WACECE NI??? BY CUTYFANTASIA PAGE FOUR

347 17 2
                                    

Cikin kuka ta soma magana

"Ya Sadik agola shine dan da mamansa ta futo daga gidan babansa ta taho dashi gidan wani mijin a sakamakon mutuwa ko saki ko? Ya Sadik yau an kirani da Agola da kunnena naji. Kenan ni ba yar Abba bace? Toh wacece ta taho dani gidan nan? I'm pretty sure ba Inna ba ce. domin yanda ta tsaneni banajin ko wuta gidanmu yake ci zata dauko ni ta taho dani, Nasan ba Aunty bace. Please Ya sadik WACECE NI??"

Duk yanda yaso danne feeling din da yake ji ya gaza gabadaya ya kasa controlling emotion dinsa kallonta yake da wata irin ma'ana wadda shi kansa bai san wacce iri bace.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel"

ya maimaita sau uku sannan yaji ya samu karfin zuciya amma duk da haka sai da sautinsa ya janye ya koma can qarshen makoshi.

"Cool down Ihman"

ya fada sannan ya mike ya nufi fridge ya dauko karamar goran ruwan
"swan"
ya mika mata.

A hankali take sha tana jin zuciyarta tana sanyi har ta shanye rabi sannan ya miko mata tissue ta karba.
"Share hawayenki ki goge fuskarki."
Ya fada.
Bayan ta nutsu ya dube ta yace
"Ihman"
ta dago a hankali ta kalle shi. abubuwanda ta hango cikin idanunsa ne suka sanyata saurin kasa da nata idon.

"Ihman idan na gaya miki magana zaki yarda dani? Zaki amince da duk abinda nace miki?kuma zakiyi alkawari ba zaki sake tambayar kowa ba?"

Da sauri ta girgiza kai alamar gamsuwa ta kara da cewa
" Ya Sadik i trust you more than anyone in this life shiyasa na fara zuwa wajenka"

Murmushi yayi yace

"Good nagode da wannan matsayin...abinda nakeso da ke shine kisa a ranki Abba shine mahaifin ki Inna mahaifiyarki ni da Farida yan'uwanki na jini duk duniya babu wanda ya isa ya sauya wannan kinji? Kada ki sake wani tunani bayan wannan duk abinda wani zai ce kada kisa a ran ki balle ki dinga wani tunani na daban kinji Ihman?"

Murmushi tayi tana goge sauran kwallan da suke shirin zubo mata. A sanyaye tace

"Ya Sadik kullum ji nake babu bakin cikin da zai wuce a tabbatar mun Inna ce mahaifiyata saboda yanda take treating dina amma a yau da naji ana kokarin rabani da Abba da kai da Farida sai naji gara ma ace Innan ce ta haifeni."

Tana maganar hawaye na ziraro mata..

" Ya Sadik i can't stand rashinku a tare dani. Zan iya facing kowanne irin challenge idan har kuna gefena"

Kamar zaiyi kuka yake kallon Ihman zuciyarsa babu abinda take sai bugawa cike da so da tausayin yar'uwarsa.

"Stop this Ihman we are all yours forever nothing is gonna change that( ki bari Ihman mu naki ne har abada babu abinda zai chanja haka.)
Now go and rejoice uhmmm. Don't let anyone knows anything kinji?"

Da murmushi a fuskarta ta amsa sannan ta mike cike da qaunar yayan nata ta futa ranta yanai mata sanyi, ta kama handle din kofar ta sake juyowa ta kalle shi, idanun shi suna kanta a lokacin! he looks soo different today!

Tana futa Hamma ya bude kofan toilet ya futo sai lokacin Ya Sadik ya tuna Hamman ma yana toilet.
Ba tare da ya dube shi ba ya je gaban mudubi ya dan shafa mai ya fesa sprays din da ke cike makil akan mudubin Ya Sadik sannan ya ciro wata danyar shedda brown ya saka.

Ba tare da ya kula da taje ko gashin kansa ba ya janyo stool din madubin ya dawo gaban gadon da Ya Sadik yake zaune ya dube shi yace

"Me yake faruwa a gidan nan? Me yarinyar nan take ce maka?"

Ya Sadik cikin sanyi ya soma magana.

"Hamma tunda nake ban taba ganin mu'amala mara dadi irin wadda Inna take yi da Ihman ba. Gaba daya ta tsane ta tsana me tsanani irin wadda zata baka mamaki ko a matsayin matar babanta tazo sai haka. Babu ruwanta da cinta ko shanta ko lafiyarta. Bata kulata bata shiga harkarta. Kwata kwata bata damu da ita ba,Idan suka zauna da Ihman da Farida cikin minti biyar zaka gane bambamci me yawa..

wacece ni?Where stories live. Discover now