RUWAN JIRA......

667 36 5
                                    

*RUWAN JIRA......*
_(A true life story)_

_*Rubuta labari*_
_*Fauziyya Tasi'u Umar*_
_*(Ummuh Hairan)*_

_*Wattpad-realfauzahtasiu*_

*P 57-58*


Washegari baqi suka tafi suka barni nida halina da sabon mijina Wanda nakejin tsanarsa kamar na kasheshi shikuma bayan yakaisu airport ya dawo yazo ya matsamin lamba taba can shafa can goga can dadai naga ba dan arziqi bane saina sulale na gudu daki na kulle na dauki wayana na lalubo number Yaya Noor  a wata takarda dana rubuta na saka a sabon layin da Alh Lukman yasamin tun daren jiya.
Kira na somayi tanata ring baa daga ba harta katse na sake kira, a haka Saida nayi sau uku sannan aka daga duk da muryar Yaya Noor me sanyi ce dama can amma sanyin ta yau tafi ta kullum yace “Assalamu Alaikum" ajiyar zuciya nayi nace “Yayana" sai naji yaja numfashi tare da alamun gyara kwanciya kodai tashi zaune yace “My Zuhr ashe Ina ranki meye tsohonnan yayi miki daren jiya?"
Jikina ne yayi sanyi nace “ya jikinka Yaya naso nazo na dubaka su Baba suka hana Amma Ina fatan kaji sauqi?" Gwauron numfashi ya sauke yace “sauqi Kuma Zuhurah nine zanji sauqin? Hmm kina wasa da zuciyar masoyi ne My Zuhr wlh bazan tabajin sauqi ba harsai ranar dana jiki a jikina matsayin matata ta sunnah Zuhr, kinsan me?"

Sai naji yayi shiru nima cikin karayar zuci nace “aa Yaya meyene fadamin?" Sake sakin huci yayi yace “Inasonki da kishinki wlh ji nakeyi kamar na kashe kaina Zuhurah waini Nuraddeen Ina raye Amma matata daya tal matar yaro a duniya ta zama ba tawa ba matar da nakeyiwa so na fansar ruhi, Zuhurah naso ace da zuciyata ta harba dinnan bugawa tayi na mutu gabadaya kowa ya huta...."
Da sauri na katseshi da cewa “aa Yaya karka mutu don Allah ba yanzu ba ka bari saina kaso wannan auren mun sake zama ma'aurata kodon na samu ladan yi maka takaba" murmushi ya sauke yace “are you sure?" Kamar Ina gabansa nace “yess" tare da Jinjina Kai alamun tabbatarwa yayi ajiyar zuciya yace “na yarda dake Amma qarqashin zuciyata yana fadamin bayan tiar akwai wata caca Zuhurah banson kibama mutumin nan dama ya fasa gardinki sau daya tak idan ya kusanceki kin tsarkaka don Allah kada ki qara yarda dashi...." Ya qarashe mgnr yana sarqewa nayi saurin tararsa dason kwantar masa da hankali nace “nifa dayanma banaso jiyama cewa nayi masa period nikeyi yau kuwa kulle qofata zanyi...." Da sauri ya dakatar dani da cewa “ya Isa haka Zuhr kada ki fasamin zuciya don Allah kwanta kawai Saida safe"

Qit ya kashe wayarsa na tsaya sake da baki inajin kamar nayi tsuntsuwa na tafi gareshi Amma Babu hali dole na miqe na zari safa da marwa inason tantance ta inda zan fara dama lissafin Alh Lukman, duk tunanina ya qare na kasa gano mafita hakan yasani dole na shiga wanka na fito daure da towel na tsaya gaban dressing mirror na shafa farar hoda na zura doguwar rigar bacci na shimfida pray mate nayi sallar magrib Ina tsaka da azkar naji qofar ta bude batare da ansa mukulli ba na juyo da sauri sai naga Alh Lukman tsaye jikin qofar sanye da kayan training ya zubamin qananun idanunsa da suke a lumshe nima na kalleshi da tsoro da firgici Allah ya sani banson ya ritsani a wannan yanayin ba,
Yanada kwarjini hakan yasani katse lantarkin idaniyata daga tasa shikuma ya samu nasarar takowa gareni ya tsugunna ya dago kaina ya saukemin lips dinsa me kamar atafa saboda laushi yace “barka da yamma matar Lukman" nandanan annurin fuskata ya dauke naji sunan ko dadi Amma banida ikon nunawa  hakan yabashi damar janyoni jikinsa ya zauna sosai yace “tashi kisa kayan training mu fita kiga gari" kinsanni da yawo kamar shanshani tuni na miqe shima ya miqe ya bude wardrobe ya daukomin irin nasa yabani na shiga bathroom nasa na fito Ina daure gashina nayi kyau kamar wata yar wasan Polo ya qara dubana yayi murmushi yace “kyakkyawata Allah yasa ki haifamin kyakkyawar Baby kamarki"
Turo baki nayi yayi dariya yace “very soon zanbaki ajiyar Baby na" na fahimci zancen yakeso yaja nikuwa nayi ficewata ya biyoni da sauri muka shiga wata mota me budedden sama yanaja yana kallona nima Ina satar kallonsa babu laifi yanada kyau duk da farinsa ya qara taimakawa fitowar kyawunsa sai Kuma saje da sumarsa ta buzaye a zahirinsa ba wani babba bane banjin zai wucce 43 years Amma kwarjininsa yakansa kakaishi 50 something.

RUWAN JIRA......Where stories live. Discover now