Kallon kallo aka tsaya ana yi tsakanin uban da yar kowanne cikin wani irin yanayi wanda biro ba zai iya rubutawa kai tsaye ba, suna cikin wannan halin na shock, dimuwa da galabaita Aunt Halima ta shigo falon, hankalinta yayi mugun tashi domin ba ta wannan hanyar suka so su hadu ba, ba kai tsaye suka tsara Sa'id zai ga Ihman ba, basu gayawa kowa da zuwanta ba kamar yanda Alaji yace sai bayan an sauko daga jumu'a an shigo an yi lunch sannan zai kira taro zuwa parlour yayi bayanin komai dalla-dalla ga iyalan gabadaya sannan ya gabatar musu da Ihman.
Ko da basu ga Sa'id a masallaci ba sai yace a hakura da taron sai an je an dubo shi, idan lafiyar shi qalau sai a gaya masa da daddare ya shigo, idan kuma baya jin dadi sai a bari sai ya samu sauki saboda sanin matukar girman wannan al'amari a wajen Sa'id yake so ya sanar da shi da kansa a tsanaki cikin nutsuwa kada ya rude ko ya famo masa mikin tsohon ciwon da ya rayu yana jinya har yau bai warke ba.
Toh sai kuma Allah bai tsara hakan ba, ya shigo a bazata ta kofar ma ba kasafai ya shigowa cikin gidan ba domin gudun cin karo da baki ko wanda zai ja shi yin doguwar magana.Tun Sa'id na kallon Ihman cikin hayyaci da hankalin sa yana recalling abubuwan da suka shude daki daki tun daga lokacin haduwar sa da Asiya, qaddarar da ta faru a tsakanin su, zuwa haihuwar Ihman........har ya kasance zuciyar shi tayi matukar raunin da ta daina bugawa yanda ya kamata, numfashin sa ya soma seizing idanun shi na lumshewa, Ganin haka yasa Aunt Halima ta runtuma da gudu zuwa garden tana neman taimako.
Gabadayan su suka taso cikin rige rige suka shigo cikin gidan suka karaso falon, tuni har ya rasa support ya sulale yana neman kai wa kasa Baba(kaninsa) da Abdurraheem suka taro shi cikin matukar zafin nama ya fada jikin su babu numfashi.Duk wannan budurin da ake Ihman tana tsaye kawai tana kallo kamar wadda aka dasa, ko motsi bata yi ba,ko gizau, ko in kula kuma.........a karshe ma sai ta tabe baki cikin rashin damuwa ta dauki robar ruwan ta ta shige dakin da aka sauketa ba tare da ta sake kallon ko gefen da Sa'id yake kwance jikin su Abdurraheem magashiyan ba.
A fusace A.Aisha ta mike zata bi ta Alaji yayi maza ya daga mata hannu yana cewa"Ku kyale ta! Ku kyale ta!! A kira wo Doctor yanzu"
Cikin mintina goma sha biyar Dr Hassan ya iso gidan, a take ya ba shi dukkan kulawar da yake bukata ya kuma yi musu bayanin cewa shock ne kawai ya gigita shi amma yayi mi shi allurar bacci, zai tashi bayan ya samu hutu.
Dakin Alaji aka mayar da shi aka rage mi shi karfin Ac da fitila aka futa aka bar shi da Aminu kawai a bisa umarmin Dr. Hassan da yace kar a sa shi a gaba a dame shi da hayaniya, duk da haka Alaji bai bari ya tafi ba cewa yayi ya koma guest room ya zauna ba zai bar gidan ba sai Sa'id ya farka ya duba yanayin jikin na shi.Bayan Ihman ta shiga dakin da take ta rufe kofa, sai ta sake murza key domin bata bukatar gani ko jin kowa a wannan yanayin, magashiyan ta fada kan gadon dakin tana wani irin numfarfashi zuciyarta na zafi, qaddarar da ta same ta ce ta fado ran ta, ranar da abun ya faru da lokacin da yanayin da azabar da ta tsinci kanta a ciki ta ruhi da gangar jiki, zuwa samun saukin ta, accepting qaddarar ta, ta gangaro lokacin tafiyar Faris da heart break din da tafiyar ta shi ta haddasa mata, da duk wasu abubuwan da suka biyo baya har zuwa ranar da taci karo da wannan littafi mafi muhimmaci a cikin rayuwarta wanda ya warware mata duk wani kulli da dauri da zargin da take rayuwa a ciki ya bayyana mata gaskiyar WACECE ITA!
Ta tuna futowar ta daga gida ita kadai a karo na farko a rayuwarta, zuwanta Abuja da haduwar ta da Iya Raheem wadda ta kasance Yayar mahaifinta ba tare da sun sani ba, zuwan ta Ghana da uwa uba wannan safiyar da suka yi idanu biyu da mutumin da babu shakka babu rabawa biyu shi ne SA'ID! Mutumin da yayi mata sanadin duk wata qaddara da masifa da tashin hankali da bakin cikin da take ciki.
Ta tuna irin alakar da ta taso Inna tana yi da ita, muguwar tsana da tsangwamar da tayi mata, har ta kai tana tunanin cewa ba ita ce mahaifiyarta ba..........Wani irin magigicin kuka ne ya kwace mata, ta kifa kanta a tsakanin pillows tana jin kamar zuciyar ta zata futo daga cikin kirjinta, bayan duk wannan abubuwan da suka faru, still ga wani tabon nan a jikinta wanda ta tabbatar shi ne zai karasa rushe duk wani sauran farin ciki da daraja da value da future din rayuwarta gabadaya.
VOCÊ ESTÁ LENDO
wacece ni?
Ficção GeralWacece ni labari ne akan matashiyar da ta taso cikin wata irin rayuwa mai ďaure kai da jan hankali. Ba abun mamaki bane idan kishiyar mahaifiyar mutum ta tsane shi amma mahaifiyar kanta ta nunawa ďanta tsantsar tsana da tsangwama da kyara abun ban m...