*RUWAN JIRA......*
_(A true life story)__*Rubuta labari*_
_*Fauziyya Tasi'u Umar*_
_*(Ummuh Hairan)*__*Wattpad-realfauzahtasiu*_
_Wani dalili yasa na mayar da wani bangare na labarin nan kyauta wani bangare Kuma paid part One free_
_Don Allah masu tambaya daga farko suje Wattpad dina zasu sameshu to beginning_*P 23-24*
Kallona Aunty Naja'atu kawai tayi tace “ni kaina Ina mamakin abinda ya janyo hakan wlh tallahi Zuhurah Yaya Noor dinki ne ne bai canza ba ki zauna ki qare masa kallo Zaki gane hakan Koda kalamansa na rarrashi gareki sannan ki rage fada masa mugayen kalamai Basu cancanceshi ba Zuhurah Koda ace ba shine Yaya Noor dinki na asali ba indai yaci sunan Nuraddeen to yakamata ya samu alfarma ta gurinki, kiyi hqr Kuma kiyi masa biyayya mijinki kyakkyawa me hqr da sauqin Kai gashi yana sonki...."
Daganta hannu nayi a zafafe nace “kinga ya Isa haka yar kwangila bazanyi biyayyar ba ubanwa yace su auramin shi bayan sunsan bana sonsa shima da shegen nac..." Sai kuma nayi Shiru na hadiye kalamai na saboda shigowar Ummah, wasu kayane a hannunta ta miqomin tace “maza saka kizo yana jiranki" a duniya Ina tsoron Ummah domin bata bani da dadi dalilin da yasa nasa kayan kenan na kukanGabana ya fadi ganin Yaya Noor zaune gaban Baba Ummah ta nunamin guri na zauna baba ya dubeni yace “Nuraddeen ga Fatima nan Fatima ga Nuraddeen nan mijinki ne yayanki ne mafi kusanci dake kaima qanwarka ce matarka ce don Allah ku riqe amanar juna kada kubawa shedan qofa cikin zamanku Kuma kuyi hqr musamman Kai Nura saboda samanta kake Kuma Kai kasan wace Zuhurah har yanzu hankali bai gama hadata ba"
Haka baba ya bata lkcnsa wajen yimana nasiha me ratsa jiki inata kukana Yaya Noor sai sharemin hawayen yakeyi yana bani hqr har Baba ya gama ya Kama hannuna ya damqani wa Yaya Noor yace “ku tafi cikin nasara Allah ya kade fitina ya sanya albarka a gabanku da bayanku"Ina kuka na me ratsa jiki na rungume Aunty Naja'atu da Ummah duk dauriya irinta Ummah kukana Saida yasata kuka daqyar Yaya Sani ya rabamu suka sani a mota Yaya Yunus yajamu muka tafi inata kukanW Wai ashe tashin asuba zamuyi shiyasa zamu kwana a wani hotel kusa da airport saboda kada mu makara.Saida suka gama komai suka zo Yaya Noor ya riqo hanuna na fito har lkcn kuka nake Yaya Yunus yaja tsaki yace “baka kwade shegiya da mari ubanme takewa kukan..." Dagansa hannu yayi yace “aa Yaya tafiya zakayi ka barmu kada ka qara hargitsamin ita ai dole tayi kuka rabuwa da gda lkc daya babu dadi" sallama mukayi da Yaya Yunus ya tafi shikuma ya hadani da jikinsa da haka muka shiga cikin hotel din muka nufi dakinmu ya mayar ya rufe nikuma na janye hannuna na zauna a kujera inaci gaba da kukana hakanan naji wani quncin rai yana tasomin ya nufoni na daga Masa hannu da sauri nace “Allah ya Isa idan ka qara tabani" tsayawa yayi sak cike da al'ajabi kafin na miqe na shige dakin na banko qofar kawai na kade gado na haye saboda ciwon da kaina yakeyi,
Ya jima sannan ya shigo ya cire kayansa ya shiga yayi wanka ya dawo ya hauro gadon yace “tashi kije kiyi alwala muyi sallah" Shiru nayi masa hakanan shurun ta wanzu na dogon lkc kafin yace “bakice komai ba" na kuwa ja tsaki nace bazanyi ba" kallona yayi yace “yinne bazakiyi ba ko kuwa yine bakyayi?" A zafafe nace “yine bazanyi ba" ya kuwa miqe yace “ok" daga haka bai Kuma kulani ba ya tayar da sallarsa yayi raka'a hudu yayi addu'o'insa sannan ya miqe ya sake haurowa gadon ya janyoni Ina qoqarin miqewa ya sake matseni ya Kama goshina yayimin addu'a sannan ya sakeni.Fita yayi nikuma bacci ya daukeni banji dawowarsa ba saiji nayi ya janyoni jikinsa ya saukemin kiss a goshina tare da hadeni da qirjinsa yaja wani huci me zafi kafin ya daidaita nutsuwarsa nikuma inata qoqarin kwacewa Amma na kasa dole tasani yin luf inajin yanda yake yawo da yatsunsa cikin sumar kaina yana sosamin a hankali.
Da nutsuwa bacci ya qara daukeni shima bai wahalar da jikinsa ba yayi baccinsa muna manne da juna, ban farka ba sai asuba shima ji nayi yana shafa gefen fuskata nayi miqa tare da Jan salati ya zubamin ido har na bude idona na miqe da sauri Ina qare masa kallo nace “Yaya Noor..." Sake saita injin idonsa yayi akaina na miqe na matsa gabansa Idonsa nakan qirjina na riqe hannunsa nace “ina kaje ka barni akacemi...." Sai Kuma nayi Shiru saboda kallon da yakeyimin na juya zan nufi bathroom ya riqo hannuna ya matso yace “akace me My Zuhr?" Qasa nayi da kaina hawaye ya zubomin nace “karka dameni don Allah kafiye takura wlh"Sakemin hannu yayi na shiga nayo wanka Ina fitowa na tarar ya fitomin da wasu riga da sikert na less na kalleshi da kayan a wulaqance na watsar na bude akwatin na dauko doguwar riga na saka, Jinjina Kai yayi ya tashi ya hadomin abin karyawa ya zauna yace “kin tashi lfy" banko kalleshi ba na koma zan kwanta yayi saurin riqeni yace “kiyi hqr kiyi break zamu makara" tsaki naja na bige hannunsa nace “bazanci ba na qoshi" yanda nayi masa din yasashi sakin baki yana kallona shi gabadaya tausayi ma nake basa.
Karyawar da baiyi ba kenan ya miqe shima ya dauki kayanmu ya fita dasu bai jima ba ya dawo ya dubeni Ina tsaye riqe da qugu yace “muje uwargida" fita mukayi babu me cewa wani ya budemin qofa na shiga shima ya shiga me motar yajamu zuwa airport har mukaje babu me cewa wani qala, muna zuwa babu bata lkc aka gama checking na kayanmu muka shiga jirgi abinda bantaba hawa ba muka daga zuwa qasar Mali,Mun sauka da wuri mukayi sallar azahar a NIAFOUNKA ni tunani na nan ne asalin masaukin mu ashe wai hutawa zamuyi sannan mu wucce TOMBOUCTOU, yanayin whether na qasar Mali ya burgeni Kuma yayimin dadi, Suby nishadi na baya boyuwa komai damuwar da nake ciki hakan ya sanya zuciyar Yaya Noor tayi sanyi muna shiga ya kamoni jikinsa ya dago kaina yana qoqarin hada bakina da nasa na lumshe idona tare da tureshi nace.
“nagaji Ina buqatar hutu Yaya kaina ciwo yakeyi" Kama kaina yayi yacemin sannu sannan ya dagani cak ya nufi bathroom dani na kallesa da sauri ya kannemin ido tare da dagamin gira yace “Wanka zanyi miki" sake zaro ido nayi nace “aa nidai kada muyi haka Yaya ka fita zanyi abuna ni daya" baison batamin walwalata shiyasa ya fita yabarni nayi wanka na na fito shima yayi, ya dawo yana taje kansa inabin bayansa da kallo, duk inda kyaun halitta take Yaya Noor ya samu, to Amma meye yasa nakejin qinsa har cikin jinina haka?" Tambayar da nayiwa kaina kenan bansamu damar samo amsarta ba naji hannunsa na yawo a jikina na dago da sauri ya zuba idanunsa masu kashemin jiki a cikin nawa yace “me zakici" sunkuyar dakaina nayi ya miqe yace “au na manta fah ashe baa 9ja muke ba bari na sauka na samo Miki abinda zakici kafin mu Isa Tombouctou acan komai na abincin 9ja akwai dake munada yawa yan 9ja a cikin Jami'ar"Fitarsa ce ta bani damar miqewa na rinqa qarewa garin kallo daga sama mutanen garin Basu da hayaniya ba kamar mutanen Nigeria ba kowa harka gabansa yakeyi, na jima jikin window Ina kallonsu kafin na dawo na kwanta Ina wasa da wayar Yaya daya fita ya bari na dade kwance sannan naji ya bude ya shigo ya zauna kusa dani ya bude ledar da yazo da ita gasasshiyar kaza ce sai fura da nono me sanyi ya miqa hannunsa ya dagoni ya yago naman yakaimin bakina na goce tare dasa hannuna na karba,
Murmushi kawai yayi ya gyara zamansa ya rinqa zugemin tsokar yana bani inaci tare da koramin da furar me sanyi banida wasa ta wajen abinci hakan yasa na zage naci sosai yaja numfashi da yaga na fara Raina masa hankali alamun na qoshi shima yaci ya ajiyemin sauran yaje ya wanke hannunsa ya dawo ya kwanta kusa dani muna kwance mu ba kurame ba Amma Babu me cewa wani shi dama Shiru dabi'arsa ce nikuwa na dole ne saboda babu abokin hira, dagowa yayi ya kalleni yaga yanda nake matse ido ya matso jikina yasa hannunsa me taushi ya zagaye werst dina yace “kinajin sanyi?"A zahiri banaji Amma saboda kar na barshi ya huta sai nace "eh" ashe rabon nasha wahala ne kawai sai naga ya miqe ya gyala labulen ya saki wani me duhu ya kashe hasken dakin ya fara rage kayansa ya cire riga ya cire wando ya rage dagashi sai singlet da boxes aa basai naga itama singlet din ya cireta ba, nakai idona ga qirjinsa da yake cike da gargasa naja numfashi Ina kallon circle din nipples dinsa me Fadi da cikakkiyar tsoka, sosai na shagala da kallonsa batare dana sani ba yayi miqa tare da takowa dauke da wani cup na lemo a hannunsa ya miqomin yace “kisha sai mu kwanta nima bacci nakeji"
Banyi masa musu ba na karba na shanye tas na miqa masa cup din yayi murmushi yace “good qanwata zakiyi bacci me dadi yi kwanciyarki" komawa nayi na kwanta Ina kallonsa ya dauki system dinsa ya fara duba wani abu idan yadanja lkc sai ya dago ya kalleni nikuwa zuwa lkcn na farajin wani yanayi a jikina kaina yana wata irin juyawa abubuwa suna rabemin uku uku, kafin na ankare tuni na daina ganin komai sai duhu daga haka bacci me nauyin gaske ya daukeni.........._Idan bana samun comments yanda ya kamata zan janye abuna yaseen🤗_
_Please_
_Comments_
_Share_
_Vote_~Ummuh Hairan~