*RUWAN JIRA.....*
*Freedom writer's association📚🖊️*
*_Rubuta labari_*
*Fauzah* *(Ummuh Hairan)*
*Dedicated to*
_Mijina Abdul Sidi Isah Haruna, son so fisabillillah_❤️
_Am sorry Fan's littafin *RUWAN JIRA....* na kudine 300 ta wannan account 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB_
_Ko Kati MTN ta WhatsApp akan wannan number 09013718241, ko VTU ta wannan number 09031307566__Ga masu buqatar karanta tsoffin littatafai na na kudi guda tara ga sauqi yazo da 1k dinki Zaki samesu documents gabadaya memakon a baya da sai kin biya 1800 kudai kada ku bari a barku a baya ta wannan account din na sama zaki biya kudinki idan kina buqata_
*5-6*
Janye jikinsa yayi daga nata yana furzar da iska me zafi ya nufi bathroom ya sakarwa kansa ruwa jikinsa duk yayi sanyi Nuraddeen... Sunan yana qara amsa amonsa a kwanyarsa, ya jima a bandakin kafin ya samu damar fitowa ga mamakinsa sai ya isketa zaune ta hade Kai da gwiwa tanata gursheqar kuka,
Zama yayi kusa da ita ya sanya hannunsa ya dago kanta ta fada jikinsa da sauri ta rungumeshi qirjinta naci gaba da luguden da takejin kamar zai iya bawa zuciyarta damar yin tsalle ta fito waje tace “My Ahmad!" Yanda tayi furucin numfashinta na sarqewa yasashi saurin dago kanta yace.“Wai meye matsalarki ne Zuhura kada ki jefamu cikin damuwa fah?" Bata iya furta masa kalma daya da zata bashi nutsuwa ba ta zame daga jikinsa ta dora kanta a saman cinyarsa tana shafa sumar dake kwance a sangalalinsa tana sauke numfashi, murmushi yayi na tausayin kansu yace “Zuhurah kina burgeni amma zurfin cikinki yayi yawa meye matsalarki?"
Shiru tayi kamar me bacci hakan ya sanyashi shima ya kwanta ya janyota jikinsa yana shafa bayanta da haka bacci ya daukesu, dasafe ya rigata tashi ya hada musu abin kari tana tashi yara angama shiryasu suka daukesu suka tafi Shafeeq gidan raino aka kaisa Husnah makaranta sukuma suka wucce gurin aiki dake juma'a ce ita yabarwa motar kasancewar tana rigasa tashi ma'anar hakan shine taje ta dauko yarsu.
Daya da rabi suka tashi ta shige ta dauki Husnah suka tafi gda suna shiga layin gabanta ya rinqa dukan uku uku ganin mota a qofar gdansu kallon motar takeyi sabuwa dal tayi horn megadi ya bude Mata ta shiga gdan tana daidaita parking dinta motar na shigowa ta fito riqe da hannun Husnah Shafeeq yana kafadarta ta zubawa motar ido, bayan shudewar wasu yan daqiqu ya zuro qafarsa ya fito ta sake bude idonta akansa dogon mutum kyakkyawa me cikakkiyar halittar mazantaka baqi irin baqinnan me kyau da qawata idanu wajen kallo.Batasan ya iso ba Saida taji iska a idanunta tayi saurin dawowa hayyacinta tare da juyawa da nufin shigewa ciki yayi saurin riqe hannun Husnah yace “kin gama qaremin kallo kina hango ramata kin juya Zaki tafi Little Yaya Noor dinki ne fah ko kin mantane?" Wannan kalma tayi tasirin narkar da zuciyarta hawayen da take hadiyewa ya zubo Mata ta kalleshi da idanunsa da suke saukar masa da kasala yace “tun shekarun baya nayi Miki alqawarin mota burina bai cikaba sai yanzu naso siya Miki wacce tafi wannan abubuwa sunsha kaina Tsoho ya matsa sai na qara aure sun kasa ganewa Zuhura bazan iya zama da kowacce mace ba wlh indai bake bace....."
Sakin yarinyar yayi yace “da quruciyata Little zan auri mace ta hudu bayan ke itanma Kuma bazata rayu dani ba mahadina yana jikinki don Allah rabonnan ya tsaya haka ki dawo gareni kada na haukace Zuhura...." Bazata iya jurewa ba shiyasa ta shige gda a guje yabita da sauri yana kiranta amma ta murda mukulli a qofar ya daki qofar tare da ficewa da sauri sai yanzu ya tuna cewa ashefa gidan mijinta ne nan din"Ta jima a zaune tana kuka a fili tace “aure! Yanzu aure Yaya Noor zai qarayi Innanillahi..." Da wadannan tunane²n ta shiga kitchen ta dafawa yaran indomie ta shige daki ta kwanta saboda har wani zazzabi takeji yana sauko mata, qarfe biyar Ahmad ya dawo tunda ya shigo idonsa akan motar yake yana shiga ya tarar da yaran sunata games a falo ya shige dakin ya tarar da ita rufe da bargo yace “Ina muka samu baquwar mota? Gabanta ne ya fadi ta dago tace “am... uhmmm... Dama Yaya Yunus ne ya siyamin..." Yanda tayi mgnr da in...Ina yasa masa kokwanto yace “tohhhh Kuma da izinin wa shi Yunus din ya siyanki mota?"
Shiru tayi batace qala ba ya miqe ya dauki wayarsa ya fita ya jima sosai sannan ya dawo ya dubeta ya kawar dakai ya dauki mukullin motar ya fice kamar tayi masa mgn Amma batason fitina shiyasa tayi shiru.
Tsayin lkc bai dawo ba har dare ya fara nisa ta miqe jikinta duk a mace ta nufi bathroom ta watsa ruwa ta fito daure da towel taja baya da sauri ganinsa tsaye yanata safa da marwa ta dafe qirji tace “Abban Husnah lfy" juyowa yayi ya dubeta ya girgiza kai kawai ya shige bathroom din ya jima sannan ya fito tana tsaye inda ya barta ya dauki rigar baccinsa yasa ya dauki pillow ya jefar a qasa,Nan fah ta qara shan jinin jikinta ta matsa ta tsugunna tace “tunda mukayi aure dakai tsayin shekara bakwai bamu taba raba gurin kwanciya ba sai yau why Abban Husnah?"
Gyara kwanciyarsa yayi yace “tunda mukayi aure dake tsayin shekara bakwai baki tabayimin qarya ba sai yau why Zuhura? Me kikeson boyemin Kuma kike tunanin zai boyu kin tsiro da sabbin dabi'u saboda wannan dan iskan dan'uwannaki me auri sakin bala'i kinaso kiyi wasa da damarki Fatima wai dama kinason Nuraddeen kika bari na aureki meyesa kika munafurceni kika barni na maye gurbin zuciyar wanina ashe ke munafukace bansani ba kuma maci amana Meye hadinki dashi da zaiyi Miki kyautar motar zunzurutun kudi har 25 millions Ina ya samesu aikin me kikayi masa?"
Kukanta ne yake neman cinye kalaminta tace “meye tunaninka akaina Abban Husnah ka tambayi megadinka yasan komai a gabansa akayi komai...." Dauketa yayi da mari yace “dallah malama rufemin baki kinje kin basa damarki ya biya buqatarsa dake shine zakizo kiyimin borin kunya wama yasan adadin lkcn da kika dauka kina munafurtata ashe ba aljanu bane kamar yanda nake tunani zumarsa ce tafi tawa gardi har takai kina mancewa da sunana lkcn jima'i kina makamin sunansa, to bari kiji daga yau ta qare bazan qara hada jikina da naki ba bare na zuba ruwana a inda wannan jahilin fasiqin ya zub...." Dagansa hannu tayi da sauri tace “aa Abban Husnah ina ganin mutuncinka kada cin mutuncinka ya wucce kaina ya qetara kan ahlina wlh bazan bari ba.........~@Ummuh Hairan~
