*_RUWAN JIRA.... BOOK 2_*
*_Ummuh Hairan ce_*
_*Wattpad-realfauzahtasiu*_
🅿️3️⃣▶️4️⃣
_Part 2 na kudine 200 regular VIP 500 ki biya ta wannan account din 0255526235 GTB ko Kati MTN ta wannan number 09031307566_
Fita Sister tayi ta kirashi ta sanar dashi halin da ake ciki babu bata lkc ya tsayar da duk wani abu da yakeyi ya nufo asibitin yana zuwa likitan ya fara da tambayarsa an taba yimin abortion ne?" Tambayar taso sanyashi faduwa saboda bashida amsarta, haksn yasashi yayi Jim na lkc kafin yace yana buqatar ganina, nan likitan yace masa ai Ina cikin halin da bazai samu jin komai daga gareni ba.
Dole tasa Alh Lukman Kiran wayar gidanmu cikin saa Ummah ta daga suka gaisa dags yanayin muryarsa tasan ba Lau ba ta tambayesa ko lfy nan yake fada Mata halin da ake ciki da abinda likitoci suke tambaya, abinka da iyayen da nan ta zayyane masa komai jikinsa ya qara sanyi maimakon yaji haushina kamar yanda kowa yakeji sai tausayina ya qara darsuwa a ransa.
Zuwa yayi yayiwa likitan bayani likitan yayi yan rubuce rubucensa ya dago yace masa “mahaifarta tayi raunin da bazata iya riqe ciki ya rayu a cikinta 9 months ba balle wannan daba daya ba yara biyu ne a cikinta dole idan anason su rayu sai an tallafawa mahaifarta ta hanyar daure bakinta da bata magungunan da zai qarfafata sannan dole ne abata bed rest duba da halin da take ciki baa buqatar namiji ya rinqa kusantarta hakan zai iya sanyata naquda babu shiri"Sosai Alh Lukman ya shiga dimuwa shida sister qarshe sister ta rinqa kwantar masa da hankali hardai yasa hanu a takardar da zaa dauremin mahaifata sukayi aikinsu cikin nasara doctor ya shimfida min dokoki dukkan dokokin inada yaqinin dagashi har sister zasu kiyaye Amma banda guda daya Lukman irin jarabbabun mazan nan ne baya iya gani ya kawar dakai musamman akaina hakan yasa nake tunanin yuwuwar wannan lukutar doka.
Gda muka koma na kwanta sunata riritani ya dubi Sister yace ”zanyi waya Niger a turo mana da wata ta rinqa taimaka Miki" nan tayi tsalle ta dire tace ita bata buqatar taimako indai akan sharafin yayanta ne daya matsa sai ta sanya kuka take cewa dashi ita yaushe zai bata dama ta nuna masa irin qaunar da takeyi masa da farin cikinsa indai ya hanata wannan damar to batada wata har abada,
Wannan ya sanyaya jikinsa ya hqr da mgnr yar aiki sukaci gaba da kula dani kulawar Sister Mardiyyah a gurina abar misali ce kasancewar tana da qualified a bangaren mertanity and health yasa takeyin komai da qwarewa,A Rana saita girkamin abinci yafi kala biyar tace na zabi wanda unborn kids dinta sukeso naci saidai nayi murmushi kawai duk lkcn da nace banso kuwa hmmm ranar yini zatayi tanamin mita wai zan azabtar Mata da yara da yunwa, wannan rayuwa kamar karta yanke watanmu biyu a Germany muka dawo Nigeria.
Ashe karamcin da mutuncin Mardiyyah asali ya samo mahaifanta da yan uwanta suka rinqa zuwa gdanmu suna Mata murna ita da Alh Lukman na samun qaruwar da zasuyi ta silar zuwana gidan nima suka rinqa sanyamin albarka tare da yimin addu'ar sauka lfy, satinmu biyu a Nigeria sannan yace mu shirya ya kaimu mugaida Ummah har tafini murna muka tafi munata Hira yana tsokanata yana cewa gani dai mace har mace Amma banida amfani saidai mutum ya kalleni ya hadiyi yawu.
Har lkcn da sauran kunyarsa a idona so tari idan ya tsokaneni ita ke ramamin to yanzun ma hakance ta faru tayi caraf tace "hakanma arziqi ne shekars nawa kana bugu kana qwaqula baka saka kwan ba sai yanzu to wlh kar naji karna gani idan mutum ya tabamin babyna qararsa zankai abimin haqqina nagaji dajin oyoyo Daddy a maqota nima so nake najishi a gidanmu ko Sister?" Ta kalleni tana murmushi nikuma sai naji tausayinta ya kamani hawaye ya cikomin idona nandanan ta kidime tace “Wayyoh! Hero tsaya Parker kaga kuka zatayi mgn ta ta bata Mata rai sister don Allah kiyi hqr ban fada da niyyar bata miki rai ba"Kwanciya nayi a jikinta na sake rushewa da kukan tausayinta baiwar Allah da watace da tuni yanzu ta hanani kwanciyar hankali saboda baqin kishi Amma ita tafi kowa son hankalina ya kwanta.
Sun dade suna rarrashina kafin nayi Shiru Saida na tabbatar Mata ba mgnrta ce tasani kukaba tausayinta ne sannan ta samu nutsuwa ta dauki tissue da ruwa ta gogemin fuskata ta dauko hoda ta shafamin tace “kada ki qara yimin kuka ji nakeyi kamar cikinnan a jikina yake ni wlh nafi kowa murna da samun qaruwar nan Zuhurah inason duk abinda mijina yakeso har ke da abinda ya shafeki"
Da wannan muka qarasa unguwarmu hmmm naji tsoron irin gyaran da akayiwa gdanmu sosai harda bene aka dora cikin wata takwas din da bananan tunanina ya tafi akan waye cikin yan uwana yayi kudi haka,
Shiga mukayi da sallama Hero sai riqeni yakeyi itama yar Taya bera barin tana tayashi Ummah tace “meye haka din Lukman?" Dagowa Mardiyyah tayi tace “wlh Ummah twince zata Haifa mana so Kuma batada lfy sosai shiyasa muke binta a hankali" murmushi tayi inda idanuna ya sauka akan Yaya Noor dake zaune saman kujera shima idonsa akaina yake yana cije lebensa na qasa gabana ya fara dukan uku² na samu guri na zauna Ina cije lips Ummah itama ta biye musu tanata zubamin sannu shikam Yaya Noor miqewa yayi ya dubi matarsa data zubamin ido ya daka Mata tsaya da cewa “tashi mu tafi kika wani kafeta da ido wata tsiyace banda Zuhurah"
