WACECE NI??? CHAPTER'S CHAPTER TWENTY-SIX BY CUTYFANTASIA

203 16 6
                                    

A nutse suka shiga cikin falon wanda yake ďauke da mutane shida, tsohon kirkin wanda ake wa laqabi da Alhaji Muhammad Yusuf Maigoro bafulatanin garin Yobe ne wanda kasuwanci ya kai garin Kano tare da iyalinsa Hajiya Gaje, Alhaji Muhammad ba shi da sana'ar da ta wuce fatauci tsakanin Kano da Shagamu da kasar Ghana, Daga qauyukan Kano yake siyan Shanu ya saka a jirgin ruwa ya shiga mota ya bisu kasar Ghana ya siyar, sai kuma yayo lodin goro wanda hausawa suke wa laqabi da ďan ankara da kuma Kante (wani zani da dankwali na saki da mata ke sakawa) ya kawo garin Kano da sauran garuruwan da suke bukata ya siyar.
Cikin wannan kasuwancin ya samu duk wata shahara da arziki da rufin asirin da ya samu, wannan kasuwancin ne ya mayar da shi kasurgumin mai hannu da shuni a zamanin sa babu inda sunansa bai karaďe ba a birnin Kano, Shagamu da kuma yankin da yake kasuwanci a kasar Ghana.

Allah ya azurta Alhaji Muhammad da ýaýa mata guda shida, namiji ya dinga sa ido yana nema ruwa a jallo Allah bai nufe shi da samu ba, a garin hakane kuma abokansa suka ba shi shawara da ya qara aure ko zai dace, shine ya auri Wata barerabiyar da suka haďu a Shagamu, an yi ďauki ba daďi ba kaďan ba kafin iyayensa da matar sa Hajiya Gaje su amince da wannan zabin, aka yi aure amma matar sai ta tare a kasar Ghana bai haďa su gari ďaya ba don gudun fitina, cikin shekara ďaya Allah ya bata haihuwa, sai dai a maimakon namijin da ake sa rai itama sai ta sillibo bayerabiyar jaririyarta mai kama sak da ita mace.
Jikin Alhaji yayi sanyi sosai, har ma ya dinga danasanin auren da kuma wulkancin da yayi wa uwargidansa a kan shi, shekara ta sake zagayowa amarya Manfusat ta sake haihuwar ýa mace wacce a dalilin haihuwar ne kuma Allah ya karbi ranta. Bayan rasuwar Manfusat iyayenta suka nemi alfarmar rikon ýaýan gida biyu shikuma yace ba zai bayar ba babu kunya kuma ya ďebo su ya kawo wajen Hajiya Gaje ya kalallame ta da magiya ta karbe su ta haďa da ýaýanta.
Komai tare take musu bata taba nuna musu bambamci ko ware ba, duk da kallo ďaya zaka yi musu ka gane cewa ba ýaýan ta bane, su mahaifiyarsu suka yo sak! Bakake masu gajeran hanci da manyan idanu, ita kuma ýayanta fulani ne farare tas masu hanci gadon uwa da uba.
Ýaýan Manfusat masu hankali da biyayya ne, kuma basu taba baiwa Hajiya Gaje matsala ba, rayuwa suke cikin gidan mai daďi musamman ma da shekarar mutuwar Manfusat na zagayowa Allah ya bata haihuwar ďa namijin da suke mugun buri ko ace Alhaji yake buri. Murnar da suka yi ba zata misaltu ba. Tun haihuwar Sa'id aka gane Alhaji bashi da abun so irin shi, bashi da abun tattali da tarairaya sai Sa'id, wata iriyar makauniyar soyayya ya nuna mata da gata na ban mamaki.
Tun Hajiya Gaje na mi shi nasiha akan kada yaron ya lalace har ta gaji ta hakura.
Haka ya taso tsakanin yayunsa mata da iyayen sa ďan lele, duk da bayan shi an haifi maza guda biyu Yusuf(Baba) da Aminullahi, Sam ba zaka haďa soyayyar da yake wa Sa'ida da ta kowa a cikin ýaýansa ba. A Kano suka soma karatu, kafin likkafa taci gaba, yayi mahaukacin gida a kasar Ghana ya tattara ya koma can, saboda soyayyar sa da kasar Ghana sannan hada hadar kasuwacin sa a can ta rinjayi ta Kano, daman garin Kanon ba mahaifarsa bace bako ne.
Sai ya zamana ragamar saro shanu daga kauyukan Kano da tura su Ghana ya bar su a hannun aminin shi kuma abokin kasuwancin shi Alhaji Alhassan ďan asalin karamar hukumar Garo ta jihar Kano, aminci da gaskiyar sa ya sanya alakar su tayi matukar karfi duk da cewa sun raba kasa kowa yana can tare da iyalinsa yana rayuwa.

Sa'id ya taso wani irin yaro mai taurin kai da kafiya wanda sangarta da gata suka kara tunzurawa yake duk abinda ya ga dama. A fannin karatu ne kawai yake abun arziki, domin komai shegantakar sa kwaro ne shi a fannin boko da Arabi don haka Alhaji bai taba ganin laifinsa ba.
Ýaýan Alhaji mata da mazan sai da suka yi karatun boko suka koshi sannan ya soma aurar da su, cikin ikon Allah kuma duk a kasar Ghanan suke samun mazajen idan aka cire Khadija babbar ýarsa da Manfusat(mai sunan mamanta) da suka yi aure a jihar Kano.

Sa'id ya koma garin Kano domin yayi degree ta farko a jami'ar Bayero a hannun Khadija da mijinta wanda yake ďan'uwa ga Alhajin, amma a shekarar sa ta farko a gidan ya aikata ta'asar da ta janyo masa duk wani kunci, masifa da bala'in da ya samu kansa a ciki.
Wannan ne dalilin dakilewar farin ciki da kwanciyar hankalin wannan family na lokaci mai tsayi, ya kuma bar musu wani katoton mikin da har yau bai warke a cikin zukatansu ba.

wacece ni?Donde viven las historias. Descúbrelo ahora