WACECE NI??? CHAPTER FIFTEEN BY CUTYFATASIA

217 12 0
                                    

Sun kai minti goma a haka, ita tana faman sake-sake da wasi-wasi shi kuma yana studyn din ta carefully. Sai da ya tabbatar ba zata yi magana ba sannan yayi gyaran murya ya soma maganar shi with alot of charisma and calmness.

"Habibty yau babu sannu da zuwa balle gaisuwa? Ko kuwa yau bako na koma miki? Ko kuma bakya son magana na baki time kada na takura miki? Idan har baki shirya magana da ni ba, kada ki takura kan ki, I will wait till you are ready and OK to talk to me even if it means waiting for you for the next decade."

A maimakon tayi maganar ko ta ba shi amsa, sai ya ga hawaye na gudun famfalaki akan fuskarta, kanta har yanzu a sunkuye, jikinta na shaking a hankali da alama she is panicking. Sai ya tausasa sauti yaci gaba da magana with the most soothing voice

"Tunda hakane let me go straight to the point, I can see that you are nervous, wanda ya bani mamaki da kuma jin rashin dadi, idan kin manta bari na tuna miki, ni Salman nayi miki alkawari cewa zan kasance da ke a kowanne hali a kowanne yanayi a kowanne lokaci, ina son ki ba don kyale kyale ta sura ko halittar ki ba, zuciyarki da ainihin ke kan ki nake so don haka wasu abubuwa wanda zasu shigo komai girmansu ba zasu chanja abinda nake ji a kan ki ba!

"Idan nace abinda ya faru da ke bai taba ni ba, bai girgizani ya karya mun zuciya ba nayi katotuwar karya, amma ba wai saboda ni zan aure ki ko tunanin wani abu naki ya ragu ko ya tawaya ba, ina jin zafi ne saboda cutar da ke da aka yi, saboda bakin ciki da trauma din da aka jefa ki ciki, saboda azaba da radadin jiki da na zuciya da kika fuskanta a dalilin haka Ihman!
Abinda ya faru da ke kaddara ce, kuma daya daga cikin kalubale na rayuwa, shin kin manta ni da ke mun yi wa juna alkawarin cewa we will be there for each other in all situations in every situation? We will help each other go through any challenge and overcome it? Kin manta mun yi wa juna alkawarin zamu rayu tare cikin dadi da akasin sa?
Idan kin manta bara na tuna miki
Ni salmanu ba gangar jikin Ihman nake so ba, ba soyayyar yaudara ko ta wani qayyadadden lokaci nake miki ba, ba soyayya nake miki akan wani sharadi ko ka'ida ko yarjeniniya ba, ina sonki ne fisabilillahi, ita kuwa soyayyar da aka gina saboda Allah wani abu ba ya shigowa ya rushe ta komai girman sa.

"Na san zaki tambayi kan ki idan gaskiya ce magana ta me yasa nayi shiru na daina neman ki tsahon wannan lokacin? Me yasa ban zo tun da wuri na kasance cikin mutanen da zaki fara kalla a kusa da ke wanda zasu baki hope da kwantar miki da hankali ba?
Amsar na wajen Yayanki Hamma, domin shi ne ya yayi mun kashedin kada na sake na kira ki sai ya bani izini tun safiyar da abun ya faru da ya bugo waya ya sanar dani komai..
Bansan manufar shi akan hakan ba amma koma menene na amsa kai tsaye saboda ina kallon shi a wani mutum da yafi kowa nuna kulawa da damuwa a kan ki! Ba zan iya zaunawa na baki labarin halin da na shiga cikin wadannan kwanakin ba, kawai kiyi kiyasin halin da ke kika shiga, ciwon a jikin ki kawai yake amma nafi ki jin radadi da zoginsa. Those days were miserable a gare ni fiye da duk yanda zan bayyana miki.

"A kullum ina kiran Hamma na tambaye shi jikin ki, tare da magiyar yaushe zan gan ki ko naji muryar ki, bai bani dama ba sai yau da safe, yana yi mun izini ban kara awa daya a Kano ba na dauko hanya na taho with alot of fear din ko za ki karbi uzurina na rashin zuwana gare ki da wuri.
Gani gare ki Ihman, ina fatan baki chanja mun matsayi ba, baki kullace ni ba, baki juya mun baya ba? Don Allah ki ajiye duk abubuwan da suka faru a mizanin kaddara wadda kowanne dan'adam bai fi karfin samun kansa a ciki ba, ki manta da komai mu fuskanci auren da yake gabanmu........."

Kukan dai take yi, sai dai ya chanja salo daga na fargaba da tsoro da bakin ciki zuwa na tausayi da farin ciki da tsantsar godiya ga Allah da alkhairin da yayi mata na kyautar mutum irin Faris.
Duk yanda taso ta tsayar da kukan ta nuna mi shi godiya da amincewar ta bata samu dama ba, a karshe sai sallamarta yayi ta shiga cikin gida yace zai dawo gobe.
........................................................................
Karfe tara na dare ta amsa kiran Abba a dakin sa, ta nemi waje ta zauna bayan ta gaishe shi, Inna da Hamma suna dakin tare da shi kuma Hamman ne ya kalmashe kafa yayi gyaran murya ya kora mata bayanin da aka kirawo ta domin sa.

wacece ni?Donde viven las historias. Descúbrelo ahora