WACECE NI??? BY CUTYFANTASIA PAGE EIGHT

260 20 4
                                    

A sanyaye ta shiga dakin ta, zuciyar ta na suya kamar zata kone, ganin ta da kayan Ihman ta yunkura ta zauna dakyar, ba tare da ko kalma ta shiga tsakanin su ba Inna ta ciyar da Ihman abincin da hannunta, Ihman na karba tana kwaranyar hawaye, bata taba samun irin wannan kulawar daga Inna ba tun daga ranar da zata iya tunawa, wannan shine karo na farko da suka zauna da kusanci irin haka su biyu a waje daya, duk da ta san cewa Innan tana yi ne out her will, bai hana ta tsinci kanta cikin wani yanayi na relief ba!

Hamma da ke bakin kofa yana kallon su yana hawayen zuci tausayin Ihman na sauka a ran shi kamar yanda ruwan sama yake sauka akan kasa, ji yake yi kamar ya tattaro duka kulawa da gatan duniya ya bata, amma ya san it will never be enough, shi da, kulawar uwar shi tafi kulawar dukkan mutanen duniya muhimmanci da jindadi a gare shi, no one can ever take a mother's place musamman idan tana raye!

A sanyaye ya karaso cikin dakin, ya karbi tray din daga hannun Inna a lokacin da take kokarin daukewa, ya sauka da shi kitchen da kan sa sannan ya dawo, kamar wani abu bai faru ba ya soma yi mata magana da irin sigar da ya saba a kowanne lokaci, duk da cewa akwai damuwa a tare shi kamar ita Innan.

"Inna ina son nayi magana da ke tun da nazo ban samu dama ba!"

Tayi tunanin akan Ihman ne, don haka ta sake daure fuska tamau tana tsare shi da idanunta masu girma irin na shi!
murmushin cikin zuciya yayi yana cewa

"Ai Inna ba ta nan zan bullo miki ba akan Ihman, i have a better way and plan"

A zahiri kuwa sai yaa tausasa murya yace

"Inna kwai yarinyar da muka hadu da ita a China, tana karatu a jami'ar da nake wannan shekarar zata kammala masters din ta. Sunan ta Zainab kuma tana da hankali da tarbiyya Inna!
Kanwar Ahmad ce abokina mahaifinsu kanin san Turakin Dukku ne uwa daya uba daya, naje sau biyu muna ganawa da shi a karshen zuwan da nayi ne yace mun idan da gaske nake na turo daga gida a tsaida magana domin tana kammala karatun masters dinta zasu aurar da ita!"

kamar yanda Quraish yayi hasashe sakon na shi ya isa irin yanda yake bukata, domin cikin dakika uku mood din Inna ya changa completely zuwa wani irin farin ciki da murmushi kai ba zaka ce ita ce ta dazu ba, A take duka damuwar da take ciki ra yaye himilin murna da farin ciki suna maye gurbin su.
abinda ya karairayawa Ihman zuciya kenan, taji wani irin tukuki a cikin zuciyarta irin wanda bata taba ji ba a duk lokutan da Inna take fifita yan'uwanta a kanta. Ta lumshe idanu yana maimaita sunan Allah "Assalam" da ya saukar mata da salama da sanyi a zuciyarta ya bata ikon cinye wannan jarrabawa.
Da yake maganin akwai sedatives sai bacci ya kwashe ta kafin su Inna su karasa maganar su.

A dakin Inna Ihman tayi wannan jinya karkashin kulawar Inna, amma ko sau daya wata kalma ta sannu ko ya jiki bata hada su ba, iyakacin su gaisuwa, duk hidimar Ihman Inna ce take yi kamar bebiya kamar gunki ita kuma tana bin direction kamar robot! A wannan lokacin sai Quraish ya mayar da dakin Inna dandanlin zaman sa, sau da yawa shi yake karbar Innan idan za ta baiwa Ihman abinci ko magani. Sadik yana shigowa sai biyu a rana, amma babu walwala a tare da shi, a ranar da ta cika sati daya da tsautsayin ne kuma babu zato aka gan shi da tikiti wai zai koma makaranta bayan ko rabin hutun na shi bai ci ba.
Toh idan yana wannan jujun ko Hamma Quraish da Abba zuba masa idanu suke yi domin baya tankwasuwa, don haka suna ji suna gani yayi sallama ya tafi cikin rashin walwala. ita Ihman lokacin tana bacci, sai farkawa tayi da dogon text a wayar ta wanda ya dinga raba mata hankali akan abinda Sadik din yake nufi da ita! kalaman sunyi nauyi su tsaya a mizanin yan'uwantaka kadai, kanta ya sake nauyi!

cikin kwanaki shabiyu ta samu sauki sosai, jikinta yayi kyau, sai dai har lokacin mai gyaran bai bata damar taka kafar ba, yace kashin bai gama haduwa yanda suke so ba! a wannan daren da suka dawo daga wajen mai gyaran ne ta farka cikin matsanancin jin fitsari, misalin karfe uku da rabi na dare, har zata motsa shashshekar kukan Inna ya dakatar da ita, she knows that Inna mai raya dare ce, mai ibada amma a wannan rana ta jiyo wa kanta wani al'amari mai girma wanda bata taba hasashen shi daga wajen Inna ba idan tayi la'akari da kasancewar Inna mace mai hakuri da yafiya da sanyi. ta bude idanunta a hankali ta zuba su akan Inna da ke can tsakiyar dakin akan dadduma tana zaune da hannayen ta duka a sama take jero addu'o'in da suka toshewa Ihman kwakwalwa da tunani duk da ba daga farko ta tsinkayi addu'ar ba tsakiyar taji

wacece ni?Donde viven las historias. Descúbrelo ahora