RUWAN JIRA.......

875 30 4
                                    

*RUWAN JIRA......*

*PART TWO*

_(A true life story)_

_*Rubuta labari*_

_*Fauziyya Tasi'u Umar*_

*_(Ummuh Hairan)_*

_Please don Allah na roqeki kada ki karantan littafi baki biya ba part 1 ne free part  na kudine just 200 VIP 500 ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB ko katin waya MTN ta 09013718241 or VTU ta 09031307566_


*P 1-2*

Tana gama wannan furucin ta fice ta barni sake da baki cikin rashin sanin abinda ya dace nayi zuciyata na zungurar ruhina da wani matsanancin kishi me azabtar da ruhi “wai mijinta?" Na maimaita kalmar nan yafi sau ashirin kafin nayi qarfin halin samawa kaina matsuguni a saman hanun kujerar dake falon na fara kissima innanillahi wa Inna ilaihirraji'un,
Tsayin mintuna ashirin da tafiyarta sannan Yaya Noor ya fito ganina a takure yasashi isowa gareni yasa hannu ya dagoni sai yaji jikina yana rawa ga wani zafi daya dauka, dago idona yayi da sauri ya kalleni sai na kawar da kaina tare da janyewa daga riqon da yayimin na nufu daki yabini da sauri yace “me...meyene hakan Zuhurah naga dai kin koreta ko?" Kamar yayimin fami na kuwa zabura nace “eh na koreta bisa rashin sani tabbas rashin sanine yasani korarta bansan alaqarku takai hakaba bansan kusancinku yakai haka ba Yaya ashe dama itama matarka ce bansani ba baka fadamin ba kaico Yaya Noor ashe dai duk gona sunanta gona ashe kaima duk nono daya kukasha da sauran mazan....."

Ji nayi ya rufemin baki da tafukan hannunsa ya fincikoni da qarfi ya hadani da jikinsa ya matseni sosai yana fitar da wani huci me zafi yace "zuciyarki tana baki hakan zata farune?" Ya fadi yana dago fuskata na sakeyin qasa naci gaba da kukana ya dagani cak ya dorani a saman kujera yace “kece kikasa na sakewa yarinyarnan Zuhurah tun farko na fada miki banasonta Amma kikayi watsi da mgn ta har tashiga jikina tayimim illah Zuhurah har cikin Raina bana hada matsayinki da wata mace a duniya bana da burin hadaki tarayya da wata mace a duniya burina Kuma tanadin farin cikin da nakeson nayi Miki shine na rayu dake ke kadai to Amma ya zanyi sama da wata hudu yarinyar nan ta samu number ta take turomin da saqwanni na soyayya wanda nasan duk sakacinki ne ya haifar da hakan,

Duk da haka nayi qoqarin hanata da daina karanta saqonninta saidai na makara duk yanda na bullo asma ta rigani nisa a hanyar a cikin watannin nan bantabajin sha'awa ko jin a Raina zan iya rayuwa da itaba saidai kawai nakasa kubcewa tarkonta har takai tana kirana mu gaisa duk da iyakar gaisuwar ce kawai  cikin kwanakinnan Kuma kawai saina samu zuciyata da son kasancewa da ita a Koda yaushe Zuhurah yanzu haka jiya babanta ya kirani yacemin Asma tace nine mijin da zata aura My Zuhr na kasa bashi amsa Ey ko aa, Allah yasani banasonta da aure Kuma ma Ina kishinki Ina kishin kaina banason hadaki da wata kuyi tarayya wajen neman wani abu a gurin...."
Ban iya jin qarshen wannan yaudararrun kalaman nasa ba na hankadeshi na kwasa da gudu na shige daki na zube a katifar na fashe da sabon kuka Ina furta “innanillahi wa Inna ilaihirraji'un Allah kasa kalaman nan su zama cikin mafarki" shigowa yayi ya zauna a gefena yana kallona zuciyarsa na sake karyewa yace “bansan yanda akayi bakina ya subuce har nayiwa Asma'u alqawarin aure ba nanda watanni biyu Zuhr Amma tunda bakiso na fasa dama baso zuciyata takeba bansan meye yake jana gareta ba"

Yana fadin haka ya miqe ya fita yafi 2 hour sannan ya dawo ya tarar ni a daki Ina kwance rijib da narkakken zazzabi da Kuma azabar zuciya bansan inason Yaya da kishinsa ba saida mgnr nan ta shigo zuciya na rayamin yanzu yace mata yanasonta fah idan na tuna haka sai naji bugun zuciyata ya nunku tana qoqarin faso qirjina, lkcn daya shigo ina zaune saman sallaya rungume da qur'ani inata kuka ni gashi ba kowane dani agarin ba bare na fita naje nayi Hira dashi naji dadi gashi saboda rashin yarda irin tawa matan ma da suke daidai dani matan lecturori bana shiga sabgarsu Hajja Mandu ce kawai ta ciri tuta itanma dan uwace to gashi ta gurinta ne barakar ta bullo nasan ko giyar wake nasha bazanje nakai mata qarar mijina akan ƴarta ba.

Zama yayi a gabana yana cewa “to Kuma menene My everlasting kece kadai kike da gurbin gaskiya a cikin zuciyata duk abinda zai zamo matsala a rayuwarmu wlh na haqura dashi ko shine qarshen farin cikina don Allah kukannan ya isa haka kinga baby na ma yanajin ki kada kisashi ya rinqajin haushina nasa mamansa kuka"
Miqewa nayi zanbar masa gurin yayi saurin riqeni ya miqe yace “haba haba rayuwar Nuraddeen idan da wata bayan ke Allah ya kasheta a daren yau kece amaryar farko Kuma kece ta qarshe, kece jini daya dangi daya yanki daya asali daya ruhi daya My Zuhr, wace ta samu wannan sufofin duk matan duniya a gurina? wace  ta samu gurbi a zuciya tun kafin zuciyar tasan sunanta zuciya, wace take numfashi numfashinta yake controlling nawa duk duniya, wace nakejin digar hawayenta kamar digar ruwan tasasshiyar dalma a qirjina tun kuwa tana qarama, wace nake rasa farin ciki da gushewar haske akan fuskarta duk duniyar nan?"

Abinka da zuciyar mace sai jikina ya mutu na qanqameshi tare da shigewa jikinsa na sake rushewa da kuka nace cikin in'ina “Yaya Kuma kace da ita kanasonta?" Dagoni yayi da sauri ya dora harshensa saman kuncina ya tsotse hawayena tsaf yace “wlh bayanke nayi alqawarin har qarshen numfashina bazan qara furtawa wata banzar mace kalmar so ba haba My Zuhr qaryama nakeyi Miki kenan idan har zan iya furta cewa inason wata bakeba"
Numfashi na sauke me qarfi na janye na kwanta ya biyoni ya kwanta a bayana ya dora bakinsa a dokin wuyana yana lasa a nutse duk ya saukarmin da kasala cikin salonsa me tsayawa a rai ya tura hannunsa cikin rigata yana zageye yatsansa saman cibiyata yana dan dannata a hankali na sauke numfashi tare da riqe hannunsa nasa nace “Yaya...." Kissing wuyana yayi yace “Qanwata" yanda yayi maganar muryarsa na shacking ya sanyani dole nayi Shiru nasan yakai qololuwar buqatuwa Kuma dama nasan yakamata ya buqatu din kusan jiya bai samu yanda yakeso ba saboda zazzabi daya hanamin sakat.

Da salonsa ya tura hannunsa can qasana ya fara lalubar HQ na yana wasa da belina yana karkada yatsansa akai wani dadi yana gigitani Ina dan budansa qafa a hankali yana qara karkada  yatsansa dadin da nakeji bamai faduwa bane a baki kasancewar Allah ya horewa Yaya Noor baiwa da hikimar sarrafa mace"
Shiru Zuhurah tayi tana sharar hawaye Suby ma tayi ajiyar zuciya tare da share hawayenta tace “kinsan meye yake sani kuka Suby?" Girgiza Mata Kai Suby tayi Zuhurah tace “Har yanzu banqara samun gamsuwar jima'i ba tunda na rasa Yaya Noor Suby magrib tayi kije gida gobe maci gaba kada Abba Na'im yaga kinyi dare"

Girgiza kai tayi tace “Ahmad yananan ne?" Murmushi Zuhr tayi tace “yaje zance inaji bazai dawo ba sai dare sosai" saurin kallonta Suby tayi tace “wai har yanzu mgnr auren tananan?" Qasa Zuhr tayi da kanta tace “tananan bata dameni ba Suby yayi din sai hankali yafi kwanciya ni yanzu burina na samu na hada kudadena na tafi Saudia nayi dawafi na roqi Allah ya gafarta min ya bani haihuwa nima ya yafemin abinda nayi nake kuka kullum wlh Suby idan kikaji kuskure daya tak da nayi a rayuwata ta baya zakiji kin tsaneni kema kamar yanda iyayena da makusantana suka wofintar dani suka qyaleni da duniya da nadamar da narasa ranar qarewarta"
Matsowa Suby tayi tace “a yaushe kikayi wannan kuskuren Zuhurah meyeshi don Allah?" Kifa kanta tayi a kafadar Suby tana kuka me taba zuciya tace “Astagfurillahi wa'atubi ilaik

_Please_
_Comments_
_Share_
_Vote_

~Ummuh Hairan~

RUWAN JIRA......Where stories live. Discover now