A stairs suka ci karo da Farida cikin irin shigar Ihman fuskar ta kamar mudubi don kyalli, kwalliyar tayi mata kyau ainun, suna kama da Farida sai dai Farida tafi ta jiki, ita kuma tafi haske.
"kinyi kyau my dear!"
Ihman ta fada cikin kulawa, Farida ta karaso ta rungume Ihman sannan ta ce
"wow! Ihman your waist is becoming smaller every day, ni kullum tumbi nake yi! naga dai duk abincin nan tare muke ci wai me kike yi ne?"
cikin murmushi Ihman ta shafa cikinta sannan tace
"ke kike noticing Hajiya, ni wadannan fi'ilin basu dame ni ba, komai shafewar cikina ko girman tumbina zanyi accepting kaina babu abinda zai daga mun hankali! kuma kun ga zaku iya ne"
"Allahu akbar my shekiya, ustaziya, imamiya....."
duka Ihman ta kai mata ta kauce da sauri tana dariya.
A wajen dinner komai ya tafi yanda ya kamata, an yi bikin cikin tsari da kamun kai, Abba yayi kashedi mai tsauri cewa idan yaji ko ya ga abinda bai dace ba anyi dinner farko anyi ta karshe a gidan shi don haka aka yi taka-tsan-tsan.
Cikin kwanciyar hankali da farin ciki aka gudanar bukin Adda Wasila aka kammala aka kaita gidanta.
kashe garin buki Hajiyar Kano suka tafi suka bar Ihman da kewa, Da yamma suna kitchen Da Inna suna aikin abincin dare Hamma ya shigo, ya dawo daga Dukku ganin mahaifin Zainab, yarinyar da yake so duk da dai bai sanar da kowa ba tukun."Baquraishe ka dade baka samu abokin naka bane?"
A hankali ya tako zuwa gaban dinning table din kitchen din inda Inna take aikin alalen gwangwani ta zuzzuba ta jere su gwanin sha'awa.
Cewa yayi"Na same shi!.... Inna wannan kamar alale ko?"
Inna tai murmushi tace
"ba kama ba shine ma"
Ya fadada murmushinsa yace
"kai Inna that's why i miss home.. inason abincin nan na gida sosai amma babu halin ci. Wani lokacin tunanin me zakaci ma ya isheka"
Cikin tausayawa Inna tace
"kullum ina wannan tunanin Baquraishe sanin ka da son cin abinci musamman na gargajiya wani lokacin in nayi wani abun kasa ci nake ina tunaka. Kana can kasar da abinda suka iya sai jagwalgwalo"
Dariya yayi sosai
"kai Inna jagwalgwalo fa kikace? chinese sun iya girki."Ihman da ke gaban oven tana ciro kajin da take gasawa mamakin Inna yana kulle mata kai......idan tana hira da yayanta da so da kulawa da jin kai kai ba zaka taba yarda ba idan aka gaya maka irin mu'amalar da take da ita ba kenan. A hankali ta sa hannunta ta goge kwallar da ziraro mata taci gaba da aikinta.
Hamma Quraish da ke lura da Ihman shiru yayi na yan wasu dakiku sannan ya dube ta yace
"ina Farida ne wai kullum ke kadai nake gani a kitchen kina taimakawa Inna ita aikin me take?"
Kan tayi magana Inna ta karbe tace
"tana taya ni itama mana. tana karatu shiyasa bata futo ba Abinda Farida ma tafi wannan zafin nama nan da nan zatai aiki ta gama ita kuwa Ihman kamar bataso haka take kamar wadda kwai ya fashewa a ciki"
Cikin jin haushin maganar Inna yace
"itama Ihman din ai tana karatun wanda ma yake haddar alqurani ai shi yafi kowa son samun kadaicewa da lokaci."
Inna sauya zancen tayi da cewa
"yauwa ya kamata fa kaje gidan Wasila yau kaga dakinta tunda in ka tafi sai sanda muka ganka."
YOU ARE READING
wacece ni?
General FictionWacece ni labari ne akan matashiyar da ta taso cikin wata irin rayuwa mai ďaure kai da jan hankali. Ba abun mamaki bane idan kishiyar mahaifiyar mutum ta tsane shi amma mahaifiyar kanta ta nunawa ďanta tsantsar tsana da tsangwama da kyara abun ban m...