*RUWAN JIRA.....*
*Freedom writer's association📚🖊️*
*_Rubuta labari_*
*Fauzah* *(Ummuh Hairan)*
*Dedicated to*
_Mijina Abdul Sidi Isah Haruna, son so fisabillillah_❤️
_Am sorry Fan's littafin *RUWAN JIRA....* na kudine 300 ta wannan account 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB_
_Ko Kati MTN ta WhatsApp akan wannan number 09013718241, ko VTU ta wannan number 09031307566__Ga masu buqatar karanta tsoffin littatafai na na kudi guda tara ga sauqi yazo da 1k dinki Zaki samesu documents gabadaya memakon a baya da sai kin biya 1800 kudai kada ku bari a barku a baya ta wannan account din na sama zaki biya kudinki idan kina buqata_
*FREE 13-14*
Kallon kallo suka tsaya sunayi da Ummah da baba dashi kansa Yaya Noor din da jikinsa yake rawa qwanjinsa ya miqe, a Fam dinmu muna da wani sign na wata jijiya a tsakanin sumar kanmu da goshinmu da indai muka shiga tashin hankali itace alama ta farko, tabbatar tashin hankalinmu ya ta'allaqa ne da wannan jijiya to shima Yaya Noor yanada ita nan take ta fito sosai a goshinsa, ya bude baki kamar zaiyi mgn Kuma sai ya fasa ya miqe ya dauki jakarsa ya shiga dakinsu shida Yaya Shamsu,
Shiru tsayin lkc bai fito ba hakan yayi daidai da fitowar Yaya Shamsu daga wanka yace “Ina Nuran yake Wai meye yake faruwa naganku dako dako haka" Bai samu amsa daga gurinsu ba saini ce nace “yawwa Yaya Shamsu wai waye wannan da yazo yanzu nifa na kasa tunashi shikuma yana nuna yama dade da sanina"Ga mamakina shima sai naga yayi kasaqe yana kallo na dake shi irin mutanen nan ne masu tsarge gsky komai dacinta sai kuwa cewa yayi “Eh mana butulu ai kinkai moro dole kice kin manta da Nuraddeen ai dama na fadanku ni tun farko da kuketa murnar yarinyar nan bata damu da rashin Nuraddeen ba nace muku ku kuma zaku damu a gaba"
Shigewa daki yayi nabi bayansa da kallo tare da tabe baki ashe shikuwa Yaya Noor tunda ya shiga dakin babu abinda yakeyi sai kuka da safa da marwa kamar qaramin yaro, dafashi Yaya Shamsu yayi yace “kaifa kanada matsala kaima Noor bansan meye yasa ka cika zafafawa akan lamarin wannan banzar yarinyar mara tuna alkhairi ba kutmar ubancan waifa ta manta dakai tace! Kai wlh wannan qaryane ma bama zai taba yuwuwa bane Noor dama ace ni tace ta manta saina yarda amma kaidai tace ta manta ka, haba kowa yaji yasan qarya ne"Cije lebe Yaya Noor yayi ya dafa kafadar Yaya Shamsu yace “har cikin ranta take cewa waye wannan bansanshi ba Ummah waye? Shamsu abinda yake wasa daga farkon farashi zaka gane wasane, da gasken gaske Zuhurah takeyi ta mantani" daga haka bai Kuma cewa komai ba ya fice daga gdan Baba yanata jiran dawowarsa Amma Shiru Koda ya kirasa a waya sai yace shi bazai iya zama Ina kallonsa matsayin baqo ba.
Kwanaki uku ban sanyashi a idona ba nama manta da babinsa na shiga wata sabgar daban dake lkcn muna gaf dayin saukar qur'ani a islamiyyar mu hankalinmu yanakan bikin saukar dagani har Aunty Naja'atu munata qissima irin kyaun da mukeso muyi ranar sauka, ranar wata laraba munje kasuwa tun safe da Ummah siyo mana kayan sauka ashe mu munacan bamusan wainar da ake toyawa a gida ba,Qarfe uku muka nufo gdan dukkanmu a gajiye muke musamman ma ni me garin jiki tafiya kadan ke wahalar dani, Ummah nata yimin tsiya Wai auta ta cika raki nikuwa sai zumbura baki nakeyi haka muka shiga gda da sallamarmu sallamar da ta maqale a maqoshinmu ta kasa samun lamunin fitowa,
Kinsan meye ya maqalar da sallamarmu Suby? Zuhurah ta tambaya, da sauri Suby tace “aa inajinki don Allah ki tafi a miqe ki daina kwana kwana" murmushi tayi me hade da hawaye tace “masomi kenan, mutane muka gani cike da gidanmu dangin babanmu matan yayyansa da qanwarsa Baba Zaiba a cike taf da tsakar gidanmu sunata hidindimunsu ga maqota nan sai kaiwa da komowa sukeyi,
Haka muka qarasa jiki a sanyaye idona yakai inda naga matan unguwarmu sun duqufa duba wani Abu kawai sai naga manyan akwatuna ne guda goma sha biyu kowannensu shaqe taf da kaya na gani a fada sunata dagawa suna "ahhh lallai Masha Allah Nuraddeen yayi qoqari Allah dai yabada zaman lfy yasa yin na Allah ne" tunda naji an ambaci Nuraddeen sai gabana ya yanke ya fadi na tsaya Ina kallon kowa daidai can wata budurwa Zuwai Abokiyar wasana ta makoni tace “Matar Nura kina sha'aninki yaudai Allah yayi aure da mara kwabo kin tabbata matar Nura kedai ke kika dace da miji bashi ya dace da Mata ba wlh"Ban fahimci komai cikin kalamanta ba duk tunanina wasan data saba yimin ne don haka nace “nifa Zuwai kina damuna da surutunku na yan qauye ke bakinki ko ciwo bayayi ne?" Ina fadin haka Ina shigewa daki kawai sai jinayi ana fesheni da turare na rintse idona da sauri Ina Kai duka Ina cewa Allah zanci uban mutum banason hauk...."
Ji nayi an rufemin baki anci gaba da fesamin turaren tsintar kaina a wata duniyar laushi ta musamman ya sanya bakina mutuwa kasala ta maye gurbin zafin Raina, Saida aka gama feshemu da turarukan sannan matan suka fice daga dakin aka barni dagani sai shi sai lkcn na samu damar sauke ajiyar zuciya tare da bude idona kawai sai naganni kwance luf a faffadan qirjinsa, na kuwa zabura da sauri nace “subhanallahi meye hakan dinne wannan ma ai iskanci ne dama bakasan haushinka nakeji ba ranar nan kazo ka wani dagani a gaban su Ummah shine yanzu zaka rungumeni a gaban mutane wannan wanne irin haline na yahudawa" nayi tunanin yanda na haqiqice Ina zuba masa masifar zaisa yaji haushina amma maimakon hakan sai naga ya qara natsoni naja da baya da sauri ya cafki hannu na yana murmushi yace “kiyi hqr My Zuhr a baya dai nasan bakya fushi da Yaya Noor dinki ko kin manta?" Kawai sai sunan ya rinqa dawo min nace Yaya Noor! Yaya Noor!! Saida na maimata yakai sau biyar sannan yace “Yes kin tunashi?" Kawai sai naji hawaye sun wankemin fuska nace “Yaya Noor ai ya mutu..." yanda nayi furucin ya sanyashi dagowa da mugun sauri yace.“Inji wa? Wanne maqaryacin ne yace miki na mutu bayan gani a gabanki matsayin da tunda aka haifeki na dauki kaina a matsayinsa a gunki wato miji Fatima kina hauka ne ke kina tunanin zan mutu batare da wannan burin nawa ya cika ba, waima meye ya goge Miki hadda akaina ne meye ya mantar dake ni dago Fatima dago ki kalleni sosai Zuhurah wlh nine Yaya Noor dinki babu abinda na canza saima rama da kalamanki na ranar dana dawo suka sanya ni"
Dagowa nayi na zuba masa ido sai Kuma nayi qasa da kaina saboda bazan iya jure kallon qwayar idonsa ba na tabe baki nace “tabdi waima miji kaidin injiwa zaka zama mijina qaryar banzan kare a gadar kura wlh Kama daina wannan mgnr donni sai nayi Masters sannan zaayimin aure......_Idan har kin kasance kinason jin qarshen lbrn nan kiyi subscribe ta wadannan hanyoyin 300 ta account number 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB ko kati MTN just hoton muke buqata ko numbers na katin ta wannan number only WhatsApp 09013718241 idan VTU ne Kuma kiyi ta wannan number 09031307566:_
_Don Allah a kiyaye kada kiyi VTU ta number farko bama buqata_~@Ummuh Hairan~
![](https://img.wattpad.com/cover/246088583-288-kcb4f79.jpg)