WACECE NI??? BY CUTYFANTASIA PAGE SEVEN

254 18 2
                                    

Cikin rashin damuwa ta dube shi tace

"Me zanyi mata? Bayan filasaina masu tsada da ta farfasa mun?"

Cikin tsananin mamaki ya buďe baki yana kallon Inna a ran sa yana annayawa ko dai Innan tana da tabin kwakwalwa basu sani ba?

"Inna ta filasan ki kike yi baki ga yarinya taji ciwo ba?"

Cikin kosawa Inna tace

"Waye ya saka ta hau abinda za ta faďi?"

Zai sake magana Ihman tayi maza ta roke shi da idanunta akan yayi shiru, dai dai lokacin yaran gidan suka soma shigowa kitchen ďin saboda karar da Ihman tayi a lokacin da Sadik ya matsa mata kafar ta babu wanda bata tayar ba.

Farida ce ta taho a guje tana cewa

"Innalillahi Ihman me ya faru? Ba dai faďuwa kika yi daga kan stool ďin nan ba?"

Cikin hawaye ta ďaga mata kai kawai tare da yunkurin mikewa amma azabar da ta ratsa ta ta sanya ta sake zabga wata karar ta koma ta kwanta tana nishi.

"Inna garin yaya ta faďo? Flasks zata ďauko ko?"

Cewar Farida tana kallon Inna da ke tsaye a gaban tukunya tana malmala tuwon ta tana naďe shi a leda.

"Idan zaki zo ki tayani mu karasa bismillah idan kuma maganar banza zaki dame ni da ita don Allah ku fuce ku barni nayi aikina."

Sadik bai san lokacin da ya mike yana huci ba, idanun sa sun rikiďe sunyi jajazur kamar gauta.

"Inna me yasa baki da ihmani don Allah?"

Cikin mamaki Inna ta dube shi ido a buďe tace

"Sadik ni kake gayawa haka? Ni zaka yi wa rashin kunya?"

Idonsa a rufe yake da wani irin tausayi da bakin cikin zalincin da Inna take gwada wa Ihman wanda yake ji har ciwon sa har cikin kahon zuciyar sa. Don haka ya manta da linzamin bakin shi, ya manta wacece Inna a gare shi ya buďe mata wuta

"Ba gara ni ba Inna rashin kunya ce kawai dani? Ke kuwa fa? Na rantse idan Allah ya tashi kama ki akan haqqin Ihman ba zaki sha ba Inna,wannan wane irin rashin imani ne haka? Ai ko a bola kika tsinto Ihman bata cancanci wannan kalar rashin tausayin daga.........."

Saukar mari babu zato ba tsammani ya katse Sadik daga maganganun da yake yi! Cikin wani irin huci ya ďago idon shi  suka sauka akan fuskar Hamma wanda kunnen shi ya karado mishi maganganun Sadik a hanyar shi ta shigowa kitchen din....

"Marina kayi saboda na faďi gaskiya? Karya nayi tana da imanin ne? Wanne mai imanin ne ýar cikin sa zata faďi a garin yi masa hidima baiyi ta tata ba sai ta filasan da aka sa Kuďi aka siya? Wanne me ihmanin zai dinga azabtar da abinda ya futo daga cikin sa babu......"

Wani Marin Hamma ya sake ďauke shi da shi! Habawa ai kamar wanda ya ziga shi. Cikin wani irin zafin nama ya isa gaban gas ďin ya dinga ďaukar tukwanen da abincin yake ciki yana zazzagewa a Dustin ciki har da tuwon Abba.

"Toh ba za'a karya ba yau a gidan nan ai ita tayi wahalar abincin ba wani ba. Wallahi ba za'a ci ba ai ita ďin ba baiwa bace, hakuri kuma ba hauka bane"

Ganin Sadik a haukace ya sanya Hamma zura mi shi idanu yana son fahimtar abinda yake faruwa a kitchen ďin don sam bai gane cewa wai Ihman ďin faduwa tayi ba balle abinda Inna tayi mata.
Abba da Anty ne suka shigo cikin sauri a dalilin hayaniyar da ta karaďe gidan!  Cikin mamaki duk suke kallon Sadik yana tabargazar juye abinci cikin shara yana fisadi yana Kumfar baki kamar zakin da aka shigowa keji aka kwashewa ýaýa.  Yana gamawa ya sa hannu cak ya ďauki Ihman da ke ta faman kuka tana rike da kumburarriyar kafarta ya kalli Inna Inna yace

wacece ni?Where stories live. Discover now