WACECE NI??? BY CUTYFANTASIA PAGE 2

510 24 1
                                    

                                   Tushe
Quraish wanda suke kira da Hamma shine babba a gidan Alhaji Muhammad Manager,dattijon shekaru sittin da bakwai mai kamala da saukin kai da nagarta.Matan auren shi guda biyu ne Inna bafulatanar garin Garo ta jihar Kano da kuma Aunty ba'abziniyar kasar Niger.

Inna tana da ýaýa shida, Quraish shi ne babba wanda yayi karatun primary da secondary a tsakanin Gombe da Kano sannan ya tsallaka kasar China ya haďo degree ďin shi a fannin economics. Quraish tun da ya tashi mutum ne mai tsananin hakuri da juriya da kawaici kamar Inna, domin da wuya kayi masa abinda zai ďaga idanu ya kalle ka balle ya tanka.
Ya taso da matukar kaunar karatun al'qurani sai dai ba kamar yanda yaso ba don bai samu yin tilawa ba da yake komai rabo ne. Abu na biyu da Quraish yake so shi ne kasuwanci, ya juya sisi ta koma kobo ya juya kobo ta koma naira. Tun yana karami yake gwada sana'o'i masu sauki wanda Abba yake iya kokarin hana shi domin kada ya ďauke masa hankali daga karatu. Ďaya daga cikin dalilin ma da ya sanya shi cilla shi can birnin sin kenan, toh da yake abun a zuciyar sa yake da yaje China sai ya samu kasar cibiyar hada hadar kasuwanci ce sai ya samu hanyar idda burinsa.

Tun zuwansa ya haďu da Hafiz wanda ke mataki na biyu a jami'ar a bangaren economics. Hafiz as a student bai zauna haka ba kayayyaki irinsu takalma da jakunkuna yake sara yana turasu gida Nigeria ana siyar masa. Wannan yasa suka kulla abota da Quraish domin ra'ayinsu yazo dai dai. Nan fa suka haďa hannu suka soma business tare. Kuďin su da ake tura musu na wata suke matse bukatunsu suke kullewa suna kasuwancin dashi. Tafi tafi Allah ya sawa harkar albarka. Kafin su kammala degree tuni sun zama manyan ýan kasuwa. Shi Hafiz takalma da jakunkuna kawai yake harka. shi kuwa Quraish bayan wannan yana turo spare parts na motoci irinsu tayoyi da kuma battery na mota sai kuma kayan dinki da kasuwar su ta soma garawa yake jarrabawa. kan kace kobo Allah ya daukaka shi ya bashi nasibi, kamar wasa arziki ya bunkasa.

Babu wanda yasan halin da yake ciki a gida sai da ya kammala degree domin shi mutum ne ba mai son hayaniya ba. Zurfin cikinsa bai bari ka gane halin da yake ciki idan ba dole ya zama ba
Lokacin da Abba yasan komai he was very impressed mamaki ya lullubeshi da farinciki. Ganin goyon bayan da ya samu daga wajen Abba ya sanya ya sake maida hankalinsa.

Wannan shine silar arzikin Quraish.
Ko da ya kammala degree bai tsaya ba kamar Hafiz masters ya ďora domin ganin ya cikawa Abba burinsa na son yayi ilmi mai zurfi.
Bayan ya kammala ya dawo Nigeria garin kano domin anan Allah ya qaddara kasuwancin nasa zai habaka. Kano itace cibiyar kasuwanci a Nigeria kuma shima ya yarda da haka. Bayan ya kammala yawancin abubuwan da yakeson yi ya samu amintattun yara guda biyu suke zaune a shagunan a qarqashin kulawar usman dan gidan Baba Bala.
Yana kammala wannan ya sake neman admission don hada phd ďinsa a fannin business administration.

Zuwa yanzu da yake gab da kammalawa Hamma Quraish ya soma zama young Millionaire domin a yanzu haka yana da manyan Shaguna a kasuwar kwari da Sabon gari!
A kwanankin nan ne kuma ya siya katon fili ya soma ginin mall din ya tattara dukkan burinsa a kanta!

Hamma Quraish kamar yanda kannen shi suke kiran shi mutum ne mai alkhairi da kyauta da son taimakon Jama'a domin haka yayi suna a family, duk da yawanci sunan na shi kawai aka sani kalilan ne suka san shi a fuska a dalilin rashin zaman sa a Nigeria da kuma rashin son mutane, duk inda taron Jama'a suka wuce biyar kunyar shiga cikin su yake yi, don haka da wuya ka gan shi a taro idan bai zama dole ba.
Yana da biyayya Kwarai irin wadda za'a kafa misali da ita domin Inna da Abba basu taba musu da shi sun ce eh yace a'a ba. Duk abinda suka umarce shi, shi yake yi  ba tare da jayayya ba don haka ya zama mafi soyuwa a zukatan su gabaďaya.
Yanda ya sace zuciyar iyayen shi haka ya sace ta ýan'uwan shi domin yanda suke ganin kadarin Abba hake suke ganin na Hamma. Bai bar su sunyi kukan komai ba, kullum sakon su a tafe yake daga gare shi, Kuďi, sutura da dukkan nau'in ababen jindaďi na ýan gata. Kuma bai taba wariya tsakanin ýaýan ďakin su da na Aunty ba don haka suke masa wata irin soyayya mara algus suke kuma girmama shi iyakar iyawar su.

wacece ni?Where stories live. Discover now