WACECE NI??? CHATER THIRTY-TWO BY CUTYFANTASIA

185 17 6
                                    

Ina dab da kammala karatuna qaddarar rayuwata ta faru, wadda ita ce sanadin juya dukkan al'amura na zuwa negative daga postive! Ita ce dalilin da ya sanya halayena da tunanina da dabi'una suka chanja completely, itace dalilin da ya sanya ake tuhumata da laifukan da ban aikata don son rai ko rashin biyayya ba, ita ce tushen dakilewar walwalata da nishadina da farin ciki, itace sanadin abubuwa masu matukar yawa, itace dalilin da ya sanya ake mun kallon mara tausayi da imani da riko da rashin yafiya, ita ta sanya ake mun zargin nuna fifiko da wariyar nuna kauna da kulawa a tsakanin yayana,ita ce dalilin da tayi sanadin abinda ya tara mu nan yau a zaune"

Kusan duk falon sun san wannan labarin da tarihin, idan aka dauke Farida wadda tayi mutuwar zaune, hawaye na sharara a idanunta, zuciyarta tayi mata wani irin nauyi mara misali! Ko da wasa ko da subul da baka ko da misali bata taba jin cewa ba Inna ce ta haifi Hamma da Adda Wasila ba, bata taba tunanin akwai wata makamanciyar alaka irin wannan a tsakanin su ba. Through out her life Inna suka tashi suke gani a matsayin uwarsu gabadaya, kuma kowa ya tafi akan hakan, ko da subutar baki bata taba jin wani ko wata ya dangana su Hamma da watan Inna ba...........
Idanunta cazur ta dago tana kallon Inna cikin tsananin tausayi da karyewar zuciya, Innan tana ci gaba da labarin dalla-dalla da wani irin sauti mai sanyi da karya zuciya.

"Bazan taba mantawa da ranar talatar 12 ga watan april ba, ina gidan Rukayya da yamma Baba ya aiko yana kirana anyi baki suna son ganin yaran Rukayya! Da yamma ne liqis Quraishi ya taso daga Islamiyya kenan, na goya Wasila na ja hannun shi muka taho gida, tun daga nesa na hango kerarrun motoci guda biyu a fake a gefen gidan mu, raina ya baci domin nasan basa rasa nasaba da mutanen Ghana. Babu laifin tsaye ko na zaune babu wani kwakwkwaran dalili kawai bana son su, kuma bana son shiga sha'aninsu. Duk girman alaqa da dangantakar da ke tsakanin Baba da Alhaji da tarin alkhairin shi gare mu banji yana burgeni ba.Haka kawai!
Cikin sanyi na shigo gidan da sallama, na nufi katoton dakin Baba inda naga takalman bakin nayi sallama na shiga, idona bai sauka kan kowa ba sai wani saurayi wankan tarwada kyakykyawan gaske, yayi shigar kananan kaya da himilin suma a kansa, fuskar shi a hade kamar bakin hadari, kana ganin shi kaga wanda duniya take damawa da shi, kallon kowa yake dai dai kamar yace duk ku kwanta na taka ku don izza da isa da kasaita.
Bayan shi sai yayar shi Khadija wadda ya sauka a gidanta da niyyar makaranta, karatun na shi a can Ghana ya gagara domin ya riga ya gama fandarewa iyayen shi, sai abinda yaga dama yake yi, mijin Khadija DSP ne kuma dan'uwan jini ga Alhaji, mutum ne mara wasa da sanin abinda yake yi, shi yace wa Alajin ya kawo shi Kano Insha Allahu zai saitu. Wajen Khadijan na je wadda take ta miko mun hannu na bata Wasila, kawar Rukayya ce sosai lokacin da suke Kano, tare suka yi primary kafin su tsallake su koma Ghana. Na durkusa na kwanto mata Wasila na bata sannan na nemi waje na zauna na fara gaishe da sauran yan'uwan nata cikin ladabi.

"Toh daga wannan ranar ne na fada tarkon Sa'id, wai tunda ya ganni yaji yana sona, saboda tsabar rashin kunya a lokacin na bashi shekaru uku, yana level one ina level 400! Da farko ban gane ba, sai da naga yawan zuwan shi gidanmu barkatai da yake yi, kuma da wuya yazo bai shigo gidan Rukayya ba. Da yake ya ga babu abinda nake so irin yayanta, kullum zai zo da kayan zaki zai tahowa Quraish har da kayan wasa, ko Wasila sai da ta gane shi ta daina yi masa quiya.
Lokacin da na fuskanci abinda yake nufi sai na chanja masa fuska gabadaya na daina shiga harkarsa, idan yazo sai na shige daki na bar shi da Inna Hauwa'u yar'uwar Hajiya da muke zaune tare a gidan. Ashe ita ta dade da harbo jirgin shi, har ma ta saka wa lamarin albarka, wai har sunyi maganar da Baba ma yace mata a bari dai shi Sa'id din ya bayyana da kan shi.
Duk wata kalar kora da nuna tsana da ake wa dan'adam nayi wa Sa'id amma bai taba yin fushi ko ya dauke kafa ba, nayi fadan nayi fushin nayi ko in kula din ko a jikinsa, gidanmu ya zamar masa kamar wani zango, duk lokacin da ya taso daga makaranta nan zai biyo.
Mummunar qaddarar kuwa ta faru ne a wata ranar asabar, Na tashi daga ni sai Rukayya da Wasila a cikin gidan, Hajiya ta dauki Inna Hauwa'u zuwa Garo gaisuwar rasuwa, Quraishi yana tahfeez din da yake yini duk weekends sai da yamma ake zuwa a dauko shi. Na kammala gyaran gidan kenan nayi wanka na baje a tsakar gida da Wasila ina yi mata kitso gashin yana ta warwarewa, Rukayya na daga gefe a zaune, bana mantawa a ranar har murmushi tayi tana kallonmu, na kalleta ina jin wasu irin hawaye ina fatan dama ace zata dawo normal da lafiyarta mu dawo da aminci da rayuwar mu ta da.
Kamar ta san me nake sakawa sai ta tashi ta shiga cikin daki ta kulle kofa, jikina yayi sanyi qalau na gyarawa Wasila gashin na kwantar da ita a jikina tayi bacci.
Kamar daga sama sai gashi ya shigo, cikin halin da bamu taba ganin shi a ciki ba, cikin mummunan yanayin da kana kallon shi ka san a maye yake. Gabana ya yanke ya fadi......."

wacece ni?Where stories live. Discover now