ruwan jira......

606 26 0
                                    

*RUWAN JIRA......*


*_Rubuta labari_*

*Fauzah* *(Ummuh Hairan)*

  _*LAST Free Page 19-20*_

_*This Book na Kudine regular 300  V-VIP 1k ta wannan account 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB*_
_*Ko Kati MTN ta WhatsApp akan wannan number 09013718241, ko VTU ta wannan number 09031307566*_

*P 21-22*

Da asuba na tashi Amma yaqi bani damar tashi daga jikinsa saima qara matseni da yakeyi bai sakeni ba Saida Yaya Shamsu ya buga masa qofa yace ya fito suje masallaci, ya kalleni a nazarce yace “kije ki dafamin ruwa zanyi wanka" zaro ido nayi Ina kada harshe sai abin ya bashi dariya ya matso da kansa ya dora a cinyata yace “me kike tunani?" Qasa nayi da kaina nace “nidai bazan iya ba" murmushi ya sakeyi yace “haka kuwa zakiyi kinsan dai bazai yuwu nayi sallah da janaba a jikina ba ko?"


Saina tsinci kaina da jin kunyarsa nasa hannu na na rufe fuskata ya miqe yabi hanun nawa yayi masa kiss tare da zamar dani ya kwanta a jikina yana cewa “tunda bazaki dafamin ruwa nayi wanka ni daya ba bari nasaki neman na gasa jikinki kinga sai Ummah ta dafa mana kawai ke kin huta" da sauri na tureshi ina haki nace “aa nidai bari na dafa maka" ban bashi damar yin wanu Abu ba nayi wuf na fice daga dakin na shiga kitchen na kunna gas na dora masa ruwan ashe Ummah tana kallo na da yayi zafi na juye na sirka masa daidai yanda nasan zau iya yi masa sannan na dauka nakai bandakin na dawo na hada masa wani na alwala a buta na shiga dakin nace masa “nakai maka ruwan" lumshe idonsa yayi tare da miqomin hannunsa yace “taimaka min na tashi jiri nakeji" banmasa gardama ba na taimaka masa ya miqe Ina riqe da hannunsa har bandakin muna zuwa bakin qofar na cake ya sunkuyo daidai kunne na yace “kizo ki qarasa ladanki kawai yiwa miji wanka yana cikin aikin mace ta gari...." Ai bai rufe bakinsa ba tuni nakai daki don na fahimci Yaya Noor irin mazan nan ne yan rayuwa sudai aji dadi kawai idan nayi wasa naci gaba da shige masa kafin mubar qasar nan gobe sai ya gogemin hadda wannan dalilin yasa na qudurce a raina yaudai bazai qara ganina ba iskancinsa ya fara isata kawai Ummah tasa yana neman canzamin lissafi Koda yake ba laifin Ummah bane tausayi yabani jiya yanda yaketa numfarfashi shiyasa banja masa turjiya ba.

Lkcn dana shiga dakin dake ba sallah zanyi ba kwanciya na sakeyi ban jima ba kuwa bacci wuya ya daukeni don na matsu sosai chest dina sai ciwo yakeyi musamman nipples dina da ya matsu daren jiya, bacci nayi bilhaqqi har wajen tara Ina bacci bansan sanda ya shigo ba saiji nayi numfashina yana sama sama na bude idona a hankali sai kawai naga ashe bakinsa ne saman lips dina baya ki tunanin wani ya shigo yaganmu a haka.
Tureshi nayi cikin jin haushi da muguwar tsanar da bansan yaushe ta dawo ba nace “meyw hakane kaine wai wanne irin mutum ne kai baka da aiki sai taba nan taba can kamar goyon kwarto ni banson wannan rayuwar fah" jikinsa ne yayi sanyi ya shafa kansa yace “zuwa nayi mu gaisa zanje Na'ibawa me zan taho Miki dashi?" Ga mamakinsa sai yaji nayi tsaki na miqe na diro daga gadon nayi waje Ina kada masa mazaune,
Girgiza kai yayi ya miqe ya fito ya tarar da Ummah a tsakar gda ni Kuma Ina kitchen Ina hada tea ya kalleni yace “baki fadamin me kikeso ba wifey" tabe baki nayi tare da juyansa baya don ma kada yasa a ransa zanyi masa mgn, bayason Ummah tayimin fada bayan fitarsa shine dalilin da yasa yace “oh sorry fushi fa akeyi dani ashe kiyi hqr zan taho Miki da Lollipop da cheese harma da sweet camfor" dariya sosai Ummah tayi abinda yasani dagowa nima na kalleshi ya taqarqare sai lissafi yake da alamun ya manta ma da Ummah tana gurin nima sai nayi murmushi na kawai dakai yace “yawwa ko ke fah ai da haka kimfi kyau bye bye"


Kallon Ummah nayi ta zabgamun harara data sanyani nima daga Masa hannu ya fice yana murmushi na koma naci gaba da hada tea na nasha na tashi na shiga wanka bayan na fito Ummah ta daukomin wani dafaffen nama ta sanyani a gaba tace nazo naci, da farko na dauka dadine saida na fara ci naji ashe babu wani dadi gashi ta tsareni da ido harda sandarta da alamun dakuwa zanyi idan nayi gardama, haka na rinqa turawa Ina matsar hawaye can na dago nace “Ummah shima wannan na basir dinne naga banma iya dinkin ba balle kice zanke zaman keke" harara ta watsamin tace “na uwar basir ne fitsararriya kici nace ko naci qafar ubanki" haka na rinqa tura naman Ina kuka dadai naga bazan iyaba saina fara kakarin amai dole aka gyaleni ta dauko wani tsumi ta bani shima jug guda tace saina shanye shikam wannan na saba tunda aka daura aurena da Yaya Noor kullum sai tayimin shi tumin ruwan rake da zuma da kanunfari da minannas da sassaqen baure sai kimba haka take dafesu sai sunyi kauri tayita bani inasha kullum sai nasha jug biyu safe da dare,
Wannan rana nasha magunguna babu qarya ga wani gyaran jiki da takira wata sudanis a unguwarmu tayimin na kwana biyu ne amma ke kyace an shekara anayimin dake fatar tawa me daukar gyarance tuni na fito a amarya ta zam, nikam idan na tuna duk wannan kwalliyar da aketa yimin sabida Yaya Noor ne sai naji kuka ya kwace min tsanarsa ta dawomin sabuwa a wannan rana Yaya Noor yasha mugun fata don har addu'a na rinqayi mota ta markadesa nayi takaba a wucce gurin,


Bai dawo ba sai dare sosai inaji ya shigo da kayansa niqi niqi nayi luf kamar me bacci ya gama haske haskensa yajamin bargo yayimin addu'a ya fice nabi bayansa da tsaki ya juyo da sauri amma sai yaga na gyara kwanciya ya Jinjina kai ya fita Aunty Naja'atu ta tashi ta bude ledar tarkacen kayan ciye² ne harda gasasshiyar hanta da taji kayan hadi sai lemuka da lollipop da Cheese, wani irin Cheese ne da yake siyomin lkcn Ina yarinya inasonsa har gobe na dauka da sauri na rungume Ina murmushi yana tunamin da abubuwa da yawa kawai sai na fashe da kuka kewar da bantaba yiba ta Yaya Noor yau itace ta tasomin Aunty Naja'atu ta dubeni tace “meye hakadin kin rungume cheese kin Kama kuka"
Cikin kuka nace “Inajin kewar Yaya Noor dina na asali nifa har yanzu zuciyata taqi yarda wannan Noor dinane idan shine meye yasa na kasa tunashi Kuma na kasa sonsa?"


~Ummuh Hairan~

RUWAN JIRA......Where stories live. Discover now