WACECE NI??? CHAPTER TWENTY-FOUR BY CUTYFANTASIA

191 13 4
                                    

Har qarfe ďayan ranar washegari Ihman bata futa daga cikin ďakin ta ba, bata nemi abinda za ta sanya a cikinta ba kuma bata runtsa bacci ba, sai wani irin zazzabi da ya rufe ta ta dunkule a cikin duvet tana rawar sanyi cikin matsanancin tsoron da bata taba tsintar kanta a cikin irin sa ba.
A nutse ta dinga jin knocking ďin kofa, tun ana yi a hankali har mai bugun ya fara yi da karfi, Ihman ko hannunta ba zata iya sarrafawa ba a wannan lokacin, ta qara runtse idanu tana kwararar hawaye.

Iya Raheem ta gaji da bugu ta sauka reception ta gaya wa ma'aikatan tana bukatar su buďe mata room 316 wanda yarinyar da suka sauka tare take, tana tsammanin bata da lafiya tun jiya bata sake ji daga gare ta ba. Cikin azama suka amince domin tare suka zo, tare suka gan su kuma maganar lafiya ake yi don haka babu bata lokaci suka bi bayanta da spare key suka buďe ďakin Ihman.
Ilai kuwa sai Iya Raheem ta tarar da ita cikin halin da take tsammani.

Aka ce na Allah ba ya qarewa kuma ba duka mutane ne suka taru suka zama macuta ba domin duk wata kulawar da Inna zata yi wa Ihman Iya Raheem ta yi mata a wannan rana. Ac ta fara kashewa sannan ta samo ruwa a towel ta goge mata jiki bayan ta sanya safar hannu, domin rashin sanin health status ďin Ihman tunda wani ciwon ba'a ido ake ganin shi ba.
Ta kammala ta haďo tea mai kauri ta taimaka mata tasha sannan ta ballo mata paracetamol mai kyau ta bata tasha, tuni gami ya soma karyo mata zazzabin ya sauka, sai baccin da bata samu sukunin yi ba ya silalo ya kwashe ta. Ba ita ta farka ba sai goshin magriba, tana buďe idanu ta ďora su akan Iya Raheem wadda tayi cancelling gabaďaya schedules ďin ta na wannan ranar a dalilin Ihman.

"Sannu yarinyata! Tashi ki samu kiyi wanka da sallolin da ake bin ki"

Ba tare da Ihman tace komai ba tabi umarnin Iya Raheem ta mike ta buďe toilet ta shiga tayo wanka da alwala sannan tayi sallah ta shirya cikin doguwar riga, tana shirin komawa gadon ta kwanta Iya Raheem ta sake shigowa bayan futar da tayi ta bata damar shiryawa.

"A'a! Ki hakura da kwanciyar nan haka mana Ihman! Magana nake so muyi"

Gaban Ihman ya faďi amma kuma ba yanda zata yi ta juyar da kulawar wannan nagaryacciyar matar a gareta, domin ba don Allah ya aiko mata ita ba, da watakila ta sheka barzahu.
A sanyaye ta zauna a bakin gadon ďakin idanunta akan yatsunta wanda suka yi wani irin haske da kyau, kamar sauran jikinta, musamman fuskarta wadda ba zaka so ka daina kallo ba.

"Zamu iya magana Ihman?"

A matukar sanyaye ta ďaga kai ba tare da ta kalle ta ba.

"Tun farkon ganina da ke cikin jirgi Allah ya sa hankalina ya kwanta da ke!zaman da muka yi gefen juna ya sanya nayi miki karatu mai zurfi na fahimci yanayin ki a take kuma na soma zargin wani abu wanda zuwa yanzu na tabbatar da shi.

"Ihman tabbas akwai abinda ya baro da ke daga gida maras daďi, wannan tafiyar da kika yo babu izini ko sanin iyayen ki da mijinki domin kuru kuru ake iya gano rashin sabon tafiya ke kaďai a tare da ke, da damuwa da fargaba da kuma ďimbin tunani! Kamalarki da nutsuwa suka tabbatar mun da cewa akwai wani al'amari mai girma a tare da ke wanda naji Sam ba zan iya barin ki ke kaďai ki faďa hannun da ka iya cutar da ke ba!

"Ni da kike ganina mutuniyar Lagos ce amma a Kano na rayu nayi aure kuma tun ina qarama nake harkar kasuwancina, na kai shekara ashirin da biyar ina International business kuma babu kalar mutanen da ban gani ba, ba irin mutanen da bamu yi hulďa  da su ba. Ina da experience na rayuwa irin wanda ba zaki taba ganewa ba ýata kuma naga cases kala kala da matsaloli na rayuwa akan mutane daban daban don haka ina ganin ki na fahimci akwai wasu abubuwa a tare da ke.

"Bazan tursasa ki akan lallai sai kin gaya  mun damuwar ki ko matsalar da kike ciki ba, amma ina rokon ki Ihman saboda tarbiyyar da iyayen ki suka ba ki, saboda kyakykawar rayuwar da kika yi a baya, saboda darajar abinda yake cikin cikin ki ki gaya mun taimakon da kike bukata a wannan halin ni kuma nayi alkawari tsakani da Allah zan baki kowanne irin taimako ne idan har ba zai cutar da ke ko abinda yake cikin ki, ko kuma al'ummar musulmi ba.....".

wacece ni?Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin