WACECE NI??? CHAPTER NINETEEN BY CUTYFANTASIA

194 13 0
                                    

Kafin tafiya Abuja sai da aka sha rikici da Aunty akan Sadik ba zai raka su ba, wai saboda saukar sa kasar kenan ko hutawa bai yi ba balle su kebe da shi su samu lokaci tare. Abba ya kalle ta cikin bacin rai yace

"Idan ke kike da iko da shi gashi nan ki saka shi a daki ki kulle ki hana shi tafiya! Sakarya wadda bata san ta girma ba"

Ta sake fashewa da kuka ta mike ta shige dakinta tana jin tsanar Inna da zuri'arta tana ninkuwa a cikin zuciyarta, cikin wannan halin Sadik yayi sallama cikin dakin nata, sautin kukan ta ne ya bashi izinin shiga ba jin amsar ta ba. A sanyaye ya nemi bakin gadon ya zauna wani sashe na zuciyar sa yana jin tausayin ta, ya san she was never Abba's favourite amma ba komai ya janyo mata rashin jituwa tsakaninta da Abban ba illa bakin halinta, tunda ba yanda za'ai mutum ya auri mace ya ajiye ta a gidansa yace baya so, toh ita Aunty bata son zaman lafiya, bata son kwanciyar hankali kowanne lokaci negative kwakwalwarta take mata viewing abu saboda haka ne har yau ta kasa samun fadar da take so a wajen Abba.

"Aunty meye yayi zafi? Ya zaki zauna a daki kina irin wannan kukan ko don gudun yara su shigo su gan ki? Aunty don Allah ki saukakawa kan ki rayuwa a gidan nan ki ajiye wadannan abubuwan ki rungumi mutanen da Allah ya hada ki zama da su, idan kika saka salama da kwanciyar hankali, toh tabbas zaki gane cewa basu da matsala babu wanda........."

Cikin karaji da kufula tace

"Shut up Sadik! Bana son jin komai daga bakin ka! Ba gara Babanku bama duk wuya mijin wata na aura watan kuma matsafiya,makira,mayya. Kai fa? Dan cikina ya juya mun baya? Dan cikina ne zai bar ni ya koma bayan makiyana wanda kullum fatan su shine su ga na tozarta? Gaya mun uwar me Asiya da yayanta suka tsinana mana da kake bin su kana rawar kafa akan su?meye hadin ka da Waccan tsintacciyar shegiyar agolar da mahaifin ku ya fifita fiye da kowa a gidan nan? Idan sauran kace kun hada uba da su ita wacce uwar kuka hada? Yar Asiya ce ba yar Babanku ba don haka babu wata alaka a tsakanin ka da ita. Kana kallon yanda ya banzatar da rayuwar Asma'u, ya tsaya tsayin daka akan Wasila tayi karatu ta auri mai kudi amma ni saboda an tsane ni an bar mun yar kamar ni kadai na haifeta, zancen aurenta yaki ci yaki cinyewa makarantar har yau ta kasa gamawa saboda tsabar makirci da tsafin wannan tsinanniyar matar......."

Cikin wani irin yanayi Sadik ya dago juyayyun idanun shi wanda suka rine da bacin rai yana kallon Aunty zuciyar shi tana wani bugawa kamar zata ballo daga cikin kirjin shi. Cikin sauri ya mike ya bar dakin yana hadawa da gudu domin kada fushin sa ya fashe a gaban Aunty, shi kansa tsoron kansa yake yi idan aka bata masa rai dalilin da yasa bai cika shiga cikin al'amuran mutane ba kenan, shi bai iya daukar raini ko wulakanci ba, baya son wasa baya son A daga masa hankali. A hanya suka ci karo da Abba da Hamma sun futo daga sasan Abban suna tattaunawa, cikin mamaki suke kallon Sadik Hamma yayi maza ya rike shi yana kallon yanayin  da ya koma kamar zakin da aka shiga cikin kejin sa aka kwashewa ýaýa.

Ba karamun danbarwa sukai ba kafin ya samu ya iya rike shi ya zaunar da shi a cikin falon, Abba ya tafi kitchen da sauri ya dauko ruwa suka dinga shafa masa a fuskar shi sannan aka ba shi yasha. Sun yi mintina goma sha biyar a kan shi kafin ya dawo hayyacin shi sannan Hamma ya raka shi daki ba tare da sun tuhume shi komai ba, sun tabbatar Aunty ce, ita din kuma mahaifiyar shi ce don haka suka bar maganar anan amma ba karamun fushi Abba ya dauka da Aunty ba. Gabadaya ji yake gidan ya fuce masa a rai, kowacce ya kalla cikin matan na shi ran shi baci yake yi don haka ya soma tunanin shirya wani balaguro yaje ya huta ko ya samu nutsuwa amma idan ya tuna yaransa masu tasowa a gidan sai yaji ba zai iya trusting din su a hannun iyayen nasu mata babu sa ido ko kulawar shi ba.

Sun je Abuja sun yi submitting duka abubuwan da ake bukata kafin ayi musu approving visa, sunyi interview cikin nasara sun kammala, sannan suka wuce garin Kano suka yi sallama da su Hajiya daga nan suka koma Gombe.
Dawowar Sadik tayi matukar farfadowa da Ihman walwalar ta, bond din su ya baiwa kowa mamaki da sha'awa, kuma kowa ya yarda babu wanda ya san Ihman in and out kamar Sadik kuma jininsu yayi matukar zuwa daya.
Babu wanda Ihman ta iya bude baki tayi maganar abinda ya faru da ita without feeling ashamed sai Sadik, gaya mi shin da tayi kuma ya sake bata nustuwa da kwanciyar hankali domin ta amayar da abubuwan da suke matukar damunta a cikin kirjinta ga wanda take da tabbaci da yakinin ba zai yi mata wata fassara ko kallo irin wanda sauran mutane suke yi mata ba.
Kwarin guiwa yake bata a koda yaushe yana kuma jaddada mata cewar abinda ya same ta ba tawaya ko nakasa bace, ba zai kuma hanata cimma komai na rayuwarta ba. Yayi matukar debe mata kewar da take ciki, idan har yana gida toh tabbas zaka same su tare cikin garden din Abba da laptop din shi a gaban shi yana nuna mata abubuwan da zasu dauke hankalinta, musamman gine ginen zamani na kasashen duniya masu kayatarwa da ban mamaki.
Wani lokacin kuma su zauna suna tsara irin yanda yake son ya gina gidan shi, tana fadin abubuwan da za'ayi shi kuma yana zanawa, sun futar da taswirar gidaje sun yi uku a wannan tsukin sannan suka dawo duba wanda yafi kyau a ciki. Da kuma yanayin decor din da ya kamata ayi masa, da colours din da za'ayi amfani wajen furnishing gidan.
Shi Sadik bilhaqqi da gaske yake daukar komai yana hango lokacin da zai mallaki Ihman a matsayin matar da zata zauna cikin wannan gidan, don haka ne yake bin tsarin ta da choice din ta akan komai domin yana son gidan ya kasance wata duniya ta walwala da farin ciki a gare ta.
Aunty tana Agadez tun ranar da su Ihman suka dawo daga Abuja ta gayawa Abba zata je garin su wai Mamansu bata da lafiya kuma itama tana kewar gida. Matar da ta kan rufe shekara bata je gidan ba wani lokacin ma ko wani abun ya faru sai ta shamuke tace tsoron hanya take ko bata jin dadi.
"Allah ya kiyaye"
Kawai Abba yace mata, a hakan kuma dai Hamman ne ya tura mata kudin jirgi lokacin da yaji ance a mota zata tafi har da extra kudin tsaraba amma duk da haka Aunty bata gani ba, sai bayan tafiyarta ne Zainab take gayawa Inna taji tana waya da Yayarta Zaituna da ke Abuja wai za'aje a shiryowa Inna.
A darare Zainab take fadin maganar saboda warning din da Inna take musu akan kawo mata gulma, but this time ita kanta Innan hankalinta bai kwanta da tafiyar Aunty ba don haka ta dubi Zainab tace

"Zainab kiji tsoron Allah ki sani duk wanda yayi qarya wutar jahannama tana nan tana jiran sa. Kar kiga bama shiri da Aunty idan kika yi mata sharri sai Allah ya saka mata"

Girgiza kai kawai Zainab take yi cikin tabbatarwa

"Wallahi Inna naji tana waya da Auntyn su Adda Asma kuma naji duk abinda take cewa"

Cikin nutsuwa Inna tace

"Toh gaya mun ina jin ki"

A ďarare Zainab ta soma yi wa Inna bayani

"Cewa tayi wai wannan ta fadi sunan ki na gaskiya wai da ke da Adda Ihman tana son abinda zaku gwammace mutuwa da rayuwa kuma sai Abba ya kore ku da kansa a gidan nan bayan ya wulakanta ku.........
Da yawa maganar wasu na manta wasu kuma ba da hausa suke yi ba amma tace dawowarta daga Niger wai ba alkhairi bane kuma wai sai ta saki kuka mai yawa"

Cikin wani irin yanayi Inna ta dagawa Zainab hannu sannan tace

"Naji ya isa haka Zainab! Ina so wannan maganar ta tsaya tsakanina da ke kadai kin ji? Ko Farida ban yarda ki gayawa ba na san itace sarkin tuhumar ki akan jin gulma! Allah yafi su kome zata je tayi taje ni da Allah na dogara kuma duk wanda ya dogara da Allah ya isar masa"

Sai da Inna ta tabbatar tayi wa Zainab kyakykawan warning sannan ta sallameta ta futa. A take Inna ta dau waya ta kira Hajiyar Kano ta sanar mata da komai cikin damuwa.

"Ki bar ta Asiya da tulin zunubi da wahalar da za ta daukarwa kanta. Ba alfahari nake ba amma mai ganin bayana sai ya shirya wallahi! Bana boka bana Malam amma ina da Allah ina da addu'a don haka mun fi karfin kowa da komai da duk wani abun cutarwa. Ke dai kici gaba da addu'o'in da kika saba, kowanne yaro cikin yaranki ki tabbatar yana azkar safe da yamma babu fashi ki kuma dinga jadadda musu muhimmancinsa. Ki yawaita sadaka da ambaton Allah, babu abinda zai faru sai alkhairi. Yanzun nan zan bugawa Alaramma asa almajirai su fara sauka, kullum za'a sauke al'qurani tun daga gobe har ranar da zata dawo mu zuba mu da ita kowanne irin tsafi zasu yi suje suyi muna karkashin kariyar Allah."

Ta dade tana yi wa Inna nasiha har ta tabbatar ta samar mata nutsuwa sannan suka yi sallama, itama Inna a nata bangaren ta saka Malamai addu'o'i masu inganci wanda suka futo daga al'qurani da hadisan Manzon Allah saw zalla, da yakini da tasdiki da ihmanin cewa zasu zamar mata kariya kuma katanga daga dukkan wani sharri da bala'i da musiba komai girmansu. Tana kammalawa taji a ranta ta wuce wajen, ta gama da wannan maganar sai dai kuma wata domin wani mahaluki bai taba dogara da Allah da fadinsa ya wulakanta ba.
Akan wannan tsarin suka taso wajen mahaifiyarsu, da wannan tarbiyyar ta raine su and so far wani mutum komai sharrin sa, wani abokin gaba komai karfinsa bai taba samun galaba akan su ba. Sun yarda da Allah sun kadaita shi shi kaďai kuma sun sallama masa akan dukkan sha'anin su.

Cikin nasara Visa ta futo, komai ya zama ready, Sadik ya sake dagewa da shi za'ayi tafiyar Abba ya goya masa baya, Aunty bata sake ce masa ci kanka ba, tsakanin su kawai gaisuwa ne da Sadik, Aunty Zaituna tace ta bar dan banza, nan da kwanaki kadan idan Aunty ta zaunar da shi ko akan wuta ne ba zai iya tashi ba sai da umarninta.
Ta bangaren Sadik din baya jin dadin yanda mu'amalar su da Aunty take tafiya amma ba yanda zai yi, fatan shi a kullum Allah ya ganar da ita da gaskiya.

wacece ni?Donde viven las historias. Descúbrelo ahora