RUWAN JIRA.......

632 24 4
                                    

*RUWAN JIRA......*
_(A true life story)_

_*Rubuta labari*_
_*Fauziyya Tasi'u Umar*_
_*(Ummuh Hairan)*_

_*Wattpad-realfauzahtasiu*_

*P 49-50*

Shiru naji sunkumayi sai shassheqar kukan Yaya Noor lkc zuwa lkc daga baya naji baba yana cewa “bai mutu ba Nura akaishi asibiti su sashi a kwalba idan akayi saa zai rayu" daga haka naji gdan yayi tsit hakan yabani damar bude qofa na fito kamar dama Ummah jirana take ta cafkoni da qarfi ta hada kaina da bango jini ya balle hakan baisa ta qyaleni ba taci gaba da dukana kamar Allah ya aikota daqyar Baba Uwa da Yaya Yunus  suka qwaceni.
Ta dubeni tace “tur da baqar zuciya irin taki Zuhurah kekam kin shiga uku mugun halinki da aqidarki ta rashin yafiya ashe tananan baki barta ba yanzu me dan cikinki yayi miki da zaki dauki fushin ubansa ki sauke akansa kinje kinyi qoqarin kasheshi ta qarfi Allah baiga damar ya kasheshi ba shine kika sabi wata hanyar to wlh indai kinason mu shirya dake kibi Nuraddeen asibiti ki karbi danki ki raini abinki idan ba hakaba kuwa to kema ki sake uwa nikam na yafeki...."

Jikina yayi sanye amma zuciyata ta kasa rusuna Ina kuka Ina maqale jikin baba uwa nace “wlh Ummah banason Nuraddeen da duk abinda ya shafeshi bana fatan wani Abu nashi ya rabeni balle ya rinqa jin yanada wata alaqa dani dama dansa ne Kuma nabasa abinsa nikam na yafe masashi har abada bana buqat....
Mazga Ummah ta sake kawomin baba uwa ta riqe hannunta tace “ya Isa haka Sa'adatu ki daina dukan Zuhurah anyi Mata abinda ya kamata ta nuna fushinta Kuma ba itaba koni bazan riqe masa dansa ba ni da na haifeshi kenan yaje ya kaiwa wacce ya zabi rayuwa da ita ta riqe masa"  duk yanda Ummah taso fahimtar da baba Uwa abin ya faskara nan Ummah tayi rantsuwa akan bazan zaunanta a gda ba muddin ban karbi dana ba inda take Baba Uwa ta shiga daki ta dauko akwatuna tajani muka fita,
Baiwar Allah me son zumunci ashe tun ranar da Baba yaje ya fadawa Alh sadiqu abinda ya faru Baba Uwa ta biyo Baba ranar Alh Sadiqu ya saketa itama, wani qaramin gda muka nufa asalin gdan na Yaya Noor ne ya ginashi tun Ina shekara bakwai yake cemin gidanki ne anan zamu zauna kafin Allah ya bani ikon Gina Miki babba, ashe anan ta dawo da zama muna shiga ta budemin daki guda na shiga komai anzuba Mata harda A.C nasan duka aikin Yaya Noor ne nikam dakin data bani harda TV da katifa qatuwa ko ledarta baa cire ba.

Kallona tayi tace “kwanta bari na dafa ruwa na gasa Miki jikinki yo ni nataba ganin wannan zalumci a dakeka a hanaka kuka Allah dai ya saka Miki wlh iyayenki basuson gaskiya duk mutumin qwarai ai yasan an zalinceki yarinya qarama dake ya mayar dake bazawara" tana fada tana komai ta kunna gawayi ta dora qatuwar tukunyar Almunium ta cikata da ruwa.
Har bacci ya fara daukata ta shigo ta tasheni muka shiga bandaki tanamin wankan Ina kuka saima data zuba sabon ruwan zafi tasani na shiga ciki wayyohh nan ne na gane banida wayo ashe gurin tsami yayi naci kukana Baba Uwa na dannani tanamin sannu bayan ta gama gasani muka koma ciki ta yaga tsumma me kauri tabani nayi amfanj dashi ta hadamin shayi me kauri ta zauna ta rinqa bani inasha daqyar Ina gamasha kuwa na dawo dashi wai ashe yunwa ta shigeni ta gyarani na koma na kwanta da zazzabi me zafi a jikina.

Fita Baba Uwa tayi ta kulle gidan bata dade sosai ba ta dawo ta siyomin duk wani Abu da tasan me jego zata buqata, tanata yimin sannu Ina kadanta Kai da dare Ina kwance nade da bargo naji muryar Yaya Noor gabana ya fadi amma sai na dake ya shigo har parlourn yana Shirin shigowa dakin Baba Uwa ta fita tace.
“ya akayi? Zama yayi yace Mata “na ajiye aikina na Mali na zan tafi qaro karatu Misra Uwa don Allah ki shiga mgnr nan subani matata inafa da sauran dama akwai malaman da sukace saki uku cikin kalma daya zaa iya barinsa a guda daya" bata katseshi ba saida ya gama ta dubesa tace “dama taqamarka kenan shiyasa kayi saki uku? To bazaa barshi dayan ba" inajinsa yanata yimata magiya Amma tayi biris  dashi qarshe ma ta tashi ta shigo daki ta mayar da qofar ta rufe.

Dole haka Yaya Noor ya tafi jiki babu qwari tun daga wannan ranar banqarajin lbrn yaron ba bansan ya akayi dashi ba   haka na wanzu a gdan Baba Uwa batare da Yaya Noor yasan inda nake ba zaizo gidan naji yanata yimata magiya yana kuka da idanunsa duk wata kafa ta ganina an kulle masa yakance shi bashida wani maijin tausayinsa a rayuwarsa nan da yakesaran jin qai ankasa jin qansa can Kuma gdansu Alh Sadiqu ya matsa masa lamba cikin biyu sai ya zabi daya yayi aure kodai Uzaira yar Baba Rahamanu ko Kuma Zaliha yar abokin Alh Sadiqun.
Shikuma zuwa lkcn zuciyarsa ta fara rauni wajen boye abunda ke cinta Allah sarki Yaya Noor har susucewa yayi a wannan karon yana tafe yana sambatu idan mgn akayi masa da sunana zai amsa kowa sunansa Zuhurah a wannan karon, zuwa lkcn nima Kuma sai Allah ya jarabceni da tausayinsa lkcn da nayi arba'in na fara dawowa hayyacina kewar Yaya ya da nadamar abinda na aikata ta fara nuqurqusar zuciyata kullum cikin damuwa nake inajin yanzu da ace banyi sanadin salwantar rayuwar dana ba da ko arziqinsa zanci nake ganin Yaya sai hawaye ya zubomin nakan yini Ina kuka.
Ranar wata asabar tun safe baba Uwa tayi asubancin tafiya Rano saboda wata rasuwa da muka tashi da ita naso na bita tace nayi zamana bangama yin qwari ba sannan kowa fushi yakeyi dani saboda labarin abinda na aikata ya fantsama duniya bama iya bakin dangina ba hakan yasa tace na bari komai ya qara lafawa.

Ina kwance a daki Ina bacci ashe na manta ban kulle gdanba daidai lkcn Yaya yazo unguwar mamaki ya cikashi ganin gdan a bude ya shigo gdan yana dube dube ko Ina baiga kowa ba hakan yasashi shiga parlour ganin inda akayi break yasashi sanin lallai da mutum a gdan a hankali ya bude dakin ya leqa ya hangeni kwance qudundune da bargo mamaki ya cikashi a ransa yana tambayar kansa to waye a gdan dama Baba Uwa ba ita daya bace?
Matsawa yayi jikin gadon yana qaremin kallo kafin yasa hannunsa a hankali ya janye bargon sai ya zubamin ido cike da farin ciki ya zauna kusa dani Wanda qamshin turarensa ya sabbabamin tashi mukayi ido biyu na miqe zaune da sauri tare da ja baya na yayumo blanket na rufe jikina kasancewar rigar bacci ne kawai a jikina wata ajiyar zuciya ya sauke me qarfi ya matso jikina sosai ya kafeni da idanunsa da suke narkar dani yanata matsata Ina janyewa har mukaje qarshen bangon ya janye blanket din da qarfi nayi saurin dunqulewa waje daya jikina sai rawa yakeyi,


Nayi tunanin rufeni zaiyi da duka Amma sabanin haka sai naji saukar ruwan hawayensa a kafadata na dago da sauri nima hawayen ne da ban shirya fitarsu ba suka zubomin kawai banyi aune ba sai jina nayi a jikinsa ya sanya duka qarfinsa ya matseni yana sunsunar wuyana cikin rikitar yanayi yace “Ma...matata Ina....sonki don Allah kada ki yarda su rabamu dauriyata ta qare akanki zan iyayin komai nasan kinaso na kema........
Ashe duk zancen baka nakeyi qarya nakewa kaina da nake cewa banason Yaya Noor yanzu ne na fara sonsa, Suby sai na shige jikinsa na rushe da kuka me qarfi Ina lalubar kansa da hannuna na dora hannuna a tsakiyar kansa Ina shafa bayansa nace “Yaya  haka ka shekara sama da goma kanaji a kaina ashe haka so yake Yaya Noor me nayi maka ka yankemin wannan hukuncin meyesa ka zabi yankemin hanzari ta hanyar datse igiyoyin aurena dakai meyesa Yaya Noor meyesa ka zabi fifita bare ka sakeni sakin wulaqanci akanta ka cutar dani Yaya ka tursasa zuciyata ta koyi sonka da qaunarka sannan kayi watsi dani, yanzu ya kakeso nayi kenan Ina na Kama a rayuwata ta gaba Ina dana Yaya ka bani dana don Allah........

Please
Comments
Share
Vote

~Ummuh Hairan~

RUWAN JIRA......Where stories live. Discover now