RUWAN JIRA.......

492 23 0
                                    

*RUWAN JIRA.....*

*Freedom writer's association📚🖊️*

*_Rubuta labari_*

*Fauzah* *(Ummuh Hairan)*


*Dedicated to*

_Mijina Abdul Sidi Isah Haruna, son so fisabillillah_❤️

_Am sorry Fan's littafin *RUWAN JIRA....* na kudine 300 ta wannan account 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB_
_Ko Kati MTN ta WhatsApp akan wannan number 09013718241, ko VTU ta wannan number 09031307566_

_Ga masu buqatar karanta tsoffin littatafai na na kudi guda tara ga sauqi yazo da 1k dinki Zaki samesu documents gabadaya memakon a baya da sai kin biya 1800 kudai kada ku bari a barku a baya ta wannan account din na sama zaki biya kudinki idan kina buqata_


*FREE 11-12*

Bata jima ba ta dawo ta zauna tana duban Suby tace “haka rayuwa taci gaba da tafiya duk wani farin cikin Yaya Noor ya ta'allaqa ga farin cikina walwalarsa tawace kukansa nawane tsayin shekaru bakwai, zuwa lkcn na fara zuwa makaranta sukuma sunyi candy Baba yana nema musu ta gaba an gama yi musu komai har Jamb sun zana Yaya Noor da Yaya Shamsu Kuma duk sun samu amma kash...
Sai Alh Sadiqu yayi gardama yace shifa wannan karon a qyalesa yayi iko da dansa ai yayi kara, Koda Baba yaje sai yake fadawa baba karatun Islam zasu tafi Tumbuktoo dake qasar Mali shida yan'uwansa,
Sosai baba yaso yaga ya shawo kan Alh Sadiqu amma abin ya faskara a wannan lkcn Yaya Noor ya Kama wata matsananciyar rashin lfy duk likitocin Kano sun tabbatar da babu abinda yake damunsa Amma sai ramewa yakeyi yana tsotsewa daga qarshe ne aka gano ashe damuwar nesa dani da zaiyi ne yasashi yake wannan ramar cikin dare Kuma yayita firgita yana kuka yana Kiran sunana idan Baba ya tambayeshi sai yace gani yakeyi ana qoqarin rabasa dani.


Nikam baa sanar dani tafiyar ba sai wayar gari nayi na daina ganinsa da fari na shiga damuwa abin har ya shafi karatuna Amma daga baya sai Baba Rahamanu yabawa babana rubutu yace abani na dangana ne, aikuwa na dangana don saida komai daya shafi Yaya Noor ya bace bat a kwanyata kamar wankin ruwa na manta dashi da duk wani Abu daya shafeshi,
Baba da Ummah sunji dadin hakan shima Yaya Noor da aka fada masa yaji dadi saboda bashi burin rashinsa ya sanyani cikin matsala shidai ya yarda ya rayu tsayin shekaru bakwai din da zaiyi cikin damuwar rashina, Suby haka abubuwa sukayita tafiya har nakai matsayin secondary SS 1 sai a lkcn ne Yaya Noor ya dawo hutunsa na farko a Nigeria, abinka da kyakkyawa yaqara kyau yayi haske sosai saidai baiyi qiba ba saima rama da kamar idona ya nunamin yayi lkcn daya dawo Bai wucce gidan babansa ba saboda ya qudurce a ransa ni zai fara gani acikin dangi aikuwa burinsa ya cika ya isheni sanye da Airmles iya gwiwata Ina shanya a tsakar gda na wanke panties dina da bra na kasancewar Allah yayimin garin jiki don wasu madauka suke nice sama da Aunty Naja'atu, saboda cikar halitta ta,


Banyi aune ba sai kawai ji nayi anyi sama dani ya qanqameni yana dariya yana cewa “burina ya cika My Zuhr ke nayi burin gani Kuma ke na fara gani na gdewa Allah daya tsaremin kena tarar dake cikin kyakkyawan yanayi" hmmmm wani abun al'ajabi mai Kama da almara Suby sai na bude idona tar akan Yaya Noor inason gane inda nasanshi amma na kasa ke da na matsawa kwanyata da tunani ma sai ta nemi yin bombing ai babu shiri nayi baya da sauri Ina haki nace “Ummah waye wannan?"
Tambayar tawa saida ta sanya Yaya Noor sakin jakarsa yayi saurin zama saboda baitaba tsammanin hakan ba, sake kallon Ummah nayi nace “wlh bansanshu ba Ummah wai shidin waye?







~@Ummuh Hairan~

RUWAN JIRA......Where stories live. Discover now