RUWAN JIRA......

1.1K 28 0
                                    

*RUWAN JIRA......*
_(A true life story)_

_*Rubuta labari*_
_*Fauziyya Tasi'u Umar*_
_*(Ummuh Hairan)*_

_*Wattpad-realfauzahtasiu*_

_Wani dalili yasa na mayar da wani bangare na labarin nan kyauta wani bangare Kuma paid part One free_
_Don Allah masu tambaya daga farko suje Wattpad dina zasu sameshi to beginning_

*27-28*

Maimakon nayi mgn saina Koma na kwanta naci gaba da rera kukana ne taba zuciyar Yaya Noor shima sai ya hade Kai da gwiwa kawai ya rafsa tagumi ni dashi babu me cewa wani qala tsayin lkc kafin daga bisani ya miqe ya fita, ya jima sannan ya dawo da tarkacen ciye²nsa ya zauna a gabana yace "tashi kici abinci sai ki kwanta"
A daqile cikin gadara nace masa "banaci" ya kalleni da sauri yace "aikuwa baki Isa ba Zuhr bazan dauki zama da yunwa ba ki tashi kici abinci kafin Raina ya baci idan wani ciwon ya kamaki kika galabaita waye zaa dorawa alhakin hakan" da wadannan kalaman ya dagoni ya rinqa turamin abincin inaci ina kukan da ni kaina bansan meye dalilinsa ba.

Saida naci da dama sannan yass tisue ya gogemin bakina na koma na kwanta inata jera ajiyar zuciya yanata kallona da haka bacci ya sake daukata shima daya gama tsara abubuwansa yazo ya kwanta ya hadeni da jikinsa, duk yanda nakai da iskanci na indai Yaya Noor ya hadani da jikinsa nutsuwa nake samu saboda wani dalili da bansansa ba.
Sai 3:30pm muka tashi ya hadamin ruwan wanka yaso yimin Amma naqi dole ya qyaleni na shiga nayi na dawo na dauki doguwar riga na saka na sake kwanciya saboda sosai jikina yake ciwo shikuma yanayin wanka ya kalleni yace "zanje training ko zaki rakani"
Banza nayi dashi abinda yafi komai dukan zuciyarsa shi ya qwammace ko zaginsa zanyi idan yayimin mgn nabashi amsa akan Shiru din da nakeyi masa tabbatar raini kenan a gurinsa, to Amma dake lallabani yakeyi sai ya juya ya fice nabisa da dogon tsaki daya sanyashi juyowa ya tsaya cik.

Yafi minti biyu kamar zai dawo sai Kuma ya fice zuciyarsa na suya shikam baitabajin lbrn yarinya me taurin zuciyata ba saikace shaidaniya saibina yake ina qara fandarewa banko tashi daga kwanciyar nan ba sai La'asar nayi sallah nayi wanka na sake kwanciya abubuwa da yawa suna dawomin na kasa manta wuyar da nasha a hanunsa waima nan karo na biyu ne to karon farko ya nayi kenan.
Da magrib ya shigo da ledojinsa a hannu ya ajiye ya matso gabana ya sunkuya tare da dago kaina yace "uwargida barka da hutawa" dan qaramin bakina kawai na motsa na kawar da kaina yaci gaba da kallona yana murmushi yace "halinki daban Zuhr bansan a Ina kika debo kafiyarnan taki ba"
Baiyi tunanin zanyi mgn ba sai yaji nace "aiba kowa nakeyi wa ba nafi yiwa mutane masu masifar naci da qulafucin masifa irinka" yanda yake kallona yaci na tsorata amma ko gezau saina cigaba da kallona da nayi, qwafa yayi ya miqe ya nufi dakin ya dade ya fito ya canza kayansa da alamun wanka yayi.

Zama yayi kusa dani yace "munyi waya da Ummah tana gaisheki" keda baki gurin idan kin tanka na tanka ya dubeni tare da girgiza Kai abun nawa ya fara qure nisan hqrnsa yace "idan kika bari muka fara wannan wasan dake zaki fini shan wahala Zuhurah saboda ke mace ce ni dama zuciyata anyita da fadin daukar abubuwa da yawa ke kuwa taki qarama ce tarwatsewa zatayi"
Ban kulashin badai ya miqe ya shige ciki nikuma na zame na kwanta a parlourn inajinsa ya dawo yayi yin duniya na tashi naqi nayi kamar bacci nakeyi dole ya hqr ya qyaleni shima ya kwanta a parlourn yanata kallona har bacci ya daukeshi, a haka cikin qasqanci da wulaqancina Saida mukayi kwanaki biyar a NIAFOUNKA sannan muka tafi Tombouctou a cikin kwanaki biyar dinnan fir naqi bari wani abu ya qara shiga tsakanina da Yaya rarrashin duniya magiyar duniya naqi ji saima kuka da nake sanya masa idan naga zai matsamin dole komai nisan buqatarsa haka zai kwanta yayita juyi har gari ya waye.

To Koda mukaje TOMBOUCTOU ma hakance taci gaba da faruwa gidan Yaya me kyau dan madaidaici a cikin Jami'ar daki biyune sai babban parlour da kitchen kowanne daki da toilet sai wani toilet din a parlour sai harabar tsakar gdan da ya cikasu da shuke shuke saboda shidin akwai tsafta da son qawa,
Ranar da muka sauka Tombouctou da yamma ya dubeni yana sauri zaije yakai wasu file cikin Jami'a yace "My Zuhr kidan ragewa gdannan qura kafin na dawo kinga an dade baa shigeshi ba" kamar abin arziki na dagansa kai ya lakace min hanci yace "yawwa yar matata Allah yayi miki albarka" ban amsa ba ya fice da sauri ya nufi cikin Jami'ar nikuwa yana fita na tashi na kama zagaye gidan Ina yaba kyawun gdan a fili nace "dama da wani zan rayu a cikin gidannan bakaiba shashasha dashi"


Komawa nayi nayi zamana har dare ban dauke ko allura ba a gdan inanan zaune wajen tara sai gashinan ya dawo ya debo gajiya kuwa da ledojinsa Yaya akwai cefane babu yanda zaayi ya fita ya dawo bai dawo min da wani abu ba, tundaga qofar parlourn alama ta fara nuna masa banyi abinda ya sani ba,
Shigowa yayi yana qaremin kallo ina kwance ina games da wayata banko dagoba ya ajiye ledar cikin sanyin jiki ya matso maimakon ya nunan bacin ransa sai kawai ya dagoni ya dafa saman kaina yace "baki samu damar yin aikin ba kenan?"
A gadarance nace masa "eh ga Kuma zahiri ka gani" yanda nayi mgnr yasashi yin shiru can yace "kin kyauta Allah yayi miki albarka Fatima inaso na cinye jarabawar Ubangiji akanki bazanyi fushi ba kuma kome zakiyi domin ki batamin rai kafin kiyi ma na yafe miki"


Yana fadin haka yaje ya nemo tsintsiya ya fara gyaran dakunan Ina zaune Ina yatsina har ya gama dasu ya dawo parlourn ban ankara ba saiji nayi ya dagani cak bai direni ko inaba sai cikin daya cikin dakunan kan wata qatuwar katifa yace "ki kwanta ki huta zan qarasa gyara parlourn sai nazo muci abinci"
Binsa nayi da kallon mamaki hakanan sai yanayinsa da hqrnsa ya burgeni naji tausayinsa yana neman kamani amma sai zuciyata take rayamin meye yasa zanji tausayinsa bashi yace yaji ya gani ba kince baki sonsa saboda naci ya kafe Saida ya aureki ai kiyita gallaza masa kawai har ya gane kurensa.
Hakanan shaidan yayita ayyanamin abubuwa da yawa a Raina na kuwa hau na zauna lkcn daya gama ya shigo yayi wanka ya dauko flat da cup ya hadamin naman daya siyo da fresh milk ya matso yace "bismillah" kawar dakai nayi nace masa "bana buqata" ya kuwa matso da sauri yace "aa wlh baki isaba yarinya" ya cafkeni Ina qoqarin tashi na kuwa fashe da kuka.


Baiko damu ba ya rinqa turamin naman me laushi inaci yana koramin da madarar har saida yaji a ransa na qoshi sannan ya tashi ya fita da kayan ya dawo ya sake wanka yayi Shirin kwanciya, mantawa yayi da wayarsa s parlour aikuwa yana fita na tashi na datse dakin da mukulli na dawo na kwanta.
Tabbas nasan bantaba yi masa abinda ya batansa rai ya tashi hankalinsa irin ranar ba saboda yagama sanya ran zai huta a matsayinsa na ango Amma na karya masa burget magiya da roqo babu Wanda baiyimin ba naqi jinsa naqi ganinsa, inajinsa har dare ya raba yanata kaiwa da komawa yana taba qofar amma fir naai budewa.
Koda safe yaso na bude saboda a matuqar buqace yake Amma naqi Allah yasa kayansa suna dayan dakin haka ya shirya badon rai naso ba ya tafi wajen aiki nikuma na fito nayi abubuwan da suka kamata kamar nemawa kaina abinda zanci.


Gyaran gda kuwa dama na qudurta a Raina ko gdan zai rube bazanyi ba Ina gamawa na koma na sake rufe qofata qarfe uku ya taso daga aiki dake ranar farko ce ya dawo a gajiye yanda ya tarar da gidan ya dagansa hankali ban gyara ba saima sake batawa da nayi, yaje ya taba qofata yajita a rufe ya sauke numfashi ya koma ya gyara gdan ya koma ya zauna.
Wannan rana ma bamu kwana daki daya ba abin ya fara damunsa cikin dare yazo ya rinqa dukan qofata inajinsa naqi na bude yayi magiyar duniya naqi bude masa kawai sai naji ya Kama dukan qofar da dukkan qarfinsa gabana ya fadi jin da gaske balle qofar yakeson yi na miqe da azama ai kafin nakai ga miqewa ma naji qofar ta fado cikin dakin na kuwa tashi da gudu na nufi bathroom yayi wani zafin naman cafkata ya hadeni da jikinsa gabadaya gabobinsa suna rawa ya wawuri bakina ya hade da nasa.

_Please_
_Comments_
_Share_
_Vote_

~Ummuh Hairan~

RUWAN JIRA......Where stories live. Discover now