WACECE NI??? BY CUTYFANTASIA PAGE TWELVE

272 12 0
                                    

A wani daren larabar da ba zata taba mantawa ba a cikin kundin tarihin rayuwarta, hausawa suka ce laraba tabawa ranar samu, toh ga Ihman wayewar garin larabar watan 23 ga watan May, shi ya tafi da dukkan wata samuwa ta alkhairi da farin cikin da take ciki a rayuwar ta.

Gabadaya shirin bikin ta ake yi gadan gadan domin watanni biyu rak suka rage, tun daga kan gado zuwa cokali Hamma ya kammala siya, hotunan yake tura musu a waya Adda Wasila da Farida su tayata zaba sannan yayi placing order, dai dai da kayan futar biki suna wajen dinki, babu yanda yan'uwanta basu yi da ita ba tace bata son biki, shima kuma angon yace bai yarda da duk wani event da za'a hadu maza da mata ba, Hamma yace a kyale su suyi abinda suke so, auren su ne, duk wanda yake son wani sha'ani ya bari idan na shi bikin yazo yayi, da wannan aka bar events guda biyu, za'a yi kamu da yinin biki a harabar gidansu, washegari ayi daurin aure sai a zarce da walima ta mata zallah, ranar asabar akai amarya Kano.

A ranar talatar da al'amarin ya faru a gidan Adda Wasila ta wuni, Kamal ne yayi waya ya sanar Wasilan bata da lafiya, ya kuma nemi alfarmar Farida ko Ihman suje su taimaketa da ayyukan gida kasancewar suna hutun zangon farkon karatu.
Sai karfe tara na dare Ihman ta tubure ita gida zata koma ba zata kwana ba, juyin duniya Adda wasila da Kamal suka kasa shawo kanta, ganin taki yarda Kamal yace su kyaleta, ba halinta bane gaddama musamman da na gaba da ita, he's sure tana da wani dalilin da take son komawa gida saboda shi har Addan tana cewa idan har Salman ne yake tafe a daren nan toh tayi alkawari ba zai ganta ba, yanda ta bata musu budget itama sai ta bata masa. da haka suka rabu Kamal ya dauki Ihman ya kaita har gida. sai ganin ta kawai suka yi a tsakiyar falo ana kallon labarai, Inna ce ta fara cewa lafiya?

cikin sanyin jiki Ihman ta zauna Abba na maimata tambayar da Inna tayi mata, a sanyaye tace

"babu komai Abba, kawai ji nayi bana so na kwana! so nake na dawo gida"

"ko dai sun yi miki wani abu ne Ihman? gaya mun"

"Abba wallahi basu yi mun komai ba! kawai dai ji nayi hankalina yaki kwanciya sai na dawo gida. kayi hakuri Abba gobe sai na koma"

sosai Abban ya kalleta, she looks strange a wannan rana, tayi wani sanyi kalau kuma babu karsashi ko kadan a tare da ita, da haka ta haura sama ta shige dakinta, ranar ko kayan bacci bata iya sakewa ba ta kwanta a gadonta, bacci mai nauyi ya dauke ta ba tare da tayi bitar karatun da ta saba yi na dare ba.

Inna ta shigo dakin ta same ta tana bacci, mamaki ya kamata domin Ihman ba gwanar bacci da kaya mai nauyi bace, a irin wannan lokacin ma zaka same ta ne tana karatun boko, idan ta kammala tayi takarar al'qurani yanda ya sawwaka sannan ta shirya ta kwanta bacci, a hankali ta isa gaban gadonta ta tsaya tana kallon ta, kallo irin wanda bata taba yi mata irin sa ba, kallo ne for the first time a rayuwar ta da tayi wa Ihman with care and concern, wanda ita kadai tasan dalilin hakan.

Har zata juya sai ta fasa, ta saka hannu ta kara a goshinta domin tunanin ko bata da lafiya, Ihman ta bude idanu a hankali tana kallon Inna cikin mamaki, duk da cewa a yan watannin nan al'amura sun soma sauki da gyaruwa a tsakanin su amma Inna bata taba yi mata irin haka ba, ba zata iya tunawa tsahon rayuwarta lokacin da Inna ta damu da jin temperature din jikinta wai don bata da lafiya ba, with this concern da soyayyar da take hangowa cikin kwayar idanunta baro baro! ko dai ta dauka Farida ke kwance ba ita ba?

"lafiyar ki kalau? me yasa ki bacci yanzu? me ya faru a gidan Wasilar kika fasa kwana?"

maganar Inna ta katse tunaninta ta kuma sake jefa ta cikin wani rudin da mamaki da al'ajabin, domin kalaman sun tabbatar mata cewa Inna ta san da ita take magana, in her whole life Inna bata taba yi mata wata tambaya domin kyautatawa ko kulawa ko son jin halin da take ciki ba, babu abinda ya dame ta da ita a kowanne hali! Toh me ya faru?

wacece ni?Where stories live. Discover now