RUWAN JIRA......

640 32 6
                                    

*RUWAN JIRA......*
_(A true life story)_

_*Rubuta labari*_
_*Fauziyya Tasi'u Umar*_
_*(Ummuh Hairan)*_

_*Wattpad-realfauzahtasiu*_

*P 47-48*

Kallon qurilla Baba ya rinqa yi masa kafin ya sanya hannu ya dagoshi yace masa “banson sakarcin banza NURADDEEN dakai da Zuhurah duka nawane ni bazan wofintar dakai ba domin nafi mahaifinka sanin ciwonka saboda haka kaje ka kwanta da safe ayi mgnr" baba ya fadi mashi hakane kawai domin hankalinsa ya kwanta amma maimakon hakan sai ya rinqa maimata kalmar “in kwanta? In kwanta?" Yana qara tambayar kansa ya kwanta anan dai baba ya tsallakeshi ya shiga gida.
To duk yanda yaso ganina ya rasa wannan damar saboda haqiqanin fushi kowa yakeyi dashi a dangi banda mahaifinsa da Baba rahamanu da sauran yan fadarsu sai wan babanmu Baba Muminu wato dagaci da yadauki girma ya azawa kansa duk da yaji ciwon abin sosai Amma yakasa nuna inda ya dosa ya tsaya akan katanga saboda ya fahimci nuna bacin ransa ba qaramar baraka zai haihar ba,



Kwana na shidda a asibitin banida aikin daya wucce kuka anqi fadamin cewa Yaya Noor yana garin duk da zuwa lkcn nasa dutse me nauyi inata kokawa da soyayyarsa burina shine danneta da mantawa dashi Amma taqi dannuwa saidai naci burin saina qunsa masa abinda yafi wanda yayimin naci alwashin dole saina raba kaina dashi kamar yanda ya yankeni daga jikinsa ya zabi kasheni nima sai nayi masa abinda zai tsaya a ransa har mutuwarsa,
Suby kinsan meye na qudurta a Raina? Na qudurce ne Koda ace wannan cikin na jikina zai zama shine qwai na na qarshe to kuwa bazan taba haihuwarsa ba na hqr dashi har gaban abada haka nayita saqa a mugun zare hardai na qarasa kwanakina na warware saboda sanyawa Raina dangana da nayi bani nasa Allah ne yasamin ita da taimakon addu'a da iyayena suka tsayamin akai, ranar da muka koma gda ranar ne nasan ashe yana garin mun fito daga mota zamu shiga gda idona ya sauka kansa yana tsaye a rakube jikin qofar gidanmu duk ya fice a hayyacinsa yayi mugun datti kayansa duk sunyi qura kamar wani sabon kamu.
Banko qara kallonsa ba muka shige gda Ummah ta kwantar dani ta fita ta daukomin shayi tazo tana bani ya samu ya shigo kasancewar matasan gidan basanan Yaya yunus da Yaya Lawan suna gidajensu shikam Yaya sani salamatu ne ko yananan babu abinda zai iya baiyi sallama ba kawai sai ganinsa mukayi a kanmu Ummah ta miqe da sauri tace


“Lfy Nura?" Sosa kansa yayi yana kallona inda nikuma nayi qasa da kaina yace “umm Ummah Zuhurah gurin My Zuhr nazo da baby na yau zamu tafi ko My Zuhr tunda kinji sauqi, don Allah karkice aa kawai komai ya wucce su bazasu gane ba Amma ke zaki gan...." Uhmm bansan inada zafin zuciya haka ba Saida ya sunkuyo kaina na daukeshi da marin da tunda uwarsa ta haifeshi Ina tunanin baa tabayi masa irinsa ba yaja da baya da sauri yana kallona Ummah tace “meye haka Zuhurah bakida hankali ne..." Daga mata hannu nayi na dubesa nace “babynka ko babynka kazo gani ko? Kaje ka kwanta kayi bacci insha Allahu bazai qara kwana a jikina ba wlh tallahi ko shine qwai na na qarshe na hqr dashi Nuraddeen dadai na hada jini dakai gara na mutu wajen abortion din cikinna....."
Rufemin baki Ummah tayi ta dubeshi tace “kaje Nura bazata saurareka ba yanzu" hawaye yake zubarwa ya matso gabana yace “Ummah zata iya fa Zuhurah kada ki tabamin dana don Allah wlh inasonsa dukan zaiyimin yawa"


Keda baki gurin idan kin kulashi na kulashi qarshema ma na miqe na fice daga dakin Ummah dake taga bani da qwari batayi tunanin fitata daga gdanba shiyasa basuyi azancin biyoni ba hakan ya bani damar ficewa daga gdan cikin saa kuwa dan sahu ya aje wasu Mata na haye nace yakaini yan santsi wato kasuwar rimi Ina zuwa na kwance sarqata da dankunne na dana daure a gefen zanina na siyar suka auna suka bani kudina na karba na tafi, kinsan wace ta fadomin?"
Girgiza Kai Suby tayi Zuhurah tace “Merry Ina tunanin zuwanki unguwarmu Basu tashi ba kinsan dai wace Merry  na fito da wayata domin na dade da number ta na kirata bugu biyu ta daga nayi Mata mgn tanajin muryata ta gane muka gaisa nace Mata tana Ina? Tace tana Sabon gari nace ta fito inason taimakonta na gaggawa aikuwa babu bata lkc tazo inda nake na zayyane Mata komai, tare da fads Mata qudurina ta Jinjina lamarin tace “Zuhurah babyn ya girma zakisha wahala wajen abortion dinsa fah" daga mata hannu nayi nace “ko zan mutu saina cireshi" haka muka tafi cikin sabon gari wani gida ta samu likitan tayimasa bayani dama aikinsa ne yasa na kwanta a gado ya dubani sosai yace saidai ayimin allurar janyo naquda na haihu kawai amma fah yaron ba lallai ya rayuba domin bai cika wata bakwai cif ba"


Kuka ta saki me ciwo tare da dafe qirji tana maimaita kalmar “innanillahi wa Inna ilaihirraji'un" Suby dake tayata kukan tace “Allah yasa dai baki kashe danki ba?" Cikin kuka tace “na kashe Suby! banyi wata wata ba wajen amincewa da sharrudan da aka gindayamin a zuwan karuwa ce ni yanke take ya bani wasu magunguna nasha yayimin Allah har uku sannan ya sanyamin wani ruwa a hannuna, muna zaune tsayin lkc ciwo ya fara kankama babu kowa nawa sai Merry Abu kamar wasa sai gani Ina Shan baqar wahala naquda gadan gadan nayita ta kwana da yini a qarshe Saida dabaru aka cire yaron cikina dan qarami  kyakkyawan gaske me kama da ubansa, lkcn da na dawo hayyacina na zubawa yaron ido inajin zuciyata tana bugawa da qarfi abin Ubangiji yaron yanata motsinsa likitan ya dubeni shima da mamaki yace Madam babynki fine boy" Merry ce ta karbeshi bayan an gyarashi muka tafi kasancewar duk irin halin da take ciki indai angama aiki baa kwana Kai tsaye gdan Yaya Noor na nufa Merry tace bazata ba nikuwa zuciyata ta bushe so nake kawai na quntata masa naje na buga gdan dake yamma ce yazo ya bude Ina tafe daqyar na shiga gdan ya biyoni da sauri yana fadin.


“Zuhurah Ina kika shiga tun jiya ake nemanki?" Murmushin takaici nayi na miqa masa yaron da yaketa mamular hannu yasa hannu ya karba babu ko riga a jikin yaron da dankwalina na nadeshi na juya zan fita yayi saurin shan gabana yace “danane wannan Zuhurah ya akayi kika haifeshi bai Isa haihuwa ba?" Hawayene ya zubomin nace “saboda banason duk wani Abu daya shafeka a tare dani Nura ga tsiyarka nan kasan yadda zakayi da ita"
Ina fadin haka na juya na fice ya biyoni da sauri yace “ki tsaya Zuhurah na kaiki gda bakida qarfi fah" ko sauraronsa banyi ba na fice daga gdan na hau sahu ya qarasar dani gda Ina zuwa na tarar dasu sunyi dako dako suna ganina sukayo kaina kowa nayimin kallo baibai Ummah ce tace “Zuhurah Ina cikinki?" Ban bata amsa ba sai zama da nayi Ina haki ta sake nufoni daidai lkcn da Yaya Noor ya shigo dauke da jaririn dan watanni bakwai dukka sai sukayi kansa ya qaraso ya miqawa Baba yaron yace “takaimin shi Baba bansan me take nufi ba" kallona baba yayi ya nufoni da yaron na tashi da sauri nayi baya luuuuu jini na dibana zan fadi Ummah tayi saurin tareni tana sallalami nace “wlh Baba banida wata alfarma da zan iya yiwa yaronnan da ubansa idan yaga dama ya mayar dashi inda ya fito dashi nikam mun rabu har abada idan ya rayu na barmasa duniya da lahira idan bai rayuba Kuma dama haka nake...."

Wata fuzga Baba yayimin ya kwadamin mari yace “ubanki yaci uwatar mahaukaciyar zamani dan uwarki kanki aka fara mutuwar aure da zakije ta qarfin tsiya ki raba yaro da ma'ajiyarsa sannan kikai masa shi to ubanme kikeso yayi masa tunda kema uwa kin kasa" maimakon na rusuna saima na qara hawa na shige daki na kullo bugun duniya magiyar duniya naqi budewa yaron sai numfarfashi yakeyi duk suka rude bama ya Yaya Noor da yake kuka kashirban yana kiran sunana yana cewa “zai mutu Zuhurah ki taimaki rayuwar danki bakida tabbacin sake samun wani anan gaba kada kiyi abinda zakiyi nadama mara amfani a gaba Zuhurah kada kibari rayuwar yaron nan ta salwanta ki taimakeni ko dumin jikinki yaji zai samu sassauci...."
Hmmmm in kinajin asalin kunne uwar shegu to shi nayi musu duk Wanda ya Isa ya fada ya fada ni kaina a ranar bansan Ina imanina ya tafi ba Shiru ta ratsa na wani lkc ashe duka akan yaron suke can naji Yaya Noor ya rushe da kuka yace “burinta ya cika ta kashemin dana a karo na  biyu ta zubarmin da cikin wata hudu ta kashemin cikakken da dan watanni bakwai Allah kafi kowa sanin komai Kaine me sakayya Allah ka sakamin, ya mutu Baba ya mutu shikenan na rasashi shima baniga tsuntsu baniga tarko na rasa Mata na rasa dana wayyohhhh rayuwata Allah kayimin sakayya"........



Please
Comments
Share
Vote


~Ummuh Hairan~

RUWAN JIRA......Where stories live. Discover now