WACECE NI??? BY CUTYFANTASIA PAGE FPURTEEN

239 18 3
                                    

Two days later.
................................
Inna ce gaban gadon Ihman tana taimaka mata ta tashi zaune domin tasha kunun da aka dama mata, daga shi sai tea take sha kasancewar su cikin jerin abincin da ake iya runtse idanu a kwalkwale ba tare da tauna ko tsotsa ba, soup din ma da aka ce lallai ta dinga ci inda aka zuba haka ake daukewa.
Ihman ta farka cikin halin da yafi wanda ake hasashe muni, da farko bata magana daga hawaye sai kuka, sai da ta ga hankali yayi mugun tashi akan tunanin ko ta daina maganar ne sannan take yin kalma daya ko biyu idan ta zama matukar dole.

Tun da ta bude idanu Inna take gani a kusa da ita tana yi mata hidima kan jiki kan karfi cikin wata iriyar kulawar da ta bata masifar mamaki, she treats her kamar kwai akan faifai, sannan tana hango wasu irin mixed emotions cikin idanun Innar wanda ba don halin da take ciki ba da ta tsaya tayi cikakken tunani akan su da kuma dalilin faruwar su.

But she has let go of everything, ta ajiye duk wani abu a gefe da yake tsakanin ta da Inna wanda ya faru ta haqa rami mai zurfi a cikin zuciyarta ta binne, koma menene ta tabbatar Inna mahaifiyarta ce kuma duk duniya bata da tamkar ta, Abinda ya faru ya bude mata idanu ga boyayyiyar soyayyar da Inna take mata wadda a kullum kwanan duniya take kokarin dannewa a bisa wani dalili wanda ita kadai ta san shi, a tunanin Ihman a garin kokarin boye wannan soyayyar Inna take nuna mata qiyayya mai karfi, but a jiya a lokacin da ta ga ana kokarin cutar da ita, abubuwan da ta hango a idanun Inna sun tabbatar mata da cewa Inna ce ta haife ta, wannan tsoro, firgici, tashin hankali da sadaukarwar da ta gani a idanun Inna irin na uwa mahaifiya ne kawai, a duk lokacin da bawa ya shiga cikin wani ibtila'i ko masifa, a lokacin yake gane masoyin sa na gaskiya kuma har abada ba ya manta wanda ya tsaya masa a wannan lokaci.
Tunda ta bude ido Inna take gani at her service, da dukkan soyayya da kulawa.
Idan za ta iya tunawa bata taba ganin Innan ta kai wani abu bakin ta ba bayan kunun nan da Adda Wasila take damowa ta kawo kullum. Tayi zuru-zuru ta rame gabadaya ta futa hayyacinta, ga shi kuma Abba ya dauki wani fushi mara tushe da ita, sama sama yake amsa gaisuwar ta babu wata doguwar magana a tsakanin su.
A yanzu kam kwakwalwarta bata da karfin da za ta dauki wannan mathematical formulas din tayi solving din su don haka ta ajiye komai a gefe tayi embracing sabuwar alakar da Inna ta bijiro mata da ita wholeheartedly domin a wannan lokacin, tafi bukatar Innan fiye da kowa da komai a rayuwarta.

Hamma kuwa gabadaya ya koma restless and helpless. Mutanen da suka fi soyuwa a rayuwar shi ne cikin gagarumar damuwa, daga Innan har Abba ya kasa gane kan su, ya kasa gano abinda ya shiga tsakanin su, abinda yake kulle kan shi shine ta yaya abinda ya faru da Ihman yake da alaka da fushin Abba akan Inna? Meye laifin ta?
Ita kuma Innan da ba ta da wanda take zaunar wa ta budewa zuciyar ta irin shi wai yau ita ce ke kauce masa tana yakice duk wani dalili da zai kebanta su su biyu a waje daya don gudun kar yayi mata tambaya akan abubuwan mamakin da suke faruwa.

A cikin wadannan kwanaki ashirin da biyar na zaman asibitin da Ihman tayi ta ga matukar kulawa da soyayya daga mutanen da suka fi kowa kusanci da ita, ta ga gata kuma ta ga kulawa irin wadda ba zata taba mantawa ba har karshen rayuwarta, da ace wani al'amari ne wanda bai kai abinda ya faru da ita tsauri da muni ba, da haqiqa zata yi farin cikin faruwar shi domin ya yi mata aikin da kowa ya kasa yi mata, ya sasanta tsakaninta da Innarta kuma ya warware mata zargin kiyayyar da take yi wa Innan akan ta.
Tun sati daya da faruwar al'amarin Aunty ta dawo daga Agadez, bata samu labari ba sai da ta dawo kuma yanayin da ta ga Abban ya sanya ta shiga mugun taitayin ta domin tayi imanin idan tayi wasa jakar da ta dawo ita zata sake dauka ta koma. Ga maganar Asma'u ta tsangare mata, dan gidan Aunty Zinatun Haidar ya dawo, amma gabadaya abubuwa ba sa tafiya as they planned, yan mata ne da shi buhu buhu, itama Asma'un dalilin da yasa yake kulatan kenan ba wai auren ta zai ba. Gashi dan gatan babansa, itama Zinatun lallabawa take In dai a akan shi ne, Asma'u kuma ta tubure ta mato ita babu wanda take so sai shi. Wannan dalilin ya sanya hankalin ta ba'a kwance yake yanda ya kamata ba balle ta samu sararin yi wa Inna rashin mutunci, duk da ta fahimci matsalar da take tsakanin Inna da Abban wadda babu ita kafin ta tafi.

wacece ni?Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin