*_RUWAN JIRA.... BOOK 2_*
*_Ummuh Hairan ce_*
_*Wattpad-realfauzahtasiu*_
🅿️9️⃣▶️1️⃣0️⃣
_Alhmdllh! Alhmdllh!! Alhmdllh!! 70 pages na bayar kyauta dominku My Fan's daga wannan nagama free alqawari nayi kuma na cika nima Ina jiran naga irin halaccinku gareni ta hanyar yin subcribe da 200 dinku VIP 500 a wannan account din 0255526235 ko Kati MTN ta 09013718241 ko VTU ta 09031307566_
Saboda ciwon ya zama biyu Saida na kwana takwas a asibiti suna kula dani inashan magunguna yarana Masha Allah kamar su sukayi kansu tsabar kyau farare tas kamar babansu kwanansu uku yayi musu huduba da Khadijah sunan mahaifiyar namijin Kuma Muhammad sunan mahaifinsa ita Kuma Mardiyyah tayi musu laqabi da Aadeel da Aadeeha babu abinda yake hadani dasu sai idan lkcn cin abincinsu yayi akawomin su na basu nono so tari kunyar yanda Alh Lukman yake kafeni da ido idan Ina feeding din yaran yakansa na kasa Basu nonon sai ya fita.
Ranar dana kwana takwas aka sallameni muka koma gida nan naga asalin gata nidai sunan na haihu ne Amma Mardiyyah ita ke jegon Baba Uwa ni kadai take kula dani saboda hatta wankan Aadeel da Aadeeha Sister keyi komansu itace Aadeel rigimamme ne daya fara kuka zatace halina ya gado babansa bashida rikici, mu muna Dubai Nigeria anacan anata shagalin suna hotunan yarana sun cika duniya shahararren dan wasan qwallon dawaki Lukman Muhammad ya samu karuwar yara biyu bayan shekaru goma sha takwas da aurensa.Abinda yaketa yawo kenan a kafafen yada labarai na wannan lkc kyautukan tickets kam na yawon shaqatawa munshasu kamar babu gobe a wannan lkcn hatta bayan wayoyin matasa hoton mijina ne da yarana, ni bansan shahararsa takai haka ba saida aka haifi Aadeel da Aadeeha aikuwa munga gata a lkcn nan.
Shiru tayi tana mayar da numfashi tana dafe qirjinta don da gaske ciwo yakeyi Suby ta taso da sauri muryarta na rawa tace “meye Kuma ya samu qirjin Zuhurah?" Kallonta tayi tace “bana fatan maqiyina ya maimata kuskurena Suwaiba, ranar da nayi sati biyu da haihuwa Ina kwance a qirjinsa yana shafa bayana yanata zubamin Hira nikuma hankalina ya tafi wata duniyar daban zuciya tana rayamin dama ace Yaya Noor ne dama kaza dama kaza.....Kawai sai n hasaso muryarsa yana Kiran sunana na gyara sosai yanda zan fahimci me yakeso yace yayi ajiyar zuciya yace “kaina ya kulle na rasa me zanyi Miki tukuicin wannan farin cikin da kika bani My paradise don Allah kada kiji kunyata ki fadamin ko me kikeso a duniya wlh matsawar baifi qarfina ba zanyi mikishi Koda shi dayane damata ta duniya"
Wani gwauron numfashi na sauke tare da miqewa da sauri yayi hanzarin riqeni nace “kace komai Daddyn twins?" Da karsashinsa yace “eh komai Zuhurah" qasa nayi da kaina gabana yana faduwa zuciyata ta imani tana gargadina Amma shaidan yayi galaba akaina, jin Shirun tayi yawa yasashi cewa “tsoron me kikeji ni nayi Miki alqawari Zuhurah Ina mutunta alqawari domin shine sirrin nasarar rayuwata" a hankali na dago nace “ka cireni daga qarqashin inuwar aurenka nakeso shi kadai tak Daddyn twins cirewar da babu Waiwaye babu dawayya a cikinta Ina nufin ka rubuta min takardar saki uku Kuma a takardar ka rubuta bisa sahalewata da amincewata da takurawata yasa dole kayimin abinda nakeso bisa yarjejeniya da alqawarin da kayimin na kome nakeso a duniya zakayimin shi matuqar kanada ikon yi"Cikin abinda bai wucce 30 seconds ba saiga gumi ya jiqe Alh Lukman sharkar bakinsa yana rawa yace “a.....aa Faf.... Zuhurah ba haka nake nufib...." Kuka na rushe dashi na zame daga gadon na Kama gwiwarsa nace “kayiwa Allah kayiwa muhammadur rasulullah kayimin abinda na buqata wlh nasan Kai adalin miji ne da kowacce mace zatayi sha'awar rayuwa dakai Lukman anan gaba zan iya cutar dakai saboda nakasa koyawa zuciyata sonka don Allah kada ka duba maslaharka ka duba tawa bisa adalcinka da furucinka da kataba yimin cewa bazaka taba rabuwa da mace ba matukar ba ita ta nemi hakan daga gareka ba Daddyn twins ka taba cemin duk son da kakewa mace zaka rabu da ita da zarar ta furta bata buqatar zama dakai please Daddyn twins......"
Ina fadin haka saina kwanta flat a qasa na saka sabon kuka ya miqe yana jiri yana dafa bango ya fice daga dakin, Shiru tsayin awa daya bai dawo ba na tashi na bishi na bude dakinsa na shiga na hangeshi zaune ya rafsa tagumi sai shassheqar kuka yakeyi ga takarda da biro a gabansa na tsugunna nima Ina kuka nace “meye ribarka idan ka zauna da matar da batasonka meye ribarka idan ka zauna da matar da take kallonka a matsayin katanga ga farin cikin rayuwar....."
Rufemin baki yayi naji hannunsa zafi zum alamun zazzabi ne yayi masa dirar mikiya yace “ya Isa haka Zuhurah tunda kika nema zanyi Miki Amma bayanshi me kikeso a gurina?" Girgiza masa Kai nayi nace “komai kayimin a baya wannan shine kawai burina na yanzu" girgiza kai yayi yace “zanyi Miki Amma da sharadin saina fadawa mahaifinki sannan bazan baki yayana ba saboda zasu hanaki cika burinki idan har kin amince" ya fadan hakane saboda qauna da yasan akwai tsakanin da da mahaifiya musamman ni da yaga na dauki son duniya na dorawa yarana duk maganata tasuce shi a tunaninsa jin zai rabani dasu zaisa na janye qudurina Amma Ina nayi nisa, budar bakina sai nace.“Idan mutuwa nayi ma rayuwa zasuyi cikin salama tunda Allah ya azurtasu da wata uwar bayanni wlh duk inda nake a duniya bazanyi tunanin bayana ba saboda nasan suna amintaccen hannu" Ina fadin haka wayarsa tayi ring ya daga suka gaisa da Baba ya zayyane masa komai yana kuka kamar qaramin yaro yace “Allah ya sani inason Zuhurah Baba Amma takasa fahimtar hakan zanyi Mata abinda takeso matukar hakan zaisa tayi farin ciki a rayuwarta inayi Mata fatan alkhairi Allah yayi Mata zabin da yafini a gaba..." Yana gama fadin haka Baba yace “karka damu Lukman yi Mata abinda takeso Amma ka fada Mata kada ta tunkaro gidana wlh tallahi billahil lazi la'ilaha illah huwa kashe Fatima zanyi domin itadin ba jinina bace na tsani Fatima saboda halinta Fatima Allah ya Isa tsakan....." Kashe wayar yayi yana dubana har yanzu ban daina kuka ba saima dora hannuna da nayi akaina Alh Lukman ya matso gabana yace
Domin darajar mahaifinki da kaucewa bakinsa ki hqr Fatima Allah yanason bayinsa masu hqr da karbar qaddara...." Daga Masa hannu nayi na dauki biron da takardar na miqa masa nace “wlh Daddyn twins saika sakeni" karba yayi hannunsa na rawa ya dora biron ga takardar yana rubutun yana dagowa yana kallona wai ko zance ya bari nikam kawai da kaina nayi yace “daya ko biyu?" A sanyaye nace “uku" take kuwa ya rubutamin saki uku ya miqomin hannunsa na rawa nasa hannu na karba nima na bude Ina karantawa ya fice wani kuka me qarfin da bantabayin irinsa ba ya kwacemin na zube a gurin zuciyata na bugawa da qarfin gaske da kaina nake tambayar kaina “shikenan na kashe aurena? Shikenan bakin iyayena ya tabbata akaina? ?Mene ribata dana rabu da mijina me sona da son farin cikina meye ribata dana raba kaina da yayana??? Babban tashin hankalin gashi ance bazan qara haihuwar wasu ba, wannen hobbasa nayiwa rayuwarsu da gaba zan bigi qirji ince ni uwa ce a garesu???
Waye zai bani amsa???_Sai mun hadu a paid group My Fan's_
Comments
Share
Vote~@Ummuh hairan~