*RUWAN JIRA....BOOK 2*
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
🅿️1️⃣1️⃣▶️1️⃣2️⃣
_Sorry My fans ku dakatar da turo kudinku haka don Allah, wadanda suka biya Kuma suyi hqr zamu hade a Littafina na gaba wato *_ZAMAN!_* nafi nishadin yin wannan free_
Kasa tashi nayi daga gurin sai kuka nakeyi na fargar jaji nadamar da bata da amfani ji nakeyi kamar na kashe kaina na huta a zahiri Suby bawai tunanin me zanje na tarar a gida ya dameni ba tunanin ta yanda zan tafi nabar yarana yaran dana qwallafa Raina akansu yaran da nakejin zan iya bada fansar ruhi akansu yarana biyu tal duniya wadanda bazan sake samun wasu bayan su ba.
Gefe Kuma ga tunanin babban rashin da nayi na adalin miji irin Alh lukman, tsikayo muryar Aadeel yanata kuka yasani miqewa jikina na rawa na fito na hangi Hero tsaye yanata jijjigashi na matsa a sanyaye gabansa na durqushe zanyi mgn yayi saurin dagoni ya miqamin Aadeel yace “yunwa yakeji Paradise" nayi mamaki daya miqomin yaron na karbeshi na zauna Ina bashi nono ya zubamin ido hawaye na bin kuncinsa yace “shikenan na rasaki Zuhurah haka kika zaba mana nida yayana Allah yasani inasonki Zuhurah nasan rabon wahala yssaki bijirewa aurena kika zabi rabuwa da yayanki domin wani daban bazan Miki mugun baki ba inayi Miki fatan alkhairi da fatan cikar burinki da addu'ar samun rayuwar da tafi wacce kikayi a hannuna, Amma kisani wlh bana kaffara kaf duniya bakida masoyin gsky sama dani Zuhurah....."Yana fadin haka muryarsa ta qara karyewa ya miqe da sauri ya haura sama daidai lkcn da Mardiyyah ta fito dauke da Aadeeha tanata yimata wasa ta nufo qasan sukayi kicibis ya rabata ya wucce tabisa da kallo ganin yanda jikinsa ke rawa tare da leqoni ta sama ta hangenj zaune kaina a qasa, zuciyarta ta rabu biyu kamar tabishi sai Kuma tadai sauko qasan ta iso da sauri ganin ashe kuka nakeyi na rungume Aadeel tace.
“Bakya rabo da matsala Sister yanzu Kuma meye ya hadoki da mijin naki naga kamar hankalinsa a tashe?" Kallonta na dago jajayen idona nayi tare da zamewa a kujerar na dora Mata Aadeel a cinyarta nace “nasan yayana bazasu taba maraici ba indai kina raye a duniya Mardiyyah duk da banida tabbacin samun wasu a gaba hakan bazai hanani cika alkhairi da alkhairi ba na baki yarannan biyu kyauta kiji aranki ke kika dauki cikinsu kika haifesu ni qaddarar dake bibiyata sake qaddaramin barin gidannan badon babansu yanaso ba saidon alqawarin fansar farin ciki da yayimin duk da zuciyata tana rayamin bazan samu farin cikin dana zabi datse igiyar aurena saboda shi ba"Ina fadin haka na juya na nufi dakina a guje hakan yayi sanadin dagulewar lissafin Mardiyyah ta miqe jikinta na rawa ta nufi dakinsa ta bude ta shiga ta isheshi a nade a gado sai tsumar jiki yakeyi ta kwantar da twins ta matsa jikinsa ta nade duvet din hankalinta ya qara tashi jin yanda yake shassheqar kuka tace “wai meye ke faruwa a gidannan ne Hero me yafaru don Allah ku fadamin"
Itama sai ta fashe da kuka jin kukan nata yasashi yunqurawa ya miqe zaune ya dafe kansa.
Cikin rawar murya yace “ta takura Saida na saketa saki uku Mardiyyah ya zanyi da qaunarta data cusamin ya zanyi da yarannan..." Zabura tayi ta miqe jikinta yana rawa tana furta “Innanillahi wa Inna ilaihirraji'un Allahummah ajirnih fih musibati wa'akalifni khairin minha! Garin ya Lukman meyesa ka aikata haka meyesa? Meyesa?? Meyesa?"Fita tayi da gudu ta nufi dakina ta banka da qarfi ta shiga lkcn Ina hada kayana a akwatu Ina kukan tunanin inda zan nufa na tarin damuwar barin yayana domin a yanzu shine abunda yafi komai damun rayuwata, ji nayi ta daukeni da mari tare da shaqata tana wani irin kuka da bantaba tunanin ko a hikaya kishiya zatayi don an saki kishiyarta ba tace “Kaiconki Zuhurah da wannan zuciyar taki da shaidan yayi gini me Fadi a cikinta ashe Ina kallonki me ilimi qungurmar jahila ce ke Zuhurah kika iya duban tsabar idon mijinki uban yayanki kikace ya sakeki saki har uku Zuhurah meye ribarki a kashe aurenki? Me Zaki fadawa iyayenki a yanzu?? Me zaki fadawa yayanki anan gaba idan sun girma sun tambayeki dalilin barinki gidan ubansu....."
Numfashi ta sauke me hade da shassheqar kuka tace “shikenan Zuhurah anyi kuskuren tun farko bansan meye yasani baccin asarar nan ba nasan duk da hakan bata faru ba Amma kisani kina cikin bata mabayyani Kuma zakiyi kuka zakiyi nadama a lkcn da nadamarki bazatayi Miki amfani ba Zuhurah kin zubar da qimarki a gurin kowa domin nasan ba qaramar asara da tabewa ce zatasa kibar Lukman ki komawa Nuraddeen ba domin nasan burinki kenan, kije gakinan ga duniyar ki damata yanda kikeso Amma kisani idan kin dama ke zata dama wataran" tana fadin haka tayi ficewarta tabarni da mutuwar gwiwowi na kasa hassala komai duk wannan abinda akeyi Baba Uwa bata sani ba sai yanzu da Mardiyyah taje ta zube Mata tana kuka sannan tasan wani abu ya faru.
