WACECE NI??? CHAPTER THIRTY-FOUR BY CUTYFANTASIA

253 20 4
                                    

Maigoro Estate,
Accra Ghana.

Haqiqa bahaushe yayi gaskiya da yace "a bar zuciya da abinda take so". Kai idan ka kalli Sa'id ba zaka taba cewa shi ne wannan murdadden bahagon mutumin da bai san walwala ko farin ciki ba. Ba zaka ce shi ne ya dinga kokawa da mutuwa yan kwanaki qalilan da suka wuce ba, ya samu lafiya sosai, ya samu nutsuwar da iyalansa basu taba ganinsa a cikinta ba, yayi fresh kamar wani sabon saurayin da ya sauka daga Turai, yayi kyau a dalilin murmushi da far'ar da suka yi wa fuskarsa ado, ya dawo cikakken mutum mai nutsuwa da kamala da kwanciyar hankali.
Duk wadannan chanje chanjen kuma sun samo asaline da budar idanun da yayi ya ga Ihman by his side at his service. Wata tsoka guda daya a miyoyin duk duniya a wajensa, wata dunkulalliyar kyauta daga rabbil izzati wadda ya fidda ran samunta. Tun ranar da ya rasa Asiya da labubuwar jaririyar da ta haifa ya kuma yi mata alkawarin futa daga rayuwarsu har abada yake jin ya rasa komai a rayuwarsa, tun daga ranar bai sake ganin darajar wani abu wanda ya mallaka ba komai girmansa, yana kallon kansa ne kullum a matsayin mutum mara kowa mara komai mara gaba mara baya wanda bai zo duniya a sa'a ba kuma ba zai bar komai na tarihi ba.
Kullum cikin neman yafiya da yardar Allah yake, yayi nadama sahihiya kuma ya fawwala Allah duk lamuransa, yana fatan wannan jarrawar ta kasance silar samun kusancinsa ga Allah toh sai gashi kuma a lokutan da ya gama sarewa ya fidda rai da komai Allah yayi ikon nasa, ya dawo masa da farin cikin da ya rasa har ma da qarin jikan da ba'a haifa ba. Ya kawo masa 'yarsa a lokacin da yafi bukatar ta fiye da komai. Haqiqa duk wanda ya dogara ga Allah, Allah ya isar masa.
وَمَنْ يَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ فَهُوَ حَسْبُهُ)
And if any one puts his trust in Allah, sufficient is (Allah) for him. (65:3)

A cikin kitchen din gidan Sa'id, wanda Ihman ta lanqayawa Uncle tun shiryawarsu, domin dalilai biyu sahihai wanda ta gamsu da su har ma take sharyi akai, na farko tace bata da uban da ya wuce Abba, so babu wanda zai kwace masa wannan kujerar da wannan sunan a bakinta har abada, na biyu tace Sa'id din is too young katuwar budurwa kamarta ta dinga kiran shi Daddy ko Abba, he looks and act more like an Uncle domin shi gabadaya wata yar qawarshi yake kallonta kuma very friendly yake mu'amala da ita don haka ko a jikinsa, toh shi ko brother ta kira shi ai a guje zai amsa idan har hakan zai janyo masa soyayya da farin cikinta.
Ihman na tsaye a gaban cooker tana juya sauce din da ta sarrafa da kwarewa tunanin Inna yana qara dabaibaye ta, domin wannan kalar girkin signature dinta ne, ita kadai ta sani da wannan recipe din na soyayyen dankalin hausa(sweet potato) da wata irin sauce mai motsa kunnuwa da tsinka yawu.
Sa'id na kan daya daga cikin kujeru ukun da suka zagaye round table a gefen kitchen din yana bata labarin kasar Ghana da yanayin mu'amular su ta yau da kullum, kai idan ka gansu sai ka rantse qanwa ce da yayanta wanda suka shaku da juna.
A cikin yan wadannan kwanakin babu abinda bata sani ba akan shi ba idan aka dauke labarin abinda ya faru tsakaninsa da Inna! A tunanin shi bata sani ba, ita kuma sai bata nuna mi shi ta sanin ba, ko da ya nemi jin wani abu akansu da ita Inna kuwa cewa tayi sai ta tambayi Inna idan tayi izini, ba kuma wai tambayar Innan ce matsala ba, kawai tsintar kanta tayi da jin nauyi da bakin cikin sanar da shi halin da ta taso da Innan a ciki da kuma abubuwan da suka faru da ita bayan a lokacin da ta baro gida bata da burin da ya wuce ta gan shi ido da ido ta bankada mi shi komai ta kuma tabbatar masa da cewa sakon da yayi aike ya dawo gare shi har ma da tukuici. Ta fahimci akwai abubuwa da yawa wanda bakin ciki, fushi da bacin rai da kuma uwa uba rashin fahimta da uzuri suke haddasawa.
Da za'a dinga tsayawa ana daurewa a fahimci juna a gyara al'amura da abubuwa da yawa basu lalace ba, da dangantaka da yawa basu rugurguje ba, da aminci da soyayya da yawa basu rikide sun koma gaba da qiyayya ba.

A plate daya ta hado musu abincin, ta kawo kan table din ta ajiye, ta bude fridge ta ciro drinks ta kawo musu sannan ta zauna suka soma ci tare cikin nutsuwa da annashuwa. Ta dauki dankalin a karo na hudu za ta kai bakinta kenan qarar bell din kofa ta katseta, ta mayar ta ajiye tana side hannunta tace

wacece ni?Where stories live. Discover now