WACECE NI??? CHAPTER THIRTY-THREE BY CUTYFANTASIA

226 16 7
                                    

Bamu taba kwanciyar hankali ko farin ciki a wannan gidan ba, ban taba zama na saurare shi ko da minti daya bane balle na gane abinda yake nufi da kalaman da yake tsarawa na ban hakuri da yayi nadama! I hate hin with passion and everything that has to do with him da gidan shi gabadaya.
Nasha attempting guduwa na bar garin, sai kuma naji tsoron kar tsinuwar Hajiya ta bini, nayi iya bakin kokarina na zauna a wannan gidan na kasa, nasha rokon Allah ya futar dani daga wannan gidan ya mayar dani prison watakila nafi samun kwanciyar hankali a can.
Haihuwar Ihman wata qaddara ce wadda ba zan iya cewa komai a kanta ba, amma tunda likitoci suka tabbatar da wanzuwar ta a cikina nake addu'ar Allah ya sanya haihuwarta ce silar ajalina. Ban taba fatan Allah ya saukeni lafiya ba, duk wani tofi ko rubutun da hajiya za ta kawo cikin shukoki na zubawa, ban taba hango wai gashi na haiwu ga abun haihuwar a hannuna ba, ban taba sha'awar sanin me zan haifa balle naji ina son mace ko namiji ba kamar yanda masu ciki suke yi! Idan na tsaya ina bayyana muku irin tsanar da na dinga ji akan Sa'id da unborn child din sa da ahalinsa da gidansa da duk abinda jibance shi, zaku sha mamaki.
Kafin a haifi Ihman na gama kaguwa da rayuwa na gama sarewa da samun duk wani farin ciki da alkhairi don haka mutuwata kawai nake jira, ranar da za'a haifi Ihman ina jin ciwo na shiga daki na kulle kaina na dinga gumurzu ni kadai! Hmmm! Allah me girma, sai aka haife ta ba tare da taimakon kowa ba, a dakina ni kadai ana kiran sallar magriba. Tsananin fargaba da tashin hankalin ganin na haiwu lafiya ban mutu ba ga yarinya sai tsala kuka take yi ya sanya na sume a wajen.
Bansan yanda akayi Sa'id ya balle murfin kofar dakin ko kuma ya kwance ta ba, na dai bude idanu na na ganni akan gadon asibiti ana qara mun ruwa.
Gabadaya iyayena da na shi suna wajen, ashe wai kwanakina biyu bansan halin da nake ciki ba, likita yace na samu hawan jini kuma zuciyata na dab da samun matsala don haka idan har akwai damuwar da suka sani ina da ita ayi gaggawar magance mun domin komai zai iya faruwa.
Ina bude idanu nayi tozali da shi, a hannun shi babyn ce rungume sai hawaye yake yi, wasu irin kibiyoyin bakin ciki suka taso suka soke mun zuciya, cikin matsanancin kuka na soma furzo kalaman da suke zuciyata ba tare da kunyar iyayen shi da yan'uwan shi ko nawa iyayen ba.
"Don Allah ku taimakeni kar ku sake mayar da ni gidan can, wallahi idan kuka mayar dani mutuwa zan yi, wallahi sai dai a dauko gawata! Na tsane shi! Na tsane shi! Wallahi ba zan iya zama da shi ba....."
Gabadaya ba'a cikin hayyacina nake maganar ba, don haka basu samu kwnaciyar hankali nayi shiru ba sai da aka yi mun allurar bacci! Kunsan an ce tsakanin da da iyaye, a wannan karon sai Alajin Sa'id ya dan kufula ya kuma umarci Sa'id ya sake ni saboda zaman namu bashi da wata ma'ana ko amfani! Shi kuma Baba sai yaji ran shi ya sosu. A ganin shi idan akwai wanda ya kamata ya dauki zafi toh shine, duk abubuwan da suka faru shi aka cuta, yayi kara yayi kawaici amma duk da haka sai da aka nuna masa gazawarsa? Sai ran sa ya baci sosai
Maganar sai ta koma ta iyaye kuma, a wannan lokacin kowa sai ya koma bayan dansa, a take kuma Alhajin Sa'id ya saka shi lallai ya sakeni, shi kuma yace idan ya sake ni mutuwa zai yi. Alhajin yace ya yarda ya mutu amma wallahi ba zai sake zama da wadda bata kaunarsa ba.
Haka aka dinga dauki ba dadi, a karshe dai yana kuka yana komai yayi sakin sai kuma aka dawo zancen baby, na sake kafewa cewa ni bana so na bar musu, tunda na tabbatar idan akwai yarsa a hannuna alakar mu bata yanke ba.
A wannan karon ne ya aje guiwoyinsa a kasa ya soma wani irin kuka yana rokona

"Na yarda na amince da duk hukuncin da kika yi mun kuma na amince da duk matakin da kika dauka a kaina! Wannan yarinyar bata da laifi kuma bata san komai ba, a halin yanzu babu abinda take bukata irin kulawa da soyayyarki! Na yarda na amince ba zan taba zuwa wajen ki akan ta ba, na amince na yanke duk wata alaka da ke a tsakaninmu, don Allah ki karbi 'yar nan ki kula da ita domin idan na rabata ta da ke duk ranar da ta girma ta nemi mahaifiyarta da dalilin da ya sanya aka rabata da ke ba zata taba yafe mun ba"
Kowa kukan tausayin Sa'id da babyn shi yake yi amma banda ni, domin zuciyata ta kekashe ta bushe in dai akan Sa'id ne bani da sauran jinkai ko tausayi!
A karshe aka yi yarjejeniya muka zauna akan matsayar cewa na yarda zan karbi yarinyar na shayar da ita amma da sharadin babu Sa'id babu danginsa babu ni! Mahaifinsa cikin kufula yace ya yarda insha Allahu kuma har abada ba zasu sake waiwayar mu ba. Wannan shine silar rushewar tsohuwar alaka da amincin da ke tsakanin iyalan gidan su Sa'id da gidanmu! Duk da cewa daga baya an sulhunta kuma akwai wani lokaci da naji kishin kishin din cewa wai Alajin yana ta neman afuwar Baba da taimakon shi akan ya taimaka ya lallasheni, Sa'id din yana cikin mawuyacin hali sun rasa yanda zasu yi, ban wani maida hankali kan maganar ba balle naji haqiqanin gaskiyar lamarin, tunda nayi aure a lokacin kuma nasa cewa ba za'a sake daura aure akan aure ba, ba kuma za'a ce kashe mun aure a sake bashi ba don haka ban dauki maganar da muhimmanci ba.

"Haka rayuwa taci gaba na dawo gidanmu da wannan jinjira, duk wata kulawa da ake wa baby Inna Hauwa'u ce ta bata, ban taba daukarta da hannuna na rike idan ba ihun yunwa take Inna Hauwa'u ta miko mun ita ba, ban taba kallonta naji wani abu mai kama da so ba, tabbas akwai wani feeling da nake ji a zuciyata me karfi, amma tsanar da nayi wa Sa'id ta danne shi da karfin tsiya. Duk lokacin da na kalleta shi nake tunowa duk da babu kamminsa ko daya a fuskarta sai nawa, duk kokarin da nayi naga na so ta na kasa, domin Allah yana kallo an yi wa zuciyata mugun raunin da ba zai taba warkewa ba har abada.
Kullum kwanan duniya sai nayi wa Sa'id addu'ar fatan sharri da masifa da neman sakayya akan abinda yayi mun, ban taba yin fashi ba, ban taba jin kiyayyar shi ta ragu ba, ban taba jin sassauci ko rangwame akan tsanar da nake mi shi ba kuma ban taba mantawa da saka shi cikin addu'ar tawa ba.

"A wannan shekarar Rukayya tayi haihuwar karshe, Ihman tana watanni goma sha daya, bazan taba mantawa ba ni da Muhammad muka kaita asibiti lokacin yazo mana weekend, kuma cikin mutane yafi kowa kulani, yafi kowa nuna mun rahama da walwala don haka da wuya ka ganni a gidanmu idan ba da wani dalili ba! Cikin dare Rukayya ta haifi Farida, sai dai ko juyawa bata yi ta kalli abinda ta haifa ba Allah ya amshi ranta"

A guje Farida ta taso ta fada jikin Inna tana fashewa da wani irin magigicin kuka! Abinda taji yayi matukar gigita zuciyarta, ya dimautar da ita ya jijjigata, wannan magana ce wadda ko da subutar baki bata taba jin ta a wajen wani ko wata ba! Toh wai wacce irin almara ce ta kai ace ba Inna ce ta haife ta ba?? Ita Farida wai ba diyar Inna bace? Sumewa ne kawai bata yi ba ta shiga wani irin hali. Dakyar Inna ta rarrasheta tana shafa mata baya, sai ajiyar zuciya take saukewa tana maimaita kalaman Innan cikin zuciyarta kamar me tilawa.

"Bayanin halin da mutuwar Rukayya ta sanya mu ciki ba zai misaltu ba, musamman ni da Muhammad! Sai da muka koma kamar wasu mahaukata, kamar majinyata don tsananin dimuwa da tashin hankali.
Babu wata shawara na soma shayar da Farida na kuma yaye Ihman! babu kuma wanda yayi mun magana akan haka, sai ma magungunan da zasu taimaka mun da aka amso mun! A haka Farida da Ihman suka taso kai daya, sai dai ni ban taba yi musu kallo iri daya ba.
Ranar da Rukayya ta cika kwanaki arba'in Baba ya kirani, yayi mun nasiha mai shiga jiki, har sai da naji tsoro ya kamani, a karshe ya gaya mun cewa wai sun daura mun aure da Muhammad a madadin Rukayya domin babu wadda zata iya rikewa Muhammad da Rukayya yayansu a duniya da ya kai ni, idan kuma har kaunar da nake yi wa Rukayyan da yayanta gaskiya ce toh na amince da zabinsu!
Kuka kawai nake yi ina jin wani irin tashin hankali, wai babu Rukayya a duniya, ni Asiya ni ce zan auri Muhammad mijinta wanda nake wa kallon dan'uwa uwa daya uba daya? Ni zan zauna a madadin Rukayya a gidanta? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!! Hakika nayi kuka! Nayi kuka!! Nayi kuka!!
Sai dai bani da zabi a wannan lokacin wanda ya wuce na rungumi qaddarata hannu bibiyu na rungumi wadannan marayun da babu kamar su cikin zuciyata."

wacece ni?Where stories live. Discover now