Da yamma Ihman tana zaune a garden ďin Abba tana karatun al'qurani cikin karyayyen sauti mai matukar ban tausayi, ayoyin suratul Maryam take karantawa zuciyarta na fassara mata kowacce kalma daki daki, kwakwalwarta na tariyo mata tarihin Sayyada Maryam Alaihassalam da irin jarrabawar da Allah yayi mata, da halin ruďani, tsoro da firgicin da ta shiga a lokacin da ta tsinci kanta da cikin Annabi Isa Alaihissalam, amma a qarshe me ya faru? Data dogara da Allah tayi ihmani da shi ta kuma miqa mi shi dukkan lamuranta? Sai gashi sunan ta ya shahara a cinin littafin Allah ba'a duniya kaďai ba, sura sukutum da guda Allah yayi wa laqabi da sunanta!
Which means that all the pain and heartbreak is worth it..............Shi Allah idan yana son ďaga bawansa da wasu darajoji, toh sai ya jarrabe shi da wasu irin jarrabawa masu tsauri, a cikin su ne kuma silar ďaukakar ta shi da duk wani alkhairi yake tabbatuwa.
A kullum sai ta samu lokaci ta karanta wannan surar, wani lokacin ta shiga YouTube ta nemo tafsiran malamai kala kala akan surar da qissar Sayyada Maryam, and she can say it is most soothing and relieving therapy da yafi kowanne tasiri a jikinta. Gabaďaya ta tattare damuwar ta ta mikawa Allah, ta koma gare shi gabaďaya ta zuba idanu kawai tana sauraren ikon shi a kanta tayi ihmani duk abinda ya saukar a gare ta shi ne mafi alkhairi domin Shi da ya halicce ta yafi kowa jin qai da qaunar ta.
Shi yake da iko akan kowa da komai don haka komai lalacewar lamari, cikin qudurar shi da hikimar shi zai gyara sai idan bai so ba.
Kun- yake cewa
Fa-yakun
Sai komai yayi fallen into the most perfect place ba tare da tsumi, taimako ko dabarar wani ko wata ba.Jin muryar Sadik tayi yana bin ayar da take kantawa ta ukun qarshen surar
"اِنَّ الَّذِيْنَ اٰمَنُوْا وَعَمِلُوا الصّٰلِحٰتِ سَيَجْعَلُ لَهُمُ الرَّحْمٰنُ وُدًّا
innallażīna āmanụ wa 'amiluṣ-ṣāliḥāti sayaj'alu lahumur-raḥmānu wuddā"Tare suka qarasa sannan suka yi addu'a suka shafa suna jefawa juna murmushi.
"You are my role model Ihman"
Ďan waro idanu tayi sannan tace
"Rufa mun asiri Ya Sadik......ban kai nan ba"
"Har ma kin wuce kin shallake.. let me show you something"
Wayar sa ya ciro daga gaban aljihun farar shaddar jikinsa, yayi yan tabe tabe sannan ya miko mata...
"A tour of our apartment in Russia"
Ta karba cikin zumuďi ta soma kallon vedio ďin ďan karamun gidan da zasu zauna a garin Moscow ďin qasar Russia wanda yayi mugun tafiya da hankalinta, tun daga kan kama hayar wannan gida da gyaran sa, da kuďin visa da ticket da kuďin makarantar Farida daga aljihun Hamma ne, aljihun nasa kuma ya girgiza, girgizuwar da bai taba yi ba, domin sai da ta kai ya ďaga manyan shagunan sa da ya siya kwanaki a cikin kasuwar Kwari ya siyar ba da sanin kowa ba. Shi dai fatansa kawai Inna da Ilham su zauna cikin aminci da farin ciki kuma zaman nasu ya zama masalaha da alkhairi.....
Sadik kawai kallon Ihman yake yi with soo much love and affection, murmushi da farin cikin da yake kan fuskarta wanda ya ďau lokaci bai gani bane ya qayatar da shi, yake kuma jin dama yana da yanda zai yi ya dawwamar mata da shi akan fuskarta har abada.
Daga can kofar shigowa garden ďin Abba ne a tsaye ya harďe hannaye yana kallon su, sha'awa, tausayi da farin ciki sun lullubeshi,zuciyar shi na ayyana mi shi irin alfanun da ke cikin tarayyar su, watakila faruwar wasu abubuwan ma suna da nasaba da wannan alakar da zata qullu a tsakanin Ihman da Sadik wadda ba don faruwar hakan ba da babu yiwuwarta ko kusa ko alama.
Ba shakka Sadik ya isa namijin da hankalin shi zai kwanta idan ya ba shi auren Ihman, ba don ya kasance ďan da ya haifa ba, sai don irin tarin soyayyar da yake hangowa ta Ihman a idanun Sadik da ayyukan sa wanda ya tabbatar soyayya ce ta gaskiya mara algus.
Ta fannin Ihman ďin kuma har mamakin yanda tafi sakewa da yin walwala tare da Sadik ďin fiye da kowa yake ciki kuwa har da Farida wadda take kusan twin a gareta.
Amma kuma da ya tuna badaqalar da take cikin wannan haďin da qalubalen da dukkansu zasu fuskanta sai yaji zuciyar shi tayi nauyi, a ajiye drama da rashin arzikin Anty a gefe, ta yaya zai fuskanci Ihman da sauran ýaýansa ya warware musu sirrin ainihin alaqar sa da ita ba tare da ya ji musu rauni mai girma a cikin zukatan su ba?.......
BINABASA MO ANG
wacece ni?
General FictionWacece ni labari ne akan matashiyar da ta taso cikin wata irin rayuwa mai ďaure kai da jan hankali. Ba abun mamaki bane idan kishiyar mahaifiyar mutum ta tsane shi amma mahaifiyar kanta ta nunawa ďanta tsantsar tsana da tsangwama da kyara abun ban m...