WACECE NI??? CHAPTER TWENTY-FIVE BY CUTYFANTASIA

174 13 2
                                    

Da sassafiyar laraba Ihman tayi wanka ta shirya cikin sabuwar Armani abaya baka wuluk, ta nannade fuskarta cikin mayafin rigar wanda ya fiddo da zallar hasken fatarta da kwarjini da cikakken kyawunta na fulani kai baka so ka daina kallonta ba. A sanyaye take komai, zuciyar ta babu abinda take riya mata sai wacce irin tarba zata samu daga ahalin da bata taba shiga ciki ba? Da wacce irin fuska zasu karbe ta kuma wanne irin gurbi zasu bata?
Abun mamaki Sharifat da mijinta sai wani ďoki suke yi da murna, bama su kaďai ba ta lura ita kanta Iya Raheem da suka yi magana a waya walwalarta ta qaru.

Karfe biyun rana jirgin ASKY AIRLINES ya lula da su sararin samaniya, bakin Ihman ďauke da addu'a yayinda qirjinta yake ta faman bugawa kamar zai Faso daga kirjinta. Wani irin tsoro ya mamaye ta lokacin da ta tabbatar tayi nisa da kasar haihuwarta zuwa wata kasar da kafarta bata taba takawa ba da mutumin da ba muharraminta ba zuwa dangin da bata gani ba kuma bata da masaniya akan yanayin da zasu karbeta.
Wasu irin hawaye suka soma zubo mata tana sharewa cikin dabara domin Abdurraheem na gefenta ita kuma tana jikin window. Ga mamakinta sai ta tsinci muryar sa yana cewa

"Calm down my sister! You a are safe insha Allah, kiyi addu'a zaki samu nutsuwa! mu ba masu cutarwa bane a gare ki."

Da taimakon ýar nasihar sa kukan ya tsagaita mata, nervousness ďin da take ji ya ragu har ma ta samu ta kurbi ruwan da aka kawo musu. Daga wannan ta sake kudundunewa tana karanta ayoyin karshen suratul baqara cikin zuciyarta idanun ta a lumshe tana tunanin yanda akai ta futo daga gida ta shigo jirgi tazo Abuja da haďuwarta da Iya Raheem da taimakon ta a gare ta. Toh shin waďannan mutanen wanne iri ne? Shin taimakon suke don Allah ko kuwa akwai wata manufar da suke da ita a kanta? Idan babu kowacce irin manufa bayan taimakon mai ya hana Abdurraheem karbar kuďin tafiyarta tun daga kan visa har zuwa tikiti? Me ya saka shi barin aikin sa ya rako ta? Ko Sharifat yayi wa haka kuwa ba za'a tafa masa ba? Balle ita da babu dangin iya ba na baba? Me suke nufi da wannan taimakon da suke ikirari?
Idan ta nutsu cikin waďannan tambayoyin sai taji hankalinta yayi mummunan tashi, tana cikin wannan wasi wasin kuma sai wani bangaren zuciyarta ya tuna mata irin ibadar su da kyakykawar ďabi'ar su wadda ta karanta a kwanakin da tayi da su, ga uwa uba addu'a da kiran Allah a kowanne sha'ani nasu. Anya kuwa macuci haka yake?

To say Ihman is confused is an understatement! Kawai dai gata nan ne a zaune amma gabaďaya bata cikin hayyacinta, sake sake da tunane tunane ne suke gudana cikin zuciya da kwakwalwar ta kamar zata zauce a cikin jirgin nan har Allah ya sauke su a garin Accra da ke kasar Ghana lafiya cikin tafiyar awanni biyu ba kaďan.

Kamar ya san garin,kamar ba farkon zuwan sa kenan ba haka ya dinga yi musu komai har suka futo daga cikin Airport ďin. Sai ta ga wani mutum ya taso yana yi wa Abdul dariya suka rungume juna suka gaisa, ya juyo cikin far'a itama ya gaishe ta.
Ihman dai ta zama kamar kurma ko mutum mutumi kawai bin su take yi duk inda suka yi tana karanto duk addu'ar da tazo bakinta har suka iso gaban motar da yazo a ciki. Ya buďe booth ya saka musu trollies ďin su sannan ya buďe mata gidan baya ta shiga, shikuma Abdurraheem ya shiga gaban motar suka tafi.

Idan Ihman tace akwai hankali a tare da ita tayi makekiyar qarya, ita dai ta san ba'a Nigeria take ba amma ko irin wannan buďe idanun da mutum yake yi idan ya sauka a sabon waje yana kallon hanya da tsari da yanayin garin da ya sauka Ihman bata samu sararin yin su ba. Ta san a cikin mota suke, akan titi kuma tafiya suke yi zuwa next destination din su wanda bata sani ba kuma bata samu kowacce irin kwarin guiwar tambaya ba.
Sai da suka iso wata unguwa suka lankwasa wani layi suka zo bakin wani cream ďin Gate sannan ya sauke ajiyar zuciya, kafin wani tsoron da nervousness su sake saukar mata.

"Ihman nan gidan Shehu ne abokina, zaki kwana a wajen matar sa kafin gobe in Allah ya kaimu! Zamu sauke ki ya kaini masauki, naga bai dace akwai gida ki je hotel ba shiyasa muka zabi kizo nan ďin"..

wacece ni?Donde viven las historias. Descúbrelo ahora