*RUWAN JIRA.....*
*Freedom writer's association📚🖊️*
*_Rubuta labari_*
*Fauzah* *(Ummuh Hairan)*
*Dedicated to*
_Mijina Abdul Sidi Isah Haruna, son so fisabillillah_❤️
_Am sorry Fan's littafin *RUWAN JIRA....* na kudine 300 ta wannan account 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB_
_Ko Kati MTN ta WhatsApp akan wannan number 09013718241, ko VTU ta wannan number 09031307566__Ga masu buqatar karanta tsoffin littatafai na na kudi guda tara ga sauqi yazo da 1k dinki Zaki samesu documents gabadaya memakon a baya da sai kin biya 1800 kudai kada ku bari a barku a baya ta wannan account din na sama zaki biya kudinki idan kina buqata_
*Free 7-8*
Shaqarta yayi da dukkannin qarfinsa yana neman aikata lahira gabadaya ta fice a hayyacinta lkcn daya saketa ta fada gadon tana kokawa da numfashinta yasa kai yayi ficewarsa zuciyarsa na suya ya zauna a parlour, daqyar ta samu numfashinta ya daidaita ta miqe ta watso ruwa saboda gumin azabar da tarinqa ketawa ta dawo ta zauna zuciyarta da kwanyarta gabadaya sun kulle tama rasa tunanin da zatayi hawaye Kuma yaqi daina zuba a idonta.
A darennan cikin mutane ukun babu wanda yayi bacci Nuraddeen sone ke wahalar da zuciyarsa sannan yana tunanin tashin hankalin da Zuhura take ciki a wannan dare don lkcn da Ahmad yaje gida yana tambayar baasin motar yana gidan a qoqarinsa na wanketa daga zargi yace shine ya siya Mata alqawarine na shekaru bai samu damar saukewa ba sai yanzu.Ashe baisani ba masifa ya jiqo Mata danya Bayason abinda zai taba kwanciyar hankalin Zuhura idan abu ya sameta ji yakeyi kamar shi abin ya sama wasu lokutan har yafita jin abin a jikinsa yanda mijinta ya fita ya tabbatar masa yau bazatayi kwanan nutsuwa ba,
Shikuwa Ahmad kishine da zargi yake neman sanya gishirinsa hawa a dare daya yayi nadamar bibiyar ba'asin motar gashi suna zamansu lfy yaje ya jangwalowa kansa zargi harma yanajin zuciya na bashi shawarar sakin Zuhura amma idan ya tuna cewa dama hakan shine burinta da makirin yayanta sai yaji bazai iyaba, yayi alqawarin indai so yana kisa to saidai ya kashesu Amma suda sake zama inuwa daya har abada,
Itakuma Zuhura tunanin irin zaman zargin da zasu fara da mijinta shine ya hanata bacci Ta kwana tana kuka tana sallah tare da roqon Allah ya kawo Mata daukin gaggawa zuwa yanzu ba Nuraddeen kadai yake azabtuwa ba itama tausayinsa yasamu tagomashin cusawa zuciyarta kadaituwa da sake amsa sunan matarsa, a hankali ta miqe tana furta.“Mijin Fari! Mahadin zuciya bugun numfashi fansar rai da farin cikin rayuwa! Mijin fari aboki masoyin qarshe wanda idan kayi saken sonsa ya hudaka zaka mutu kana wahala da qaunarsa, zama tayi a bakin gado tace “Allah ya jiqan Baba Andee tasha fada mana cewa mijin fari sirri ne munkasa ganewa ashe wannan ranar tana zuwa, ashe haka Yaya Noor ya kwashe shekaru sama da 16 yanaji akaina amma na kasa yimasa halaccin qauna?"
Zamewa tayi daga saman gadon ta dafe kanta da yake sarawa da qarfi tace “kaico da bahaguwar zuciya irin tawa wadda bata fahimtar abinda ya dace sai bayan abin yayi Mata nisa, ya zanyi ni Fatimatul Zuhurah ina zankai qaunar mijin wata ba mijina ba?"
Sake tashi tayi tayi sujjada cikin kuka tace “Allah nafi kowa son na kasance cikin farin ciki amma nakasa samarwa kaina Allah Kaine da ragamar farin ciki kafi kowa sanin a Ina farin ciki yake, Allah idan har zai zamo yankewar damuwa ka dauki rayuwata kawai kada ka jarabceni da zama zindiqiyar baiwa me sabonka Allah idan Kuma qaddarar wahalata bata qare ba to Ina neman alfarmar ka dauke igiyar zargi tsakanina da mijina, ka ciremin son wani da ba halali ba ka dasa so da qaunar mijina uban yayana a cikin zuciyata na rayu dashi da amanar da bazata yanke ba har daqiqar qarshe....."Ta qarashe addu'ar tanajan zuciya kukanta yana sarqe numfashinta, hannu yasa ya dagota zuciyarsa na bugawa da qarfi ya mannata aqirjinsa yana shafa bayanta ta maqalesa tace “Abban Husnah don Allah kada ka zargeni wlh bantaba ha'intarka ba...." Rufe Mata baki yayi da sauri ya sanya harshensa ya lashe hawayenta ya zare Mata hijjab dinta ya kwantar da ita yana shafa gashinta cikin saa bacci ya dauketa ya jima yana kallonta kafin yayi nasarar miqewa ya dauki wayarta ya zare layukan ya zuba a toilet yabida ruwa ya jefa wayar a cikin kayansa ya koma ya kwanta,
Har yanzu zuciyarsa bata daina fada masa cewa Zuhura taci amanarsa ba domin girman tunaninsa ya kasa yarje masa namiji zai iya yima mace kyautar 25 millions batare data mora masa komai ba, da haka dai shima bacci ya daukeshi,
Da safe yana tashi yayi wanka ya fice ita Kuma taci gaba da ayyukanta kamar mara lafiya ta shirya yaran suka tafi islamiyya tana zaune a parlourn tana karatun qur'ani me tsarki domin samun salamar zuciya taji beil din parlour ns ring ta miqe ta bude,
Murmushi tayi tace “bantaba ganin natacciyar mace irinki ba Suwaiba takwas da rabi har kin fito Ina kika baro abban Raudah?" Murmushi tayi tace “wlh jiya ban iya bacci ba saboda qaguwa naji labarin soyayyarki da Yaya Noor da Kuma dalilin rabuwarku, Zuhura iyakar sanina duk inda saki uku ya biyo bayan aure to baayi zaman dadi ba duk da cewa fadin Allah ne sai ya jarabci zukatan ma'auratan da mararin junansu amma fah naku yayi yawa kinasonsa fiye da tunani shima yana sonki amma ke kullum kina proud cewa ko rabuwa kikayi da Ahmad bazaki koma hannunsa ba, don Allah bani insha"
Girgiza kanta tayi tace “banson tuna baya a wannan lkcn Amma ba yanda na iya nayi Miki alqawari Kuma zan cika bijahi rasulullah kedai ki zauna kisha lbrn sarqaqqiyar dabaibayayyiyar qauna me cike da burgewa da ban tausayi, Suwaiba ki tanadi tisue domin tare hawayenki domin da kanki kika nemi zubarsu"~@Ummuh Hairan~
