WACECE NI???CHAPTER SIXTEEN BY CUTYFANTASIA

234 15 0
                                    

A motar Faris Ihman, Mami da Farida suka je dauko amarya suna tafe ana raha da annashuwa domin Faris ya iya entertaining mutane idan yaso duk da cewa Ihman tana hankalce da yanda yake ta kokarin danne damuwar da yazo da ita.
Bayan an kai amarya sun dawo ne su Farida suka yi mi shi godiya da sallama suka shiga gida suka bar shi tare da Ihman. Cikin nutsuwa tayi mi shi magana

"Kamar wani abun yana damun ka ko?"

Murmushin yake yayi yace

"Ashe kina studyn dina Ihman"

Ta dan yi Jimm sannan tace

"Me yake faruwa? Is it about me?"

Ta karasa maganar cikin fargaba.

Cikin rashin jin dadi yace

"Yaushe zamu bar wannan maganar? Yaushe zaki fahimci cewa wani abu tsakanin mu bai chanja akan wannan dalilin ba? This a different case"

Ta sake nutsuwa tayi shiru cikin tunani, tun zuwan shi ta gane damuwar da yake kokarin boyewa cikin raha da barkwancinsa, kuma tayi matukar mamakin ramar da ta gani a jikinsa, wasu lokutan ya kan tafi tunani cikin magana har sai ta dawo da shi! Tabbas akwai matsalar da ta ke damunsa, kuma  kowacce irin matsala ce, tana da matukar girma.
A hankali ta tsinkayi muryar shi yana yi mata bayani hopelessly

"Akan Ammi ne"

"How about her? Me ya faru?"

"Wajen wata biyar kenan tana dan ciwon ciki kadan kadan, idan muka je asibiti aka bata magani sai yayi sauki, sati biyu ko uku sai ya sake dawowa, a karshe likitan yace mu je AKTH domin proper medication, na dauke ta muka je, anyi running tests kala kala da scanning da Endoscopy, result ya futo aka ce ovarian cyst ne, wanda can baya ta taba fama da shi ta warke, so amma Doctor yace akwai futher binciken da yake so ayi mata, kusan duk lokacin nan da kika dauka baki da lafiya nima ina can da Ammi muna sintirin asibiti, sai last week final result ya futo.
Da yake doctor din abokin colligue dina ne, so a gida ma muka hadu yake mun bayani, Da farko anyi tunanin ovarian cyst ne kawai, amma bayan anyi cikakken bincike an gano it has become cancerous.
Wannan news din yayi breaking dina into pieces, idan na zauna gaya miki matsayin da Ammi take da shi a wajena bayan ma matsayin uwa, zamu kare a motar nan ban gama ba, tasha wahala a kaina, tasha kuka tasha tunani tasha tashin hankali to a point da ta kusa rasa tunaninta gabadaya..

"A yanzu da na zama mutum, na fara inganta mata rayuwar ta, na fara farfado da walwala da kwanciyar hankalin ta, lokacin da zan amfani da duk wata da dama da nake da ita wajen faranta mata da bata duk wani jindadi da farin ciki, sai ga wani ciwo yana son kawo shamaki a tsakanin mu."

Muryar shi ce ta soma rawa don haka yayi shiru yana goge kwallar da take sauko masa daga idanunsa, something Ihman has never seen, don haka taji wani irin tausayi da tashin hankali yana tsirga mata, a halin yanzu Salman ne hope da farin cikin ta, idan aka ce matar da tafi kowa muhimmanci a rayuwar shi tana cikin wannan halin ya za'ai ya samu tashi nutsuwar da kwanciyar hankalin har ya samar mata itama? She knows alot akan wahalar da Ammin ta shi tasha da shi da kuma gwagwarmayar rayuwar da suka yi kafin ya cimma gaci, to say wannan abun zai karya masa zuciya ma is an understatement.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!! Allah ya bata lafiya, Allah ya bata lafiya, Allah ya tashi kafadunta don alfarmar Annabin rahama Alaihissalam! Kayi hakuri, insha Allah she will be fine, zata warke ta samu sauki ka cika burikan da ka dauka akan ta gabadaya da yardar Allah"

Wani yake yayi mai ciwo yana kallon steering idanun shi taf da hawaye

"Ihman Allah kika ce, amma ciwon yayi spraying sosai a jikinta! Na yanke shawarar kai ta Egypt, akwai wani abokin karatuna Alee mahaifin shi kwararren likita ne a Saudi German Hospital da ke Cairo. bayan na gaya mi shi ya saka nayi forwarding result din zuwa email din Baban nashi Doctor Hussain ya gani, Yace tana stage II groupT2 ne,abun has spread to her both ovaries and uterus da wasu wuraren ma..........
Har hanzu ban gayawa Ammi komai ba, na dai kammala mana shirin tafiya a cikin satin nan, zamu tafi tare and fight this cancer together da yardar Allah, idan Allah ya nufa zata warke sai inda karfina ya qare, idan kuma........."

wacece ni?Where stories live. Discover now