Kwakwalwarta ce take ta kokarin sarrafa mata tunanin da take so tayi amma tsananin mamakin da take ciki da kullewar kai ya gagare ta yin komai!
bata ankara ba taji an sake murda kofar an shigo
Farida ce this time, ta nufo ta da sauri ta rungume tana cewa"I'm soo happy for you my sister! Allah ubangiji ya tabbatar mana da alkhairi! Ihman kin gan shi kuwa? dan gaye mai kyau kamar wanda aka zabo miki shi? Yana zaune yana sauraren karatun alqurani da na je kai masa lemo, wallahi kun dace shima daga gani......."
Basu san Inna ta shigo ba sai ji muka yi tana cewa
"Kar ki shirya ki tafi, ki zauna jin surutun Farida"
Cikin sauri Farida ta juya tana cewa
"Inna yanzun nan zata shirya, naje na kai masa abun tabawa kuma nace masa tana zuwa! kar ki damu Inna ki bar komai a hannuna"
harara Inna ta sakarwa Farida ta juya, da alama dadin maganar Faridan taji! ohh! me ya shiga kan Inna ne yau?
Atamfa ta futo mata da ita, Ihman tayi mata kallon 'you have problem upstairs' tace
"wallahi bazan yi abinda kike so nayi ba Farida! you know me well kayan dinki basa cikin tsarina kuma duk inda zanyi presenting kaina nafi so naje da kamata da shigata da personality dina da yau da kullum idan mutum ya ga zai karbeni a haka toh, i can't start what i can't finish!"
Duk dadin bakin Farida bai yi tasiri ba domin dai cikin wannan Abayar Ihman ta shirya, baka mai purple din duwatsu ta nade kanta da mayafin kamar balarabiya, kwalli da lipgloss kawai ta saka wanda ya futo mata da ainihin kyawunta da nutsuwarta.
Ta dauko turaren "Fantasy" ta fesa kadan sannan ta juyo tana yi wa Farida gwalo!
Murmushi Faridan tayi tana jin dadin farin cikin da yar'uwarta ta soma samu a rayuwa! zata fi kowa farin cikin idan wannan al'amari ya tabbata akayi auren Ihman ta matsa daga gaban Inna itama ta samu nata jindadin da kwanciyar hankalin.Ta jima a kofar shiga sitroom din kafin tayi kundunbala ta shiga cikin siririyar sallama!
Yana kishingide akan kujera sanye cikin shadda wagambari skyblue an zizara aikin zare mai kayatarwa dan zariya ya dora hula damanga akan askakken kan shi! fuskar shi sai kyalli take yi da hasken karatun alqurani mai girma, ya gyara zama da sauri ya dauki wayar sa ya kashe kira'ar Shuraim da ke tashi cikin suratu Daha!"wa alaikissalam wa rahmatullahi wa barkatuhu ya habeebati"
Tayi murmushi ta zauna tana kallon yatsunta sannan ta gaishe shi a nutse!
ya kalle ta sosai, she is nothing but his perfect match! Sassaukar kyakykawar mace mai kunya da kamun kai da kamala, mara iyayi da hayaniya!
most of all mai tarbiyya da ilmin addini da karatun kur'ani! Idan har yayi dace Ihman ta kasance matar shi, toh tabbas Allah ya amsa addu'ar da Ammi tayi shekaru tana yi mi shi akan macen aure.Hirar awa daya suka yi mai matukar ma'ana da nuna tsantsar sanin daraja da ciwon kai, babu wani shirme da sharholiya ballantana kauce hanya! yayi mata irin bayanin da yayi wa su Abba sannan ya dora da manufar sa a kanta da soyayyar da yake yi mata nagartacciya tsabtatacciya wadda yake burin ta kai su ga aure!
sai ya bukaci sanin WACECE ITA? kuma menene burin ta game da rayuwa, cikin hikima irin ta malamin koyarwa a jami'a ya samu tayi mi shi bayanin da ya fahimtar da shi ita din wata mace ce mara hayaniya da dorawa kai abinda yafi karfin shi, komai na ta mai sauki ne kuma wanda zai kasance mai amfani a gare ta, idan akwai abinda take da buri dogo a cikin sa a rayuwa toh karatu ne, a wannan fannin kam tana da zuzzurfan buri, bayan wannan she is just a simple decent fulani girl wadda bata dauki duniya da zafi balle ta kona ta ba.Wannan dalili ya sake ba shi kwarin guiwar jin cewa tabbas ya samu matar da ta dace da shi wadda rayuwa da burin su da fahimta da ra'ayinsu yayi matukar dacewa. cikin lokaci kalilan magana ta koma babba, iyaye suka shigo ciki, waliyyan Salman suka zo neman auren Ihman aka kuma ba su, aka karbi kudin zance da sharadin idan ta kammala karatun secondary za'a saka rana, Abba yace lallai sai ta samu gurbi a jami'ar bayero kafin a daura musu aure da Faris, cikin gamsuwa aka kammala taron aka tashi.
And that was it, the beginning of everything.
------------------------------------------------------------
------------------------------------------------------------
Satikan da suka biyo baya shakuwa ce da dimbin soyayya suke wanzuwa a tsakanin Faris da Ihman, mafi yawan lokuta suna makale a waya, tana karatu yana jiye mata ko kuma yana bata shawarwari da dabarun masabaqar al'qurani mai girma, idan aka yi sati biyu ya kan ajiye komai ya taho garin Gombe ya gan ta, shima zuwan bata sake zani ba, abinda suke yi a waya shi suke maimaitawa idan yazo, domin dukan su basu da nishadin da ya fi tilawar alquranin a rayuwar su.
Duk musulmun kwarai ya kalle su sai sun ba shi sha'awa, kamar zabo su aka yi aka hada su don dacewa, abinda zai baka armashi kuma shine, duk su biyun didn't fall in love da halittar junansu sai halayya da dabi'a, ba kyau ko kyale kyale ko wata manufa suke hangowa akan junansu ba, so ne na gaskiya da haqiqa daga min indillahi, kowanne ya amince da dan'uwansa zai kasance da shi a kowanne hali a kowanne yanayi a kowanne lokaci.
Ba wanda ya rufe halin shi ga daya don yaudara ko ya bullo da wani sabon hali don burgewa, they are just themselves and nothing more, they let everything flows naturally ba tare da tursasawa ko tsayarwa ba don haka suka nutsu da juna suka samu kwanciyar hankali.
![](https://img.wattpad.com/cover/148545749-288-k758199.jpg)
YOU ARE READING
wacece ni?
General FictionWacece ni labari ne akan matashiyar da ta taso cikin wata irin rayuwa mai ďaure kai da jan hankali. Ba abun mamaki bane idan kishiyar mahaifiyar mutum ta tsane shi amma mahaifiyar kanta ta nunawa ďanta tsantsar tsana da tsangwama da kyara abun ban m...