RUWAN JIRA.......

562 20 0
                                    

*RUWAN JIRA.....*

*Freedom writer's association📚🖊️*

*_Rubuta labari_*

*Fauzah* *(Ummuh Hairan)*


*Dedicated to*

_Mijina Abdul Sidi Isah Haruna, son so fisabillillah_❤️

_Am sorry Fan's littafin *RUWAN JIRA....* na kudine 300 ta wannan account 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB_
_Ko Kati MTN ta WhatsApp akan wannan number 09013718241, ko VTU ta wannan number 09031307566_

_Ga masu buqatar karanta tsoffin littatafai na na kudi guda tara ga sauqi yazo da 1k dinki Zaki samesu documents gabadaya memakon a baya da sai kin biya 1800 kudai kada ku bari a barku a baya ta wannan account din na sama zaki biya kudinki idan kina buqata_


*Last Free 9-10*

  

Zama tayi bayan ta kawo Mata ruwa da abin tabawa tana nazarin ta inda zata fara taji an dafata, dago Idanunta tayi da suka canza kala ta ajiye numfashi tare da dauke qwallar idonta ta fara da cewa.

*_Waiwaye_.*

Fatima Abubakar Dandattu shine asalin sunana Alh Abubakar Dandattu shine mahaifina mun kasance mu bakwai ne a wajensa Wanda ya kasance Hajiya Rakiya itane mahaifiyarmu, Yaya Sani shine babba sai Yaya Yunus dake bi masa sannan Yaya Shamsu sai Yaya Hadi sai Autan maza Yaya Qasim sannan Aunty Naja'atu sai ni auta Fatima,
Dani da Aunty Naja'atu mun taso cikin gatan kulawar da bata sanyamu sangarta ba duk da kasancewar Babanmu bame dukiya bane Amma Allah ya hore masa zuciyar kula da iyalinsa harma dana wasu,
Kafin nan na manta ban sanar dake ba su babanmu su bakwai ne Suma Baba Abdurrahman shine babba sai Baba Uwa wacce take mahaifiya a gurin Yaya Noor su biyun nan dakinsu daya shiyasa na hade Miki lissafi a jimla yanda zakifi ganewa amma a lissafin haihuwa Baba uwa itace ta hudu domin kuwa Baba Abdulmuminu da muke Kira Baba me mota shine da na biyu a gidan dagaci Ummaru me turare sai mahaifina Abubakar shine na uku sannan baba uwa sai Baba Abdulqadir wadannan su ukun dakinsu daya wato babana da yayansa daya da qaninsa daya,
Baba Nuraddeen sannan baba zaibu wacce itace auta a gidan dagaci Ummaru me turare Suma dakinsu daya jimillar matan kakanmu sun Kama uku kenan, Ina fatan kina ganewa?"


Daga Mata kau suwaiba tayi tace “har nayi hadda Zuhurah ci gaba da lissafi"
Numfashi ta sauke taci gaba da cewa “baba Uwa da mahaifina Abubakar Dandattu suna da wata sihirtacciyar shaquwa da duk family babu kamarta har takai abin yana sosa zuciyar Baba abdurrahamanu saboda shi dama tun farko tasu batazo daya da babanmu ba, hakanne ya janyo suke takun saqa har takai ko gaisawa Basu cika yiba a matsayinsu na yan'uwa.
Lkcn da hankali ya ratsasu bayan mutuwar Ummaru me turare sai mahaifina yaso su dawo su hade kansu amma Ina abin yaci tura domin a lkcn Babanmu ya lura bawai dashi kadai Baba Rahamanu yake hamayya ba da dukkan yan dakinsu ne kasancewar sune suka lashe kaso mafi rinjaye na dukiyar da Ummaru me turare ya mutu ya bari,
Koda mahaifina ya matsa akan su dinke barakarsu gudan kada muma mu taso mu tarar da ita, haqansa ya gaza cimma ruwa a qarshen qarshe baba Rahamanu ya dubi tsabar idon babanmu da yan uwansa yace “Kunzo a bayana kun gaje komai da mukasha wahala da Tsoho muka tara hakan bai isheku ba yar uwartawa ma guda daya sai kun rabani da ita takai ta kawo batajin mgnta sai taka Abubakar"  fasali yaja kana  ya dora da cewa “hakane wannan damarku ce kaje nabar maka Uwa duniya da lahira karta qara kallona matsayin dan uwan da mukasha nono daya sannan Abu na qarshe shine zan aurar da uwa kamar yanda tsoho ya umarceni ga Alh Sadiqu"


Wannan taro ya tashi da hayaniya, azahiri ba kalamansa ne suka girgiza Fam ba aa mgnr auren Baba Uwa da Alh Sadiqu itace ta tashi hankalin kowa, sunyi duk me yuwuwa akan hana wannan aure Amma haqa ta gaza cimma ruwa ba komai yasa suke son hana auren ba sai ganin kwara da cutarwa qiri² kasancewar Alh Sadiqu amini ne ga Ummaru me turare wato kakanmu harma ana rade²n ya girmi kakanmu.
Sosai mamaki ya cika zuciyar Fam saboda su sanannune akan yanda  tsoho yake da qoqarin tsayawa akan haqqin bani adamu to meye yaja ra'ayinsa akan hada wannan aure?"
Wannan tambaya ce da Basu da amsa haka sunaji suna gani Baba Uwa batason aurennan aka hadashi aka dauketa aka kaita gidan Alh Sadiqu cikin matansa uku da Kwantsin yaya sunfi talatin, Alh Sadiqu yayi aure aure sosai don a qiyasi ana hasashen ya auri mace sama da talatin kawai don yawancinsu basa haihuwa ne,


Hakanan baba Uwa tayi yan guje gujenta a qarshe dai Alh Sadiqu ya kafeta a gidansa shekararta biyu sai ga rabon ciki a jikinta haka ta rinqa haukan zata zubar da wannan ciki itace jiqa madaci jiqa kanwa jiqa gishiri amma ciki yaqi zubewa zamanin tsoron zuwa asibiti akeyi,
Babu Wanda baiyi Mata mgn ba taqi ji Amma ana fadawa mahaifina yaje har gidanta yayi mata fadan girma tana kuka tace “yaya wlh banason cikinnan na tsaneshi Amma tunda kace na barshi zan barshi amma da sharadin bazai rayu dani ba kaji shima Alh yaji idan na haihu zan bakashi ka tafi dashi ka hada dasu Sani sa Yunus ka riqe"
Babu wani jayayya Alh Sadiqu ya amince da wannan ta hqr ta haifemin fitinar rayuwata😭😭


Numfashi ta sake saukewa sannan ta dora da cewa lkcn haihuwa yayi Baba Uwa ta haifo danta namiji kyakkyawan gaske saidai baqine irin baqin fulanin Rano Ranar suna yaron yaci sunansa Nuraddeen sai Kuma me? Saiga baba uwa na cewa itafa abarta da danta idan ya Isa yaye ta badashi a babana, hakance ta faru taci gaba da rainon Nura har ya isa yaye ranar data yayesa kuwa ta hawo akori kura ta kawoshi gdanmu lkcn Ummah Rakiya nada tsohon cikin Yaya Shamsu haka ta karbeshi sukayi sallama ta riqeshi tamkar yayanta na cikinta babu wani babu wani bambaci da take nuna masa sai qauna da kulawa,
Wata daya da kawoshi Ummah ta haifi Yaya Shamsu daganan taci gaba da haihuwa har kawo kaina, Ummah tayi wani furuci ranar da aka haifeni lkcn Yaya Noor yanada 12 years bama ya  gida yana kasuwa aka tashi dan aike domin a fadawa baba haihuwata kafin dan aiken ya dawo Yaya Noor ya dawo gda tana ganinsa tace.
“Miskili kafi mahaukaci ban haushi duk haihuwar da nakeyi ko barka baka taba yimin ba yanzun meye ya kawoka?" Tace sai kawai ya sosai Kai yana dariya yace “matata nazo gani" wannan kalma tabawa kowa mamaki aikuwa tundaga wannan rana wannan kalma ta zauna a bakin Fam tun Ina jaririya haka ake kirana Matar Nura Sai ya kasance sunan da mahaifina ya radamin ya bace bat dangi gaba da baya matar Nura sukece min shikuma Yaya Noor yana Kirana da Zuhurah dole iyayena ma suka maya bakinsa suke kirana da Zuhurah.


Kowa yana mamakin kulawar da Yaya Noor yake nunamin duk da dayawa suna daukan kalamansa shirme na quruciya amma ayyukansa suna bayyana gaskiyar girman yanda ya dauki lamarina Yaya Noor yanayin kuka idan Ina kukan yarinta na quruciya idan Ummah tayi masa mgn sai yace shifa baisan sanda yake hawaye ba idan yaga dama Ina kuka kawai yanajin kamar wani Abu nake buqata banida damar fada.
Haka zai miqe ya rakito wancan ya hado wannan duk ya hargitsawa Ummah gda don farin cikina ni kadai idan kuwa naqi Shiru to kuwa kudi kona uban waye zai dauka ya saceni mu fice daga gdan yaje ya kasomin bazai dawo dani ba sai yaga ina dariya
Miqewa Zuhura  tayi  Suwaiba ta riqota tace “ya zaki tashi Zuhura kin fara sanya idona tsiyaya Wai dama ana haka da gaske?" Kallonta tayi ta qaqalo murmushi me kama da yaqe tace “tun yanzu Suby ai baki fara kuka ba zan duba abinci ne na sauke haqqin me gda kada na shagala Allah ya hukuntani da hukuncin da yafi wannan wlh Suby haqqin Yaya Noor yake bibiyar rayuwata ya hanani kwanciyar hankali, ki dan jirani kadan kada ki gaji so nake kiyimin alqalanci keda me karatu.....


_Idan har kin kasance kinason jin qarshen lbrn nan kiyi subscribe ta wadannan hanyoyin 300 ta account number 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB ko kati MTN just hoton muke buqata ko numbers na katin ta wannan number only WhatsApp 09013718241 idan VTU ne Kuma kiyi ta wannan number 09031307566:_
_Don Allah a kiyaye kada kiyi VTU ta number  farko bama buqata_




~@Ummuh Hairan~

RUWAN JIRA......Where stories live. Discover now