WACECE NI??? BY CUTYFANTASIA PAGE SIX

284 16 3
                                    

Cikin girmamawa abokan Kamal suka gaishe da Hamma sannan Ya Wasila ta soma touring din shi cikin gidan kafin su dawo falon da Ihman take su zauna.
A nutse ta tashi za ta basu waje Hamma yace
"ina zakije Ihman?"

Murmushi Ihman tayi tace
"kitchen zanje na kawo maka ruwa"
cewa yayi
"nace ina jin kishirwa ne? Ita wadda nazo gidan na ta itace zata bani ruwa bake ba"

murmshi Ihman tayi tace
"Hamma ai hutar da ita zanyi tunda nazo"

tana fadin haka ta wuce da sauri ta futa.
Murmushi Wasila tayi tace
"hmm Ihman kenan! Hamma babu wani ruwa fa! Kawai so take ta bamu waje"
ajiyar zuciya ya sauke yace
"Wasila menene matsalar Inna da wannan yarinyar? Abinda idona yake gani bayan dawowata na Gaza gane kansa! Wacce irin mu'amala ce wannan Inna take yi da Ihman?"

Tuni fuskar Wasila ta koma kalar tausayi da jimami.
Babu bata lokaci ta warware masa duk abubuwan da suke faruwa a tsakanin Inna da Ihman da irin kokarin da kowannen su yayi ya ga ya gyara mu'amular su amma abun yaci tura.

Ran Hamma Quraish yayi masifar baci da wannan bayanai da yaji masu ruďa kai da bakanta zuciya.
Wannan ya sanya basu wani yi hirar kirki a gidan Wasilan ba ya tashi yace tafiya zasu yi.
Har bakin mota Wasila da mijinta suka rako su sai da suka bar gate ďin sannan suka koma abokan Kamal suna cikin parlour a zaune, Ihman ta kasa jurewa sai da ta saci kallon ciki, caraf kuwa suka hada ido da wanda take neman gani, kunya ta kama ta, tayi maza ta juya ba tare da ta kula da hannun da ya daga mata ba alamar bye bye.

Tunda ta shiga motar ta gane ran Hamman a bace yake don haka ta nutsu ta kama kanta.

Basu wani yi nisa ba yayi parking a gefen hanya yana kallon ta sannan ya kira sunan ta a nutse.

"Kiban aron hankalin ki magana zamu yi sosai kuma idan kika gaya mun abinda ba gaskiya ba don ki kare kanki Allah yana kallon ki"

Sai da gabanta ya faďi domin taji a jikinta maganar Inna zai yi mata kuma ta san kowaye shi a wajen Inna da yanda suke ji da juna. Babu wanda zai fahimci cewa wai shi ďin ďan fari ne saboda wani irin bond da suke sharing mai wuyar fassarawa. Inna tana da kara akan dukkan ýaýanta amma bata yarda wannan bahaguwar al'ada ta fulani akan ýayan fari tayi tasiri a kanta ba. Tana jan ýaýanta a jiki ta san matsalar su, tayi hira da su da wasa da dariya kamar sakonnin ta idan dai aka ďauke matsalar da take tsakanin ta da Ihman Inna uwar da kowanne ďa zaiyi alfahari samun ta ne a matsayin uwa.

"Ihman meye tsakanin ki da Inna?"

Cikin tsoro da fargaba fa ďago tana kallon shi!

"Ki daina kallona kamar wani dodo ki bani amsa tsakanin ki da Allah!"

Kan kace kobo idanunta sun soma zub da hawaye. Bayan Sadik bata taba maganar Inna da wani a rayuwar ta ba. Ko shi Sadik ďin ma sai idan tana neman wani taimako ne take shigo da shi cikin sabgar ta amma ba kai tsaye take kai karar Inna wajen shi ba.

"I don't like crying you know(Ni bana son kuka kin sani) kuma ba kuka nace kiyi mun ba bayani zaki yi mun iya fahimtar ki"

Aikuwa bai Ankara ba ta barke da kukan mai tsuma zuciya irin wanda mutum bai isa ya tsayar da shi ba domin daga can cikin zuciya yake samun umarni. Irin wannan kukan ne wanda mutum yake tarawa yana cinyewa tsayin lokaci yana kaf kaf da shi kada ya taho, toh a duk lokacin da ya samu damar tahowa kuwa babu wanda ya isa ya tsayar da shi. Fahimtar hakan da Quraish yayi ne ya sanya shi yin shiru yana sauraren ta zuciyar shi na karyewa domin shi mutum ne mai tsananin damuwa kan lamarin ýan'uwan sa da mahaifansa, idan akwai wani weakness ďin sa bai wuce kuka ba, bai son ganin ko da taruwar kwalla a idanun mutum balle jininsa makusancin sa balle ya gane kukan bana shagwaba ko sa kai bane, kuka ne na damuwa da bacin rai. Toh nan da nan hankalin sa zai tashi ya rasa inda zai sanya kansa sai ya nemo maganin wannan damuwa ya kawo wa mutum zai samu sukuni. That aside, Ihman is his favourite sister( wannan a gefe, Ihman ita ce yafi so duk cikin kannen sa) saboda wasu dalilai da kuma kasancewar ta makaranciyar alkur'ani! Quraish bai haďa karatun alqurani da komai ba saboda haka duk wanda yake da baiwa cikin karatun alqurani toh ya samu zuciyar shi ya gama. Na biyu kuma ita ce wadda ba'a taba kawo mi shi karar ta ba, yana son mutum mara kiriniya da fitina. Ya sha saka Sadik ya zane Farida akan kawaye da shirmen su amma ita Ihman bayan Farida ko a family bata da kawa balle wasu shirmammun da za'a raba ta da su. Sannan a zuwan sa ya fahimci babu wadda Inna take mora a gidan kamar Ihman, kuma duk irin abubuwan da take yi Mata yarinyar ta shanye fa haďiye tana yi mata biyayya. Wannan yake kara haďuwa yana kulle masa kai tamau akan dalilin da ya sanya Inna tsanar Ihman.

wacece ni?Where stories live. Discover now