RUWAN JIRA.......

694 30 7
                                    

*RUWAN JIRA......*
_(A true life story)_

_*Rubuta labari*_
_*Fauziyya Tasi'u Umar*_
_*(Ummuh Hairan)*_

_*Wattpad-realfauzahtasiu*_

*FREE BOOK*

*P 45-46*

Sakin takardar nayi nayi wata miqewa da bansan a rayuwata zan iya irinta ba aikuwa jiri ya debeni nayi kasa na saki qara me qarfi tare da faduwa kasa luuuuu cikin daukewar numfashi da fitar hayyaci Ummah tayo dakin a guje har tana jifa da buhun garin tuwon dake hannunta suna rigen shiga ita da Yaya Yunus suka rufu a kaina suna Kiran sunana Yaya Shamsu ya dagoni cikin tashin hankali yaga jini yanabin cinyata a razane ya kalli Ummah yace “jini take fitarwa Ummah"
A azama Yaya Yunus ya fita sai gashi sun dawo da Yaya Lawan ƴan  takife ɗin gidanmu kenan suka could ciccibeni suka sanyani a sahun Yaya Lawan dukkansu suka fita harda Ummah ya rage gdan daga Yaya Shamsu sai Yaya Sani babban yayanmu sai Aunty Naja'atu har sun juya zasu fita Yaya Shamsu yayi bal da invitation din da yake cikin jini ya tsaya yana nazarinsa inda idonsa ya qara kaiwa ga takardar  zuciyarsa ta qawatu dason ganin abinda ke ciki domin yanada yaqinin shine ganina na qarshe kafin na shiga wannan yanayin.
Ya kuwa sunkuya ya dauka hankalinsa yafi karkata a takardar da yaga anyi rubutu da manyan baqi to Koda canma tsiya mukeyi masa na bai iya karatu a zuciba ya bude murya kuwa yace.

_“NI NURADDEEN SADIQU ATTAJIRI NA SAKI MATATA ZUHURAH ABUBAKAR DANDATTU SAKI UKU BATARE DA SANIN DALILI BA"_
tashin hankali wai gobarar gemu dukkansu sai suka kalli juna Yaya Sani zuciyar Mata gareshi kawai sai jiri ya debeshi ya zauna daɓar a qasa yana furta "Innanillahi wa Inna ilaihirraji'un Allahummah ajirnih fih musibati wa'akalifni khairin minha" shima Yaya Shamsu zama yayi inda Aunty Naja'atu ta karbi invitation din ta fara dubawa tuni kuka ya qwace Mata tace.
“Innanillahi Yaya NURADDEEN wannan wanne irin wulaqancine da tozarci kayiwa qanwarka jinin jikinka wadda kake iqirarin ba'ayi kamarta ba bakuma zaayi ba wannan wanne irin lkcne me cike da qunci da tashin hankali? Wannan wanne irin mugun ganine ashe dama abinda ka shirya kenan ka turomana ita gida ashe dama saboda zakayi aure kayi Mata wannan sakin wulaqancin Ina hankalinka Yaya Noor Ina tunaninka suke Hasbunallahu wani'imal wakil wannan rana! Wannan rana!! Wannan rana!!! Saki uku Zuhurah ga tsohon ciki dole ki shiga kowanne irin yanayi don Allah qanwata me kikayiwa Yaya Noor wlh hankalina yaqi daukar babu dalili yayi sakinnan..."

Tana gama wannan mgnr ta fada jikin Baba dake shigowa tace “shikenan Baba tafaru ta qare qanwa taqi aurennan kuka dage har Kuna dukanta akansa yanzu ga tukuicin halaccinku nan yayi muku Allah ya isanmu wlh Allah ya isan qanwa ya lalata Mata rayuwa ya kashe Mata burukanta na rayuwa sannan ya hadata da ciki ya sakota sakin tozarci saki uk....."

Baba da yakasa gane inda batun ya dosa saboda shi kiransa Yaya Lawan yayi yace masa yazo gida babu lfy Zuhurah na asibiti rai a hannun Allah shine dalilin zuwansa, dubansu yayi yaqa qaratan yayan nasa madaka qato dukkansu suna sharar hawaye yace “ta mutune?" Miqewa Yaya Shamsu yayi yace “ba gare mutuwa ba akan wannan wulaqancin da wannan dan iskan yayi mana saki uku a Zuhurah me tayi masa ta cancanci wannan wulaqancin?"
Zama Baba yayi ya karbi takardar dake hannun Yaya Sani farko invention din ya fara dubawa yagani ya girgiza Kai tare da cije lebe yakai dubansa ga takardar sakin ya karantata a zuci, ji yayi zuciyarsa taqi lamunta hakan yasashi karantowa a fili
_“NI NURADDEEN SADIQU ATTAJIRI NA SAKI MATATA ZUHURAH ABUBAKAR DANDATTU SAKI UKU BATARE DA SANIN DALILI BA"_  tuni Baba ya zabura ya miqe yace “eh lallai ne shege bai gaji halacci ba wato ni Nura zaiciwa mutunci na dauki yar nabashi a mutunce ya wulaqantata ya dawomin da ita babu komai zai gane yayi da dan sunnah wlh tallahi muddin Ina raye Zuhurah tabarshi har abada kamar yanda ya yanke shawarar barinta Allah ya sauketa lfy" 

Yana gama fadin haka ya juya fuuuuu ya fice yana hada hanya Allah sarki uba na gari mahaifina ya shiga tashin hankali da wannan sakin wanda hakan yayi sanadiyyar girgizar zumuncin mu domin kuwa Baba yana fitowa gdansu Nuraddeen ya nufa ya tarar da Alh Sadiqu a zaure anata fadanci ya shiga Koda ganinsa sai Alh Sadiqu ya miqe saboda yana ganin girman Baba sosai suka gaisa hawaye ya zubowa Baba yace.
“Alh kanada masaniyyar cewa Nuraddeen ya qara aure?" Babu wani alamun jin nauyi Alh Sadiqu yace “eh ya fadamin shekaran jiya wani abune?" Kallonsa Baba yayi da mamaki yace “aa babu komai Amma nasan qila bai fada maka cin mutuncin daya shirya yi mani ba ko?" Da mamaki Alh Sadiqu yace “name fah?" Hawaye Baba ya Kuma sharewa yace “ya turomin Zuhurah yau da asuba ya kirani yacemin zata taho saboda batada lfy shikuma zai tafi California so na dauka abin na arziqi ne ashe ba haka bane yanzu Ina kasuwa aka kirani nazo Zuhurah tana halin dimuwa data fitar da fitar da ita daga hayyacinta sannan tana zubar da jini yanzu haka suna asibiti, hakan yasani rufe shago na taho gida Ina zuwa na tarar da sabanin tunani Nuraddeen ya yanke alaqar aure tsakaninsa da Zuhurah kwata² ta hanyar yimata saki uku batare da wani dalili na shari'a ba ba sakin ne yafi damuna ba domin nasan idan zama ya qare babu tsumi babu dabara Amma yaronnan dake ba dan mutunci bane bai duba girmana da darajata da Kuma arziqin zumunci ba saki uku Alh Sadiqu saki uku a yata ta cikina Nuraddeen ya iya rubutashi?"

RUWAN JIRA......Where stories live. Discover now