar ni kaina nasan nayi abinda Bai dace ba banduba girmansa ba na zageshi tas tare da fada masa qaddara takusa rabani da masifaffen aurensa badon ma jarababben cikin daya nanamin ba da a yau bazan kwana a gidansa ba.Suby Alh Lukman bai kulani ba bai tankani ba har na gama Ina gamawa ya dubeni da idanunsa da suka kada sukayi jawur yace “kiyi hqr My paradise banyi tunanin fada matan zai zama laifi gareki ba na dauka kamar yanda ta daukeki haka kika dauketa haba uwar yayana ai kinsan bazanyi don na bata Miki ba nayine saboda inason walwalarki ta dawo"
Rarrashin duniyar nan ya kasa samun kaina qarshe ma nabar masa dakin dole ya qyaleni da safe muna dinning munacin abinci ya dubemu yace mu fara shiri zamu tashi zuwa Dubai birth Moon nan da sati daya tabe baki nayi na miqe dukkansu suka cika da mamaki shikam jikinsa ne ya qara sanyi ya rasa gane inda na dosa ganin hakan yasa Mardiyyah dafa kafadarsa tace “Hero kayi hqr don Allah ni kaina na kasa gane kan sister Amma bari najena sameta...." Saurin riqeta yayi yace “Aa karkije qyaleni da ita" zama ta sakeyi tace “meye yasa?" Murmushi ya qaqalo yace “karki damu dan sabani muka samu jiya bari naje zata sauko" numfashi ta sauke tace “ok Allah yasa"Ji nayi ya bude qofar ya shigo ya tarar dani kwance a kan gado nayi rigingine kwanciyar da duk likitocina suka hanani a cewarsu tana takure babyna yana ganin haka ya nufoni da sauri ya sanya hannu zai dagani nayi saurin miqewa tare da cewa “meye haka malam?" Zubamin qananun idanunsa yayi da duk tsagerancin mace bazata iya barin nata a cikinsu na 1 minute ba yace.
“Wai meye yake damunki ne kin hana kanki nutsuwa kin hanamu dubi yanda kika tashi hankalin yar'uwarki kewai ko kallon yanda take tafiyar da rayuwar aurenta kiyi koyi bakyayi komai akayi Miki a yan kwanakin nan baa iyaba wai me kike nufine yaushe kikeso mu rayu cikin jin dadi Zuhurah da girmana da komai ki mayar dani sususu saboda kawai kinga inasonki, to gsky ki gyara banjin dadin wannan halin da kika dauko"
Juyawa yayi zai fice can ya tsinkayo muryata nace “ai biri dan agani a fada yake barna Alh Lukman wlh tunda nake dakai tsayin wata goma sha daya bantaba sanya kaya dan kaji dadi ba bantaba fesa turare don kaji dadi ba Kai hatta abinci bantabaci a gidanka don farin cikinka ba kamar yanda bantaba kwanan jin dadi a gdanka ba, bawai don ka gaza ba aa saidon zuciyata bata tare dakai bakai take buqata ba".......Please
Comments
Share
Vote~Ummuh Hairan~