*RUWAN JIRA......*
_(A true life story)__*Rubuta labari*_
_*Fauziyya Tasi'u Umar*_
_*(Ummuh Hairan)*__*Wattpad-realfauzahtasiu*_
*P 53-54*
Kallon juna mukayi ni da Yaya Noor gabanmu dukkanmu na faduwa idona ya ciko da qwallah daidai lkcn da aka qara dukan qofar Baba yace “wai Nura bazaka bude bane sai ranka ya baci..." Da sauri ya bude qofar kamar dama baba ya saita ya daukeshi da mari yace “ashe kaima haka ka zama Dan iska bansani ba ashe gaskene da ake cewa dani ana ganinku a wasu gurare nake musawa turr da wannan rayuwar da kuka zabawa kanku, waima kanku aka fara mutuwar aure ne?"
Cafka Baba yakaimin ya watsani waje yana me nuna Yaya Noor da hannunsa yace “tunda kazama dan iska kada na qara ganin qafarka a gdana daga yau na yanke duk wata alaqa dakai har sai Zuhurah tayi aure" yana gama kora masa ya fito shida Yaya Lawan Yaya ma ya biyosu baba ya dakamin tsawa na shiga adaidaita muka tafi gida.Muna zuwa gda sabbin dokoki suka hau kaina ciki harda ta tafiya ta karatu Niger American University a cewar baba wani ubangidansa ni yakeson aurena harma yace masa idan na amince a daura Amma ni a Niger zan zauna saboda harkokinsa sunfi acan.
To dake dama neman mafita muke Kuma faduwa tazo daidai da zama ban jaba na amince inda amincewar tawa tabawa kowa mamaki, da dare nake fadawa Yaya Noor a waye cikin qaraji naji yace “what?" Sai jikina yayi sanyi na Kama kuka shima hakan ya sanyata mass jiki yayi qasa da muryarsa yace “bazan iya jure ganinki da wani ba Zuhurah amma banida yanda zanyi na dawo dake gareni dole sai hakan ta faru karki damu dani kiyi aurenki Amma don Allah kiyimin alqawari daya tak"
Da sauri muryata na rawa nace “wannene Yaya?" Shiru yayi kafin ya busarda iska yace “kiyimin alqawarin sau daya tak zaki amince da mutumin nan sannan kiyimin alqawarin wata daya zakiyi a gidansa ki dawo kiyi idda mu mayar da aurenmu"Numfashi na sauke batare da tunanin komai ba nayi masa alqawari mukaci gaba da hirarmu Ina kwantar masa da hankali daqyar na samu ya saduda, abin mamaki wai kwanaki uku dayin wannan mgnr saiga su Yaya Shamsu da Yaya Lawan sun shigo gida wai daga Rano suke gurin daurin aurena,
Hakanan gabana tayi kwance² ta fadi cikin razani na shiga daki na Kira number Yaya Noor yana ganin kirana ya daga yace “Baby gabana yau sai faduwa yakeyi na rasa meye yasa" numfashi na sauke nace “Yaya an daura fah" da sauri yace “me...me aka daura?" A sanyaye nace “auren..." Wani salati da Yaya ya saki kawai saijin faduwarsa nayi can naji Baba Uwa tana Kiran “dannan Kai dannan meye haka..."
Daga haka ban sakejin komai ba wayar ta yanke na miqe Ina safa da marwa zuciyata na gurin Yaya Noor inason fita naje naga halin da yake ciki Amma Babu hali da canma an hanani fita balle yanzu Ina cikin wannan zulumin naji sallamar wasu manyan mutane uku su Yaya sunata masu sannu da zuwa aka shimfida musu darduma qatuwa suka zauna suka gaisa dasu Ummah da fara'a.Can naji wani cikinsu yace “Mama wannan shine Alh Lukman shine surukin naku" gabana ya fadi sosai Ina tsaye Amma Saida na zauna kafin daga bisani naji Ummah tace “Allah Sarki ya iyalin naka?" Amsawa naji yayi da cewa “lfy Lau suke" can Ummah tace “bari a kiranku ita tana ciki"
Miqewa Ummah tayi ta shigo dakin ta isheni na hade Kai da gwiwa sai kuka nakeyi ta gallamin harara tace “hqr shine ya kamaceki da istigfari na sabonki da kikayi ki tashi kije suna jiranki" Shiru nayi ban bata amsa ba ganin zanzo da tsalle yasata dakamin tsawa tace “banson iskancin ki Zuhurah ba qananun mutane ke jiranki ba" ganin ranta ya baci yasani miqewa na dauki hijjab dina na fito,
Daqyar na gaishesu suka amsamin da fara'asu ganin babu kowa yasa wannan sarkin azagwaigwai din fara yimin bayani a zahiri sauraronsu nake Amma a badini zuciyata tana gurin Yaya ganin basuda niyyar sallamata na miqe zan shiga daki sai lkcn Alh Lukman ya magantu da cewa “bakiji ba?" Tsayawa nayi ya miqe inda sukuma suka fice ya matso bayana dake dogone ya kereni sosai ya sunkuyo ya sanya hannunsa ya dago fuskata.Hawayen da naketa shanyewa suka zubo a kuncina sai ya sakeni da sauri yace “Sorry please bansan bakiso ba dama inason nace Miki ki shirya gobe zamu wucce wani Abu na gaggawa ya tasomin na fadawa Baba harma ya fadawa wadanda zamu tafi tare dasu saboda ganin guri.
Yana fadin haka ya zaro kudi masu kauri 10 back 1500k ba qaramin kudi bace ya bani yace nayi gyaran jiki ban karba ba saiya ajiye min nikuma na shige daki na fada gado na rushe da sabon kuka, Suby kinsan meye yake sani kuka? Kawai tunawa cewa yanzu fah shima Alh Lukman jin kansa yakeyi a matsayin mijina.
Idan na tuna haka sai na sake fashewa da kuka qaddara tayimin yankan qauna mutum daya nakeso a matsayin nan duk duniya gashi yayi wasa da damarsa, inanan kwance naji yara suna shigo da kaya shirgin kayan abinci da qwalam sai wani qaramin akwati yaron yace ance abani Wai abinda nake buqata baby na kirashi na fada masa.Please
Comments
Share
Vote~Ummuh Hairan~
