WACECE NI??? BY CUTYFANTASIA CHAPTER THIRTY-ONE

181 13 2
                                    

Unedited

Blurry Sa'id yake kallon Ihman yana faman kokawa da numfashin sa, kwakwalwar shi na hasko mi shi hoton abinda yafi so fiye da komai a rayuwa a gaban shi tana gaya mi shi kalmomin da yafi bukatar ji fiye da komai a duniya daga bakinta....
But matsanancin halin da ya shiga ya hana shi kowacce irin damar da zai iya yunkurawa yayi wani abu, duk da haka salon bugun zuciyar ta shi ya sauya, dalilin da ya sanya Dr Hassan cewa a tafi asibiti kenan kamar yanda yaso tun zuwan sa gidan bayan an kira shi sai Alhaji ya hana domin gani yake ba zasu isa ba Sa'id zai cika, gara ya mutu a cikin dakin sa a tsakiyar su.

Cikin gaggawa aka saka shi cikin mota, suka dauki hanyar asibiti zukatansu ma matukar fatan samun lafiyar shi da kwanciyar hankali bakidaya.
A wannan ranar ne kuma Iya Raheem ta sauka a garin su, a gidan su ba tare da ta wuce gidanta da ke garin Kano ba saboda tsabar son sanin halin da dan'uwanta yake ciki da kuma taimakon da za ta iya bayarwa a gare shi.
......................................................................................
A babban falon Hajiya aka gudanar da taron, Ita Hajiyar kanta, Baba Bala Yayan Inna, sai Abba, sannan yayanta Hamma, Adda Wasila da Farida.
Cikin wata irin nutsuwa Inna take zaune, kwakwalwarta na tariyo mata abubuwan da suka faru dalla-dalla daya bayan daya. Ta dade kanta a sunkuye kafin ta samu courage din bude baki ta soma basu cikakken labarin abubuwan da ba kowannen su suka sani ba! Da kuma makasudin faruwar abubuwan da suke faruwa a yanzu, da dalilin kasancewar ta cikin wannan yanayin da mutane suke kalubalantar ta a kansa.

Bara muji daga bakin Inna wai daga ina cakwakiyar ta samo asali ne? (In brief)

TUSHE
"Mun taso cikin kyakykyawar kulawa a gaban iyayen mu, Kamar yanda ku ka sani Bala shi ne babbanmu, sai Rukayya yayata sannan ni. Mun taso cikin tsananin zumunci da kaunar juna da Rukayya duk da cewa akwai ratar shekaru shida a tsakaninmu.
Na kan manta da Hajiya na tafi wajen ta a duk lokutan da nake bukatar taimako ko shawara ko wanda zan yi wa magana naji sanyi.

Lokacin da ta kammala secondary ni kuma na shiga aji daya, a shekarar ne kuma ta tafi jami'ar Ahmadu Bello ta soma karatun gaba da secondary dinta a fannin Accouting, anan ne kuma Allah ya hada ta da Muhammad(Abbanku) yana shekarar karshe ita tana aji daya........."

With confusion Farida take kallon Inna! Ta san Innan tana da elder sister ta rasu, ta kuma sha ganin hoton ta, amma kuma wata magana taji tana yi tsakanin Yayarta ta da Abba, mahaifinsu kenan! Toh me ya kawo wannan hadin gambizar? Dakyar ta danne tunanin da yaso fin karfin zuciyarta taci gaba da sauraren Inna with open ears

"Soyayya ce mai tsafta da ban mamaki a tsakain Rukayya da Muhammad irin wadda duk wanda ya zauna da daya daga cikin su sai ya gane irin soyayyar da yake wa dayan. A hankali Muhammad ya koma kamar dan gidanmu, bashi da shamaki da zuwa a kowanne lokaci, ya saba da kowa kuma ya shiga zuciyar kowa saboda kyakykyawar mu'amala da tarbiyyarsa.
Rukayya tana aji uku a jami'a aka daura auren su da Muhammad, wanda yake hannun Uncle din shi wato qanin mahaifinsa a jihar Bauchi kafin a kirkiro garin Gombe. Su yan asalin kasar Mali ne, karatu ne ya tsallako da kanin mahaifin na shi kasar nan, daga can ya taho da matar shi wadda bata taba haihuwa ba, sai yayanshi kafin Allah yayi masa rasuwa ya dauki Abbanku ya ba shi, yana shekaru biyu bayan ya rasa mahaifiyarsa, wanda ba jimawa da auren su Muhammad suka yi accident su ma suka rasu, sai Muhammad ya kasance ba shi da wasu makusanta kamar iyayen mu, suka hada shi da mu suka rike cikin gaskiya da amana muka sake dunkulewa muka zama abu daya.
Daga baya kuma takanas Baba ya nemi hanyar da yabi ya sada Muhammad da danginsa da ke Mali, duk da cewa basu da yawa kuma basu shaku ba.

"Shekarar su daya da aure Rukayya ta samu da namiji wanda Baba ya sanyawa suna Muhammadul Quraish, a lokacin suna zaune ne a garin Zaria, Muhammad yana lecturing a ABU ita tana karasa karatun ta, da taimakon aminin uncle din Muhammad ya samu aikin banki a jihar Bauchi, a wani bangare na gidan Uncle din shi Baba Yusuf suka zauna, ba dadewa ne kuma suka yi accident a hanyar su ta zuwa Mali suka rasu a take, tun kafin ya mutu ya rubuta takarda cewa duk abinda ya mallaka idan har ya mutu bai haiwu ba toh na Muhammad ne, tunda bashi da iyaye duk sun rasu.
A wannan gidan Rukayya ta sake haihuwa ta biyu, yaron bai zo da rai ba, a lokacin ne kuma ta hadu da lalular eclapcy(farfadiya). Ba karamar wahala aka sha akan ta da magani ba, amma ciwo kamar tura shi ake yi, maganin asibiti da na gargajiya babu wanda ba'a gwada ba amma abun sai godiyar Allah kawai, wasu su ce a wajen haihuwa ne ta samu ciwon, wasu suce shafar aljanu ne wasu ma suce asiri ne, wannan ciwo na Rukayya ya daga mana hankali ya saka mu cikin damuwa kuma shine sanadin komawa ta gidan ta gabadaya, a lokacin na kammala secondary kenan.
Wannan shawarar Muhammad ce, saboda shi yanayin aikinsa ba zai bashi damar ya kasance tare da ita a nan Kano ba, idan kuma ya tafi ya barta baya iya abun kirki a wajen aikin, sannan ga gidanshi da komai acan, sai ya roki Baba akan don Allah ya taimke shi ta basu ni na zauna tare da su aga mai Allah zai yi akan ciwon nata, idan ta samu sauki sai na dawo.....
Dakyar ya shawo kan su Baba suka amince muka tattara muka koma gidansu tare, Tun daga ranar da na koma gidan Rukayya na karbi duk wasu responsibility nata a gidan ta, tun daga kan girki, gyaran gida zuwa kula da Quraish,Rukayya ta haifi Quraish ne kawai amma duk wasu al'amura na rayuwa a wajena ya samu, a jikina yake bacci, a jikina yake tashi, da yatsuna yake ci, da su yake sha, ni nake masa wanka, nayi masa abinci na ba shi yaci na shirya shi, na debe masa kewar kowacce irin kulawa ta uwa.
Wata irin shakuwa ce ta shiga tsakanin mu ta ban mamaki, har ya kasance ya daina kallon Rukayya a matsayin wata bangare a rayuwar shi balle kuma uwa. A mafi yawan lokuta tafi shiga cikin daki ta kulle tsawon yini, ta daina magana mai tsayi kuma bata cika fahimta ba idan kayi mata, ta sauya completely daga Rukayyan da muka sani zuwa wata irin stranger, domin bayan ciwon farfadiyan an sake diagnosing din ta da amnesia wani ciwo da ke saka dan'adam manta rayuwar shi.
Kallon mu take yi kawai amma bata cika gane mu ba, wani lokacin muyi hira normal wani lokacin kuma tayi ta kallon mu kamar ranar ta fara ganinmu, watarana kuma ta shige daki ta kulle kanta bata sauraron kowa.
Duk wanda ya ga Muhammad a wannan lokacin sai ya bashi tausayi, ya futa hayyacinsa gabadaya ya lalace, duk wani attention na rayuwarsa yana kan Rukayya da Quraish. A karshe dai da abun yaki yiwuwa dole muka tattara gabadaya muka dawo Kano domin ba zan iya ni kadai ba don kullum ciwon nata gaba yake yi.

"Mun dawo Kano, Baba ya bawa Muhammad gidan shi da ke cikin wannan unguwar muka koma da zama, Hajiya ta dauko wata dattijuwar kakarta take taya mu zama, domin Muhammad kuka ya dinga yi yana cewa idan aka dawo da Rukayya gida aka ajiye ba zai yafe wa kansa ba, tunani zai yi tayi kamar ya gaza bata kulawa, kamar an raba auren nasu, kamar shikenan rayuwar su ta qare a tare. Baba yaji tausayin sa ya kawo wannan shawarar, amma ya tabbatar mi shi da cewa bai yarda ya ajiye aikinsa ya dawo Kano yayi zaman banza ba, ya koma aiki idan yaso ya dinga zuwa ganinsu duk bayan sati ko sati biyu. A cikin wannan lokacin ne kuma Baba ya matsa mun sai na cigaba da karatu, babu kalar kuka da magiyar da ban yi ba don nuna cewa bana so a kyaleni da yarona Quraishi wanda nake jin kamar bani da wani abinda yafi shi muhimmanci cikin rayuwata. Soyayyar da ke tsakanina da mahaifiyarsu ta rikide ta koma kan shi har ma da qarin tausayi da jinqai.
Duk abinda zan yi sai da nayi amma ban samu goyon bayan kowa ba, a dole aka samar mun gurbin karatu a Bayero Univerity, haka nake yini karatu ina dawowa na zarce gidan Rukayya nayi mata abubuwan da ni kadai nake iya yi matan da gudan jinina Quraishi wanda sai da aka hada mi shi da rubutun dangana kafin ya hakura da makarantar da aka sa shi saboda baya ganina tun safe sai yamma.
Cikin nasara na shiga matakin qarshe a jami'a, a wannan shekarar ne Rukayya ta haifi Wasila, murna a wajena ba'a cewa komai, Quraishi ya girma ya shiga primary sai gidan ya sake yi mana dadi albarkacin wannan baby da hidimarta.
Kamar Quraishi ni nayi rainon Wasila duk da ina karatu lokacin, amma ina dawowa bani da lokacin komai sai nasu, a jikina take kwana, sai na yi mata wanka na shirya ta nake tafiya makaranta, ranar da zan tafi da sassafe kuwa sai dai a jira na dawo da yamma, idan kuwa aka yi mun karambani aka yi mata na dinga mita kenan.
Ina dab da kammala karatu Baba ya soma yi mun maganar aure domin ya fahimci gabadaya hankalina bai kai wajen ba, shekaruna ashirin da daya ga tarin maneman amma kowa yazo korar shi nake nace ban isa aure ba, dalilina guda a duniya shi ne idan nayi aure na bar yarana a hannun wa? Ko kuwa rabani za'ayi da su? Wannan tunanin yake sawa naji na tsani kalmar aure balle wani saurayi ko soyayya.
Lokacin da Baba ya matsa mun yayi mun fada na tabbatar da gaske abinda suke so nayi kenan, sumewa nayi a wajen saboda rudani da fargaba, babu horror din da ya kai rabani da wadannan yaran tsoro da tashin hankali. Toh daga nan suka shafa mun lafiya, aka koma addu'a hankalinsu ya kara tashi matuka akanmu ni da Rukayya domin kowacce matsalarta abar dubawa ce.

A wannan shekarar Baba yayi wa Muhammad aure, auren da bai taba tunani ba, bai taba tsammani ba kuma bai karba ba sai da Baban yace idan har bai amince ba babu shi babu shi ! Ya karbar mi shi auren Aunty ne a hannun baban ta wanda tafiyar aikin hajji ta hada su tare da ita da kishiyar mamanta, Baba ya yaba sosai da nutsuwa da tarbiyyar ta, domin Aunty macijin sari ka noke ce, idan ta rikide kalar tausayi ba zaka ce za'a saka mata hannu a baki ta iya cizawa ba.
Aminta ce sosai ta kullu tsakanin Baban ta da Baba, har suka soma zumunci bayan dawowarsu, toh a dalilin shigata makaranta ne hirar take hada su da Baban Aunty, yake wa Baba complain cewa shi bashi da buri irin yaga ta kammala karatu yayi mata aure domin tana neman ta soma sauya halinta, da wasu abubuwan ma da ya sakaya bai fada ba, yakana da kirki irin na mutanen da ya sa Baba yayi subul yace yana da idan Baban Auntyn zai bashi zai hada su, kamar wasa maganar ta zama babba, Hajiya bata ce komai ba domin a lokacin lafiyar Rukayya tafi komai muhimmanci a gare ta, kuma idan adalci za'ayi toh ya kamata ace Muhammad ya samu wata macen ya kaita Bauchi domin wani lokacin ko abinda zai ci ma wahala yake masa, a wajen aiki yake wuni, lokacin da ya dawo dare yayi kuma ga gaji, shikuma ba gwanin cin abincin restaurants ba, lokaci daya ulcer ta kama shi, ga damuwar ciwon Rukayya da kewar yaransa, sai Baba yake ganin kara mi shi aure will be a solution.

"Ya auri Aunty ne a bisa umarni da biyayyar Baba, kuma yayi alkawarin ba zai ba shi kunya ba, wannan dalilin ne ya sa yake hakuri da Aunty for all this while darajar Baba take ci da girman alkawarin da ya dauka akan rike ta amana.
Tana ganin shi tace taji tana gani tana so, kuma aka yi auren cikin qanqanin lokaci, watanni tara cif da auren aka haifi Sadik, suna can Bauchi mu muna Kano muna jinyar Rukayya. Muhammad bai taba fashin zuwa duk sati garin Kano ba, komai ruwa komai rana komai iska ko bashi da lafiya sai yazo, ba don kashedin da Baba yayi masa ba, wasu lokutan katsidik muke ganin shi ranar laraba, wai hankalin shi ne bai kwanta ba ya taho ya gan mu. Auren da yayi bai rage ko kwayar zarra na soyayya da kulawar da yake wa Rukayya ba don haka muka sake ba shi girma da daraja ta musamman a rayuwar mu."

wacece ni?Where stories live. Discover now