WACECE NI??? BY CUTYFANTASIA PAGE NINE

252 21 2
                                    

Sanye take cikin jilbab ruwan kasa, da yake ba ranar makaranta bace ba uniform suke sakawa ba, babu komai akan fuskarta sai gumin karatu da gajiya amma duk da haka a nutse take cikin kamalarta ta kowanne lokaci.

Suna isa gida ta bude mota ta futa tana yi wa Malam Ali sannu, sannan ta rungumo alquraninta tayi hanyar shiga cikin gida, ganin bakuwar mota tayi a fake, da wani kamshi na daban wanda bata saba ji ba.
Sai tayi tunani Hamma ne ya dawo daga Kano da sabuwar mota, kuma qamshin ma nasa ne tunda shi bashi da turare guda daya, kowanne ya samu fesawa yake yi. Da wannan tunanin ta samu kwarin guiwar tunkarar cikin gidan cikinta na kiran chiroma don rabonta da abinci tun shayin safe.

A kitchen ta samu Aunty tana girki tare da Asabe, ta gaishe ta ba tare da sa ran jin amsar ta ba sannan ta wuce cikin babban parlour, sallamar ta ce ta katse a sakamakon kyakykyawan ganin da tayi a cikin falon.
Abba ne zaune a kujera 3seater, a gabansa Hamma Quraish, daga gefe kuma Kamal mijin Ya Wasila da wannan matashin da tun ranar da ta fara ganin shi bata sake bacci ba tare da tunanin shi ba.
The charismatic Salmanul Faris Bunu! Yana sanye cikin voile fari tas malum malum da hula, ya cika duka falon da kwarjini, he looks older than his age! babban mutum mai haiba da kamala da cikar zati.
Ba don sun hada idanu da Abba ba, da babu abinda zai hanata juyawa da baya, jikinta yayi matukar sanyi ta bude baki dakyar tayi sallama cikin siririyar murya mara amo.

A take Ya dago suka hada ido, tayi maza ta dauke kanta ta wuce gaban kujerar Abba ta durkusa ta gaishe shi

"Abba barka da gida"

"Barka da dawowa Ihman, ya karatun?"

"Alhamdulillah Abba"

"Me yasa kika ce Malam Ali ba sai ya kai miki abinci ba?"

sunkuyar da kanta tayi bakinta yayi nauyi, ba don bata da amsar da zata baiwa Abba ba sai don wanzuwar Salmanul Faris a wannan waje.

"Toh idan kika ci gaba da wasa da abinci zaki daina zama kina yini a makaranta Ihman! sai wani ciwon ya kama ki?"

A sanyaye tace

"Kayi hakuri Abba bazan sake ba"

A nutse ta dubi Hamma ta gaishe shi, ya amsa cikin kulawa sannan ta juya wajen su Kamal tace

"ina yinin ku?"
A tare suka amsa

ta sake cewa
"Ya kamal ya A.Wasila?"

Ya washe baki yana cewa tana nan lafiya tana gaishe ki.

Daga nan ta mike ta nufi hanyar bene cikin sanyinta, ta bar zuciyar Faris tana luguden bugun kaunar ta! wani birgeshi ta sake yi da ya gane cewa ita din masoyiyar karatu ce kamar shi, kuma fargabar kada Abba ya hana shi ita ta mamaye shi, ya gano yar lele ce a wajen Abban da Yayansu Hamma, watakila ma a wajen mahaifiyar su abun yafi haka.
Shiyasa zuciyar shi tayi tsam bayan Kamal yayi gyaran murya ya soma kwararowa Abba jawabin abinda ya kawo su!
A nutse Abban ya kalli Salman sannan yace

"Salmanu kai mutumin ina ne?"

Faris ya kaskantar da kai ya soma koro jawabi

"Ni haifaffen garin Borno ne, mahaifina Alh Yusufu Bunu ya rasu tun ina watanni uku, ni kadai ne a wajen mahaifiyata! rashin sukuni da wadata ya sanya ta kasa rikeni, ita din mutuniyar  Sudan ce, bata da kowa a kasar nan, yawon neman ilmi ya kai mahaifina kasar su Allah ya kaddara auren su.
Bayan rasuwar mahaifina ta sake aure, wani mutum mai kudi wanda ya rasa matar sa a sakamakon hadarin jirgin sama! Ya auri Mamana ne Hajiya Zahiya Zarouk as a nanny wadda zata rike masa yayansa ta raine su ba a matsayin mata ba!
Sannan ya kafa mata sharadin ko da yini baya son ya ganni a cikin gidan shi balle kwana, rashin makama da gata ya sanya Mamana amincewa ta aure shi!

wacece ni?Where stories live. Discover now