*RUWAN JIRA....BOOK 2*
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
_Part 2 na kudine ki biya tanan VIP 500 regular 200, account 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB ko Kati MTN ta nan 09013718241 or VTU ta 09031307566 wadanda suke Niger zasu tuntubi wannan number ta WhatsApp +227 84 50 64 76_
2️⃣3️⃣▶️2️⃣4️⃣
Tana fadin haka ta juya a qufule zata fice yasa hannu ya fincikota ya dalla Mata mari kafin ya gama sauke hannunsa ta daukeshi da Wanda yafi wanda yayi Mata yana qoqarin daidaita nutsuwarsa ta sake daukeshi da wani marin ta nunanshi tare da wawuro wata wuqa dake soke jikin kankana tace “durun uwarka yau idan ka fasa dukana Ahmad ni dakai shege ka fasa a gdannan an daina daganka kafa dan uban babanka ko an fada maka tsoronka nakeji, Allah ya tsine maka albarka yau idan ka fasa sakina, wlh idan ka fasa ma ba Saratu ta haifeka ba sannan ka sani ko kafasa sai nabar tsinannen kangon gidannan Kuma yayanka nima bazasu kwana a inda nakeba ka nema musu uwa ba Zuhurah ba Zuhurah uwar Aadeel da Aadeeha ce..."
Shammatarta yayi ya shaqo wuyanta tsammaninsa zaiyi nasara amma cikin rashin saa ita Kuma tasa kaifin wuqar ta yankeshi a gefen hannu nan take jini ya balle ganin jinin yasashi hada kanta da bango ta saki wata azababbiyar qara ta sulale a qasa abinda ya janyo hankalin yaran suka fito suka nufo dakin a guje gabadaya hudun sukayi kanta twins suka fada jikinta suna jijjigata suna fadin “Mammah ki tashi kada sanyin tiles ya shigeki Mammah waye ya dakeki...." Da sauri Husnah tace “Abbanmu ne dama ya saba dukanta mugu azzalumi kawai Allah saiya saka...." Dauke yarinyar yayi da mari ya dura Mata ashar yana qoqarin treating jinin dake zuba a hannunsa daidai lkcn da Aadeeha ta dauko ruwa ta zubawa maman nasu ya miqe ya nunasu da yatsa yace “dan kutumar ubanku ku ficemin daga gda yan iska yayan zina daku da uwar taku duk bana buqatarku ku dauketa ku fice da ita na saketa saki biyu shegiya irin maita wato da kasheni kikayi niyyar yi......" Numfashi ta sauke daidai lkcn daya wullo Mata takarda ganin takardar yasa gabanta faduwa ta yunqura ta miqe da sauri ta karanta takardar kanta na juyawa saboda ba qaramar buguwa tayi ba.
Jikinta ya qara sanyi wasu hawaye masu dumi suka zubo Mata cikin hausar yaron da bata fita sosai yace “Hur are you da kake dukamin mammah....." Hannu takai ta rufewa yaron baki ta miqe da qarfin hali ta Kama hannunsu ta dubi Ahmad tace “na godewa Allah daya kasance rabuwata dakai ya zamo sanadin yayana ba yayanka ba na godewa Allah daya kasance ban cutar dakai ba iyakar zamana dakai na godewa Allah karon farko na rabu da miji salin alin batare da jin ciwon rai ko qunan zuciya ba am sorry fah don Kaine da sannu a yanzu da nan gaba tun yanzun ma zaka fara amsa sannu dan Kaine ka kwana a ciki"
Shiru tayi tana sauke numfashi kafin ta dago tayi masa wani murmushi na mugunta tace “kasan ko banki idan yana binka kudi ka kasa biyansa yakan riqe kadararka ya baka tymes kaje ka nemo masa kudinsa idan lkcn ya cika baka kawo ba zai kadawa kadararka qararrawa ya siyar ya zame kudinsa yabar maka yan canjin, so Ahmad kake ko?" Bisa adalcina na baka nan da sati uku tun dagakan pants dana siyawa yayanka har zuwa school fees zuwa ciyarwa da nayi tsayin 8 years yana rubuce na kashe musu zunzurutun kudi har 3.5 banda issue na health shi wannan nabarshi a matsayin sadaka ga talakan da ya kasa, yawwa sai Kuma mu dawo kudadena daka karba yana rubuce kasa hannu nasa har 5.8 millions still motar da ka bare jiya ka hau kasan arziqin aure yasa nayi maka Shiru bawai don ka isa hawanta ba course Ina tunanin babu ko biyar ta Hajiya Saratu a ciki itama rent nabaka ka hauta sau biyar daga jiya zuwa yau duk hawa daya 15000 sai ka lissafa kaji ya lissafin zai kama, idan ka gama calculation ka fadamin nawa zaka cikamin idan da ragi sai nayi maka Amma kafin nan bari na Kira lauya na yasan me ake ciki"Tana fadin haka ta figi yaranta ta fice ta kulle gidan da key ta zare sannan ta shige daki ta datse saboda tsoron kada yayi yunqurin kasheta tana shiga ta Kira Jami'an tsaron gaggawa babu bata lkc kuwa sai gasu a gidan maigadi da baisan me ake ba ya bude musu Ahmad ya leqo ta window yaga yanda ta cika masa gida da Jami'an tsaro qirjinsa sai dukan tara tara yakeyi lallai ashe Zuhurah masifa ce baisani ba bayan qoqarin yasheshi da tona masa asirin da takeyi harda shigo da hukuma cikin mgnr, Babu bata lkc gumi ya jiqashi sharkaf yau ya debo ruwan dafa kansa yasan ba gidansa ba wannan kangon injita da fada ko da kansa zai hada bazaikai biyanta abinda ta lissafa masa ba tabbas da yasan abinda zai janyowa kansa kenan da baiyi fuffukar iska ba yabita a yanda takeso da yasani ya Kama yayanta ya rungume an rabu lfy yanzu gashi ya fadi babu nauyi,
Ji yayi an bude qofar ga mamakinsa sai yaga itace a gaba sai Yaya Lawan dan tujara kenan ki a dangin Zuhurah yana tsoron Lawan da Yunus, bayansu Kuma Jami'an tsaro ne sai lauyanta da wani mutum, murmushi tayi tace “Mal Wada ka duba gdan sosai kayi Masa qima bisa adalci babu cuta babu cutarwa" tana fadin haka ta matsa jikin wata loccar ya nufota da sauri ta miqe ta daga Masa hannu tace “don Allah kada ka batawa kanka lkc Ahmad dare qarayi yake neman gurin kwana a garin daba na ubanka ba akwai wahala" wasu takardu ta dauko ta miqawa lauyan tace “wannan sune takardun yarjejeniyar bashi da mukayi dashi tun dagakan rainon yayansa abinda zasuci suturarsu da makarantarsu ku lissafa kugani zaikai nawa"
