WACECE NI???CHAPTER EIGHTEEN BY CUTYFANTASIA

241 11 0
                                    

Direct gidan shi ya tafi da Sadik, ko cikakken parking bai yi ba ya kashe motar ya bude ya futa, sannan ya zagaya ya futo da Sadik wanda gabadaya duniyar ta hargitsewa yake jin shi tsakanin ido biyu da mafarki, babu abinda zuciyar shi take jaddadawa irin
"Ihman ce ta koma haka?"

He just can't believe his eyes! Ihman ce ta lalace ta rame ta jeme ta koma wannan kodaddiyar yarinyar mara sha'awar gani? Me yasa aka boye masa? Abun yana masa ciwo da matukar zafi na boye mi shin da aka yi, bayan yana tunkahon yafi kowa kusanci da ita a cikin gidan.

Zainab ce ta bude musu kofar, kyakykyawar bafulatanar Gombe yar siririya fara sol, tana da far'a sosai da saukin kai sannan kallo daya zaka yi mata ka gane ilmi, wayewa da exposure din rayuwa a tare da ita, duk da haka mace ce wadda ta samu tarbiyya mai kyau.

Cikin far'a ta tarbe su, amma ganin halin da Sadik yake ciki ya sanya jikinta sanyi ta koma da baya ta basu hanya suka wuce home office din Hamma.
Sai da ya zaunar da shi sannan ya koma ya kulle kofar har da key, ya bude karamun fridge din da ke cikin dakin ya dauko mi shi goran fresh milk mai sanyi saboda sanin soyayyar da yake mata.
Babu musu ya karba ya kwalkwale kamar wanda ya shekara da kishirwa, ya sake dauko wani food warmer zai bude Sadik ya daga mi shi hannu yana cewa

"Bani da appetite Hamma ba zan iya cin komai ba"

Bai takura mi shi ba ya mayar ya ajiye sannan ya janyo dan stool din da ke gaban shelve din littattafan shi ya zauna gaban Sadik cikin nutsuwa ya dafa kafadar shi sannan ya soma yi mi shi magana cikin tsananin taushin murya

"Tunda na dawo daga China na fuskanci akwai shakuwa mai karfi da soyayya a tsakanin ka da Ihman fiye da duk sauran yaran gidanmu, har ma nayi mamaki sosai, amma ko sau daya ban taba baiwa kulawar ka da yawan shiga sha'aninta wani meaning na daban ba sai ranar da ta fadi a kitchen tana taya Inna aiki, a ranar komai ya bude mun na hango duka feelings da manufofin ka akan Ihman baro-baro akan kwayar idanunka!
Sadik you are my blood brother wanda nake matukar alfahari da shi, ba sai na gaya maka ba, kasani kullum burina shi ne na hada kanmu gabadaya na samar da zumunci da zaman lafiya mai karfi a tsakanin mu tare da kokarin ganin alakar Inna da Aunty bata shafi tsakaninmu ba.
Sadik inaso ka fahimce ni ka kuma yi wa magana ta kyakykawar fahimta, ka kalleni as dan'uwanku na jini kai da Ihman wanda baya fatan wani tashin hankali ko damuwa ko bakin ciki a tare da ku, wanda zai tsaya da jiki da jini yayi muku duk wani gatan da kuke bukata ya yaye muku damuwar da zai iya yi muku magani ya kuma samar muku da dawwamammen farin ciki.

"Sadik you are a good person with a pure heart wanda ko ba'a dan'uwana kazo ba zan yi farin cikin ka shigo cikin zuri'armu domin mu amfana da juna, baka da wata matsala ko makusa wadda zata janyo a hana ka auren kowacce irin yarinya komai nagartar ta.
But Sadik, I'm sorry! Bazan iya supporting din relationship din ka da Ihman ba, ba zan bari ka idda wannan nufin ba a kanta har abada"

Cikin wani irin speed da kaduwa Sadik ya daga ido ya kalli Hamma, wani madaukakin tashin hankali ya tsirga masa tun daga kwanyarsa har zuwa yatsun kafarsa. Soyayyar da yake yi wa Ihman bata rana daya bace, it wasn't love at first sight, ya fara sonta ne tun kafin ma ya san menene ma'anar so, tun kafin ya san abinda yake ji akanta sunan shi so! A hankali feeling din ya dinga girma yana karuwa yana bunkasa har ya kai mizanin da ya dinga barazanar yin bindiga daga zuciyar sa ya bayyana kansa, shikuma ya dinga kokarin boyewa iya karfinsa domin sanin it was not the right time, domin sanin cewa akwai wasu tashe tashen hankula da tarzoma da kalubale da bayyana soyayyar tashi zata haifar kafin ya samu nasara.
A yanzu da ya kammala karatu yake shirye-shiryen yanda zai yi ya bullowa wannan al'amarin da yanda zai tunkari wanda yake bukatar goyon bayansu akan alakar musamman Hamma, sai kawai yaji maganar auren Ihman da kaddarar da ta fado mata da kuma lalacewar waccan maganar ta mijin da yake jin kamar ya nemo shi yayi ta azabtar da shi har sai ya ramawa Ihman ciwon zuciyar da ya haifar mata.
A daidai lokacin da yake shirye ya bayyana soyayyar da yake wa Ihman ko da kowa zai juya masa baya ciki har da Aunty wadda he knows well ba zata taba basu blessing dinta cikin sauki ba, amma yayi alkawarin he will fight for his love, for their love and he will make her his wife no matter girman kowanne irin tsanani da tashin hankalin da zai fuskanta, toh kawai kuma sai Hamma ya shigo masa da wannan maganar mai kama dafin tsinin mashi ya soka mi shi? Ya ma kuwa san wanene shi? Ya san kuwa yanda yake yi idan yana son abu? Ya kuwa san cewa a cikin rayuwar shi babu giving up babu tsoro babu ja da baya akan dukkan abinda ya tunkara? Ya kuwa san irin zuciyar da Allah ya mallaka masa ba irin wadda take bari ayi defeating mamallakinta bace???Hamma kuwa ya san wanene shi akan abinda yake so?........

wacece ni?Where stories live. Discover now