*_RUWAN JIRA.... BOOK 2_*
*_Ummuh Hairan ce_*
_*Wattpad-realfauzahtasiu*_
🅿️7️⃣▶️8️⃣
Yanda yake kallona yana nufoni jikinsa na tsuma Saida hanjin cikina suka kada na fara ja da baya tunanina rufeni zaiyi da duka sabanin haka sai naga ya durqushe a gabana ya Kama gwiwowina ya dora kansa akai ya bude bakinsa muryarsa na rawa yace.
“kiyiwa Allah kidaina fitomin da qiyayyarki Zuhurah babu yacce zakiyi dani babu yanda zanyi dake mun riga mun zama daya arziqin yarannan da zasuzo su shiga tsakanina dake Zuhurah ko a lahira wani na cin arziqin wani balle ni da banyi Miki wani abu daya cancanci ki qini ba, ban hanaki komai na jin dadin rayuwa ba kece kika takura kanki kikaqi fadada tunaninki kike ganin kamar na tauyeki Zuhurah kada zuciya ta kaiki ta baroki itan mugun namane da take gurbata daga sha'awe²n duniya qarshe Kuma ta kaika inda zaka fadi faduwa irinta qosasshen doki kinsani cewa idan ya fadi baya tashi, to nidai Ina qara neman alfarmar ki soni kiyi domin ki faranta min kodan arziqin yaya....."Yana rufe bakinsa wayata dake gefe ta dauki ring yakai hannu ya dauka idanunsa ya sauka akan sunan tuni naga ya zabura ya miqe ya dubeni jikinsa na tsuma kinsan buzun namiji da baqin kishi yace “zancen kenan ko?" Jikina yana rawa ya danna wayar ya kunna record ya miqomin tsoro ya lullubeni ya zaremin ido murya na rawa nace “he...hello" a daya bangaren Yaya yace “My Zuhr inason ganinki yau don Allah kiyimin alfarma ki samu ki fito ko a gidane naganki zuciyata tayi sanyi nifa yanzun ni kadai nake rayuwa da zaliha da Samira duk na sallamesu bazasu iya daniba sun kasa yimin maganin matsalata ke kadai ce maganina...."
Cire wayar yayi daga kunne na yayi murmushi me ciwo tare da datse Kiran sannan ya kashe gabadaya ya fice da sauri bansan Ina ya nufa ba nidai naga fitar motarsa a guje na koma na zauna zuciyata na bugawa tsorona ya nunku tunani na ya tafi akan kada yayiwa Yaya Noor wani abu haka nayita kaiwa da komowa har dare wajen 9:00pm Sister Mardiyyah da taga bai shigo ba ta dauko kayan abincin ta hawo samana dake yinin ranar ce Mata nayi banida lfy ta zauna ta hada Mana abincin tanata jana da hira nidai binta nake da eh aa Amma kacokan hankalina yanaga Alh Lukman,Ban iyacin abincin kirki ba ta Kuma fita ta damo min kunun Cous-Cous da yasha madara ta kawomin saboda taga naqicin abinci Allah Sarki Mardiyyah yar aljanna ta rinqa takuramin da rarrashi da komai saidai taga nasha sannan ta qyaleni tace “mijinki bai dawo ba Allah yasa dai lfy" gabana yabada wani rass nayi qoqarin basarwa nace “inajin filin atisaye ya wucce daga kasuwa...."
Tsinkayo muryarsa nayi yana cewa “wlh Paradise inacan muna atisaye duk na gaji Qurratul Ainy a bani wani abun nasa a cikina" miqewa sister tayi tace “duk kasamu a damuwa My qanwa ko abinci ta kasaci...." Zaro ido yayi yace “for what?" Sai nayi qasa da idona cike da tsoro da mamakin ganin ya shigo fuskarsa a sake babu alamun wata damuwa, jinayi yana shafa cikina qato dashi yana murmushi yace “cikinnan yayi girma da yawa Qurrah anya ba uku bane" dariya tayi tace “kaikam Hero ka cika zari wlh uku Kuma ai saika sanya qanwa kuka biyun ma tace dame zata rainesu" kafin na ankara yasa hannunsa ya fito da nono na ya shafa yace “danan bari kiga yanda zakike shayarmin da baby's dina" wannan dabi'a ta gidansa tana bani kunya shidai baisan kunyar idon kowa ba ko ita ya Kama haka zaiyi Mata a gabana dole zama tasa ko kinajin kishin ki daina,
Itama dake ba ariyar ce yar uwan dayan sai cewa tayi “ai baka iya ba dana dama ake farawa" ta matso ta Kama kansa ta wani saita masa kamar yaro qarami ai kafin ya Kama na zabura na miqe ya miqe shima yace “wlh sai nasha yarinya garama ki tsaya" bazan iya hawa sama ba hakan ya sani nufar dakin qasan da gudu na datse qofar inajinsu sunamin dariya yana cewa “dubi yanda take gudu kamar agwagwa matsoraciya kawai" nidai inajinsa naqi fitowa Saida ya gama abinda zaiyi naji ya haura sama sannan na fito na nufi saman Ina Shirin shiga dakina naji yayi wuf ya riqoni ya dagani cak bai saukeni ba sai a gadon dakinsa Koda ya saukeni din bai qyaleni ba saida ya gurjeni sosai numfashina har daukewa yake saboda azaba kafin ya qyaleni yana mayar da numfashi yace.