*RUWAN JIRA......*
_(A true life story)__*Rubuta labari*_
_*Fauziyya Tasi'u Umar*_ *_(Ummuh Hairan)_*_Ina Mai farin cikin sanar daku Ina gaf da gama FREE PART 1 saboda qaunarku gareni yasa na rage muku kudin subscribe daga 300 zuwa 200 idan Kuma V-VIP kike buqata to zaki ki tura 1k, tura kudinki ta wannan account din, 0255526235: Fauziyya Tasi'u Umar GTB idan Kuma katine ki tura pin din katin ko hotonsa ta wannan number 09013718241: in VTU Kuma zakiyi ta wannan number 09031307566 pls Banda Kiran number VTU banda text_
*P35-36*
Hmmm kinsan abinda ya faru Suwaiba? Maimakon Ummah ta dauki mgn ta da muhimmanci saita kamani da fada wai rashin mutunci ne kawai yake damuna ba wata tsiya ba inba hakaba ya zaayi mutum yana iyakar qoqarinsa amma ni banida aiki sai rashin mutunci da diban albarka, haka ta rinqayimin fada nikuma Ina qara tabbatar Mata da gskyta Amma taqi saurarona qarshe ma tacemin indai ba alkhairi zan fada Mata ba kada na qara kiranta addu'a zata tayani da ita nima Kuma na dage nakeyiwa kaina.
Haka na ajiye wayar cikin sanyin jiki Ina kuka me tsuma zuciya a nan zaune Yaya Noor ya shigo ya tarar dani inata kukana ya matso gabana da sauri ya riqoni yace “meye kuma ya faru My Zuhr?" A hankali na shige jikinsa Ina shafa qirjinsa hawayena naci gaba da ambaliya nace masa“Yaya Nuraddeen" dago fuskata yayi hawayen tausayina dake qoqarin zubo masa ya zubo a cikin qwayar idona na lumshe idona tare da budewa a lkc daya nace masa “kanajin abinda nakeji a qasan zuciyata kuwa?"Saiya kalleni sosai ya bude idonsa da Koda yaushe suke a lumshe bantaba sanin yanada manyan idanu ba sai ranar ya zubamin su yana qaremin kallo a hankali cikin muryarsa me sanyi yace “me kikeji Zuhr?" Saina kwantar da kaina a kafadarsa na sake fashewa da kuka nace “kaima bazaka fahimceni ba Yaya tunda bakajin abinda nakeji kawai ku qyaleni duk ma abinda ya faru dani iyakar ni kadaine.
Hankalin Yaya ya tashi dajin furucina ya riqoni sosai jikinsa yace “ba...bani lbrn me kikeji?" Abin tausayi Kuma sai bakina ya kulle na kasa cewa dashi komai kawai saina qirqiri qarya nace masa ciwon cikine ya dameni har inajin zuciyata kamar zata fashe" ya rinqa kallona da alamun bai gasqata zancena ba Amma dake shidin ba mutun ne me son doguwar mgn ba saiya miqe ya shiga daki ya fitomin da hijjab dina da mukullin mota a hannunasa yace tashi muje asibiti"Na miqe muka fita a qofa muka hadu da Asma'u tana gaida Yaya Amma ko kallonta baiyi ba saima hade rai da yayi ya shige mota na tsaya muna gaisawa ya leqo yace “ko in tafine?" Jin hakan yasani nufarsa na shiga muka tafi, babban asibitin garin yakaini suka cajeni tsaf suka tabbatar masa da lfyta Lau tare da bani magunguna muka dauko hanyar dawowa.
A hanya ya rinqa tambayata Ina da Ina kemin ciwo nidai nayi masa Shiru domin nasan a zahiri qlau nake babu inda yakemin ciwo sai ciwon da na kasa furtashi da bakina saida muka biya wani shagon siyayya ya siyamin dogayen riguna da takalma sannan ya tsinto wasu kaya na baby masu kyau na sanyi ina kallonsa har ya gama yazo ya riqi hannuna muka fita muka isa gdaMuna zuwa wanka nayi duk jikina a sanyaye nayi sallar La'asar na kwanta saboda jikina dake ciwo Ina kwanciya kuwa bacci ya daukeni, hmmm saime? Ai sai wani Abu me kama da almara ya faru dani kamar bacci kamar ido biyu naji cikina yana wata irin juyawa kamar ana garamin amagari.
Aa can basai naga wani hanu me tsayi yana saukowa daga sama ba Ina ja da baya da baya har hannu yazo saitin cikina kawai sai fuskar Yaya Noor ta bayyana a jikin hannun ya budemin bakinsa haqoransa sunyi baqin qirin sai zaremin ido yakeyi kwatankwacin Wanda yayimin dazu, Ina wannan kallon nasa naji wata murya me amo tana cewa dani.
Badai kinqi zubar da cikinnan ba to kuwa zamu cireshi ta qarfi mu kasheki mu kashe banza....." Inajin haka na qwalla qara ina Kiran Yaya kayi hqr zan zubar wlh zan zubar ai Kaine kaqi barina naje na zubar...." Ban qarasa mgnr ba naji an rufemin baki da qarfi nayi wani juyi na diro daga kan kujerar.Ina wani haki hadi da uban gumi dake ketomin kawai sai naga Yaya ya bude qofa ya shigo Kuma sai daidai lkcn hannun nan ya bace bat fuskar ma me kama data Yaya ta bace tanamin dariya, nikam banda tsuma da ambaton sunayen Allah babu abinda nakeyi.
Da sauri naga ya aje kayan hannunsa ya nufoni na kuwa miqe da azama nayi baya Ina cewa “kada ka tabani Yaya inaneman tsari dakai da sharrinka" saiya tsaya yana kallona na kuwa qara kwashewa a guje na shige daki na garqame yayi bugun har ya gaji naqi budewa tun daga ranar ya zamemin musiba indai zan kwanta bacci Kona Rana ko na dare sai nayi wannan mugun mafarkin
Ke takai har ido biyu ma sai naga wata gajerar Mata da qoqon jini a hannunsa tana bina tana kibani da... Zuhurah jini.... Jinin dan cikinki job nin Nuraddeen nakeso...." Idan nayi addu'a saita kama dariya idan nayi ihu saita bace bat,Qarin tashin hankalin idan muka kwanta tare da Yaya cikin dare zanji kamar an tasheni idan na tashi sai naga bakinsa ya dawo goshinsa kunnansa ya dawo kumatunsa hancinsa ya baje ma'ana babu shi ya budemin baki yana cemin.
“Jini.... My Zuhr zansha jini...." Idan nayi nufin tashi sai kawai ya janyoni ya antayamin wutsiya yayita cina har gari ya waye, Suby duk na susuce na rame na lalace tsoro da fargaba suka shigeni na rasa gane gaskiyar abinda ke faruwa dani abin mamakin Kuma idan gari ya waye sai Yaya yayita yimin mitar na daina yarda dashi tsayin kwanaki shi ya gaji da wannan wofintar dashi din da nakeyi.
Cikin tsoro zance masa jiya ba kayi ba sai yayita fada wai Ina rainansa hankali shi mahaukaci ne da zaiyi kwanciyar aure dani Kuma yazo yana qorafi da safe.Nan na qara shiga damuwa gashi nakasa fitowa na fada masa asalin abinda yake faruwa dani bama shiba duk wani makusancina, ramata kullum qara tsananta takeyi Yusrah ce ta fahimci rashin walwalata tayi yawa take ta fadawa Hajja Mandu karon farko ta tako tazo gdana tasani a gaba tanamin addu'a tana tambayata meye yake damuna.
Abin mamaki sai kuwa na zayyane mata komai nan hankalinta ya tashi ta bani addu'o'i sannan tace na rinqa zama ko yaushe da alwala nayi Mata godiya ta tafi akan cewa zata nemi Yaya suyi mgn shima yayi quruciya daya kasa gane inada matsala.
Ashe banidin aka damu dani ba cikin ne baaso a jikina to sai abin yazo daidai da wani furuci da nayi a daren da cikin zai fita Yaya ya dameni na bansan na furta mgnr ba a zahiri ashe Wai tashi nayi cikin dare na tasheshi nace masa wlh Nuraddeen cikinka bazai qara kwana a jikina ba" nidai kawai naga da safe ya tashi yanata kumburi to dake bancika son damuwa ba saiban kula ba.Hajja Mandu na tafiya kawai sai na miqe domin fara aiwatar da abinda tacemin na nufi bathroom da nufin yin alwala kawai sai naji wata guda a bayana cikin gudar naji ance “lkcn shan jini...." Kafin na kamo zaren addu'a kawai naji an daki qasan cibiyata da mugun qarfi.
Saida nayi baya nayi tafiya ta kafa biyar daga inda nake cikin halin azabar ciwo sannan na fadi qasa tik kawai sai jini ya ballemin gashi ni kadai a gida kafin gushewar hankalina sai naga wani kwali da qullin magani sun fado daga sama sun dira akan center table dina still naga wannan matar me bani tsoro tazo ta kwarfi jinin ta bace bat.
Daga haka banqara sanin inda kaina yake ba sai bayan kwanaki hudu na bude idona da salati a bakina na saukesu akan Yusrah da Hajja Mandu dake zaune a gefena na kalleta sosai tare da yunqurin miqewa daidai lkcn da aka bude qofar aka shigo Yaya ne ya kuwa sauke idonsa akaina da wani kallo dana kasa gane wanne irin ne, ya sake dauke idonsa yace “hajiya tunda ta farka zaku iya tafiya mun gode Allah yabar zumunci"Hajja Mandu tace “aa Nura adai sallameku saimu tafi" baice komai ba ya koma ya zauna kawai ya hade Kai da gwiwa inajin yana sauke ajiyar zuciya, inata kallonsa cike da mamakin yanda ya kalleni ya watsar batare da ko sannu ta shiga tsakaninmu ba.
Sake dagowa yayi ya dubeni na yan mintina sai naga idanunsa sun kada alamun cikin matsanancin bacin rai yake, daqyar nayi qarfin halin cewa “Yaya...." Kamar me jiran nace din saikuwa ya miqe ya matso gabana ya durqusa, kawai daiya kamo hannu na ya dora kansa akai ya fashe da kuka.
Zuciyata ta buga da qarfi inason mgn amma na kasa can bayan yayi iya yinsa sai ya dago ya zuba idonsa akan fuskata yace “Allah ya jarrabeni da sonki son da nake kasa daukar mataki akan abinda ya dace na dauki matakin akanki Zuhurah Amma kisani kin cutar dani Kuma kin zalumceni bazan taba yafe miki salwantar min da gudan jinina da kikayi ba, Zuhurah wanne irin qi kikeyimin hakane, me nayi Miki da zafi haka da kika hanamin rayuwa farin ciki............_Please_
_Comments_
_Share_
_Vote_~Ummuh Hairan~
